Daga Bakin Mai Ita tare da Funky Mallam

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Daga Bakin Mai Ita tare da Funky Mallam

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Said Muhammad, wanda aka fi sani da Funky Mallam.

Tauraro ne da ya fara yin suna a finafinan Nollywood na kudancin Najeriya kafin ya leƙa Kannywood a arewaci.

An haife shi a jihar Edo, kuma ya fara karatun firamare a jihar Delta kafin ya kammala a jihar Abiya - duka a kudancin Najeriya.

Ya yi sakandare a jihar Filato, sannan ya samu shaidar digirin farko a fannin yaɗa labarai daga Jami'ar Bayero da ke Kano.

Yayin da ya yi fim ɗinsa na farko a Kannywood mai suna Tataɓurza, ɗan wasan na fatan ɗorawa daga nan a masana'antar.