COP27: Yadda Afirka ta Kudu za ta yi fama wajen daina amfani da makamashin kwal

Afrika ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Afrika ta Kudu

Afirka ta Kudu ta dogara ne kan kwal kusan kacokan a matsayin makamashinta amma daya daga cikin manyan matsalolin da kasar take fama da su ita ce yawan daukewar hasken wutar lantarki.

Don haka abin tambayar shi ne, yaya za ta iya rage dogaro da makamashi mai gurbata muhalli sannan ta mayar da hankali kan makamashi mai tsafta, yayin da kuma take kara hasken wutar lantarkinta?

Kamfanin samar da wutar lantarkin Afirka ta Kudu Eskom ya bayyana irin gagarumar matsalar da suke fama da ita a wani sakon Tuwita da ya wallafa a watan jiya.

Kafin mutane da dama a kasar su karya kumallo, kamfanin ya wallafa sakon da ke cewa: "An aiwatar da shirin rage hasken wutar lantarki mataki na hudu da misalin karfe biyar da rabi na safiya sakamakon lalacewar injini biya da ke samar da wutar lantarki a tashoshin samar da hasken lantarki biyar da tsakar dare."

Duk da cewa ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, Afirka ta Kudu ta yi fama da yawan dauke wutar lantarki a shekaru 15 da ska gabata. Sai dai wannan karon matsalar ta yi kamari.

Cibiyoyi biyar a tashoshin samar da hasken lanatarki biyar daban-daban sun fuskanci matsalar wutar lantarki abin da ke nuna irin kamarin da matsalar samar da lantarki ta yi kuma ta bai wa mutane da dama mamaki.

"Wannan abin tsoro ne saboda bai kamata a ce cibiyoyi biyar a tashoshin samar da hasken lantarki biyar su fuskanci wannan matsala a dare daya ba. Mene ne yake faruwa? " in ji masaniya kan makamashi Lungile Mashele.

"Cibiyoyin samar da lantarkinmu suna nuna yadda ake kula da su… Suna nuna cewa Eskom ba ya aikin da ya kamata, Eskom ba ya kula da su kuma dukkan ayyukan da suka kwashe shekaru suna yi ba su tsinana komai ba," in ji ta a tattaunawar da ta yi da BBC.

Eskom na da tashoshi 14 na samar da hasken lantarki daga makamashin kwal, wanda shi ke samar da kashi 80 cikin dari na wutar lantarkin kasar. Sai dai galibinsu sun tsufa, ba sa aikin da ya kamata sannan suna yawan fuskantar matsala.

Sabbin tashoshin biyu da ke amfani da kwal, wadanda aka soma kafa su a shekarar 2007, na cinye makudan kudi wajen gudanar da su, sannan ba sa aiki kamar yadda ya kamata.

Afirka ta Kudu na yin asarar megawat 4,000-6,000 kowacce rana sakamakon wadannan matsaloli - kusan kashi 10 na wutar da ake amfani da ita a yanzu.

Yawan dauke wutar lantarki yana matukar bata ran 'yan kasar Afirka ta Kudu.

Lamarin yana shafar 'yan kasuwa, manyan da kanana. Kazalika ana fuskantar cunkoson ababen hawa idan aka dauke wutar da ke kan tituna, kuma mutane ba sa iya dafa abinci sannan wanda suka dafa yana lalacewa sakamakon dauke wutar lantarki.

Matsalar tana ci gaba da yin kamari sakamakon rage yawan tashoshin da ke samar da hasken lantarki ta hanyar kwal, saboda ana so a koma amfani da makamashi mara gurbata muhalli.

A watan Oktoba, tashar hasken lantarki ta Komati da ke da karfin wegawat 1,000 da ke lardin Mpumalanga ta kasance ta farko da aka rufe .

Sai dai abin sha'awa shi ne yadda ake shirin sauya wa tashar Komati fasali domin ta rika amfani da makamashi mai tsafta, akuma tuni ta samu $500m (£440m) daga Bankin Duniya.

Afrika ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Babbar tashar lantarki ta Kusile mai amfani da kwal na daya daga cikin wadanda suke bai wa firka ta Kudu hasken lantarki

Sai dai ana bukatar karin kudade yayin da ake sa ran rufe tashoshin lantarkin da ke amfani da makamashin kwal . Kamfanin Eskom yana shirin rufe tashar lantarki mai amfani da kwal mai karfin megawat 45,000M nan da shekarar 2035.

Don haka ana bukatar sauya irin wadannan tashoshi da masu amfani da makamashi mai tsafta.

Sa'ar da Afirka ta yi ita ce Allah ya huwace mata iska da hasken rana masu dimbin yawa amma tana bukatar lokaci mai yawa da kudade masu dimbin yawa, domin sarrafa su.

A shekarar 2010, ta kaddamar da shirin samar da hasken lantarki na hadin gwiwa da 'yan kasuwa masu zaman kansu da zummar samar da lantarki ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.

An dan samu cigaba a wannan fanni. Yayin da yake magana a wajen taro kan makamashi a kwanakin baya, Ministan Makamashi Gwede Mantashe ya ce shirin ya samar da hasken lantarkin da ya kai megawat 6,000MW.

Amma hakan bai isa ba.

A 2020, an samar da kashi bakwai cikin dari na wutar ne kawai daga makamashi mara gurbata muhalli, a cewar Hukumar Makamashi Ta Duniya.

Ana kashe kudi sosai domin samar da hasken lantarki ta hanyar hasken rana a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana kashe kudi sosai domin samar da hasken lantarki ta hanyar hasken rana a Afirka ta Kudu

Kasar tana cikin kasashen da suka fi fitar da iska mai gurbata muhalli a duniya.

Shi ya sa kasashe masu arziki suke yin kokarin taimaka mata domin ganin ta mayar da hankali wajen samar da makamashi mai tsafta.

Ana kallon matakin bai wa kasar $8.5bn domin shawo kan wannan matsala a yayin taro kan muhalli da aka gudanar a Glasgow a matsayin wani babban mataki na taimaka wa Afirka ta Kudu domin magance wannan matsala.

Afrika ta Kudu

Asalin hoton, Reuters

Duk dai abin da ya faru, samar da hasken lantarki ta hanyar makamashi mai tsafta ba zai magance matsalar karancin wutar kasar ba.

Gabanin taron wannan shekarar a Masar, Shugaba Cyril Ramaphosa ya fitar da shiri na shekara biyar domin daina amfani da kwal zuwa makamashi mara gurbata muhalli, sai dai ya ce shirin zai lakume $84bn.

Yayin da yake kaddamar da shirin, shugaban kasar ya ce zai samar da ayyukan yi da kuma hasken lantarki a lokaci guda.