Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar yi wa mutane kisan gilla a Najeriya

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar yi wa mutane kisan gilla a Najeriya

Jama'a a wasu sassan arewacin Najeriya sun shiga tashin hankali da ɗimauta a 'yan makonnin nan, sakamakon samun ƙaruwar yiwa mutane kisan gilla a gida, waɗanda a mafi yawan lokuta makusantan mamatan ne ake zargi da aikata hakan.

Kashe-kashen da hukumomin tsaro ke ba da rahotannin an aikata cikin wasu jihohin arewa kamar Kano da Bauchi da kuma Jigawa, na ƙara jefa ayar tambaya a zukatan al'umma cewa: 'shin me yake faruwa ne");