Daga Bakin Mai Ita tare da Hannafi Rabilu Ɗan Ibro

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Daga Bakin Mai Ita tare da Hannafi Rabilu Ɗan Ibro

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Hannafi Rabilu Musa, ɗa ga tsohon tauraron wasan Kannywood Rabilu Musa Ibro.

An haifi matashin a garin Danlasan na ƙaramar hukumar Warawa ta jihar Kano, kuma yanzu haka kansila ne a gwamnatin ƙaramar hukumar.

Kamar mahaifinsa, shi ma ɗanwasan barkwanci ne, kuma ya fara fitowa ne a fim ɗin Gidan Dambe, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Sauran shahararrun finafinan da ya fito sun haɗa Gidan Badamasi, da A Cikin Biyu.

Hannafi Rabilu Musa