Yadda aka tsinci Hamdiyya a dajin Zamfara bayan ɓacewarta a Sokoto

Asalin hoton, Abba Hikima/Facebook
Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi.
Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari'ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto.
A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari'ar da har yanzu ake gudanar da ita.
A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara "cikin mummunan yanayi."
Ya ce ''wasu mutane ne sanye da kayan ƴansanda suka kama ta a cikin Sokoto, daga nan suka kai ta wani gida a cikin Sokoto, inda suka ɗan azabtar da ita, har ma suka yi mata allura''.
"Bayan yi mata allurar ba ta tashi ganin kanta ba sai a tsakiyar wani daji da ke jihar Zamfara, inda ɓarayi ke kama mutane'', kamar yadda lauyan nata ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa daga dajin ne Allah ya taimaketa ta gudu tare da wani mutum , har suka kai wani ƙauye da ake kira Ƴargeɗa.
Abba Hikima ya ce kawo yanzu matashiyar na samun kulawar likitoci da jami'an tsaro a jihar Zamfara, sai dai ya ce tana cikin mawuyacin hali.
''Ban ganta ba, amma na samu na yi magana da ita (ta waya), kuma bisa ga maganganunta za ka fahimci cewa tana cikin damuwa sosai dukka alamu tana cikin ciwo'', in ji shi.
'Yadda aka kama Hamdiyya'
Hajiya Zainab Ahmed, da aka fi sani da Bintu Hijazi daya daga cikin makusantan matashiyar ta shaida wa BBC yadda aka kama Hamdiyya.
''Bayan ta kammala cefane ta shiga keke Napep domin komawa gida, sai wani mutum ya tare Napep din sannan ta shiga cikin, bayan sun yi ƴar tafiya, sai wasu mutane sanye da kayan ƴansanda suka tare Napep ɗin, suka zargi mutumin da ya shiga daga baya da shaye-shaye'', in ji ta.
''Nan take sai mutumin ya ce ni bana shaye-shaye in ma kun musa ku tambayeta, sai ya juya kan Hamdiyya, sai ita kuma ta ce masa to ni na sanka ne? sai ya ce e mana ba tare muke ba");