'Na sha wahala saboda dokar hana fita' - Yadda jihohin Najeriya da aka sanya dokar ke fama

Wasu jihohin Najeriya sun sassauta dokar taƙaita zirga-zirga da suka sanya bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka fara ranar 1 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tarzoma.
Sai dai mazauna jihohin na jin raɗaɗin da dokar ta janyo musu. Yayin da kasuwanni suka kasance a rufe, wasu mutane kuwa na alhinin rasuwar 'yan'uwansu sakamakon zanga-zangar.
Zanga-zangar na zuwa ne yayin da 'yan ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Masu zanga-zangar, waɗanda suka fito da nufin gudanar da ita tsawon kwana 10 na buƙatar samun shugabanci nagari daga jagororin ƙasar.
Yayin da zanga-zangar ta kasance ta lumana a wasu sassan kudancin ƙasar, a ɓangaren arewacin ƙasar zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali da ɓarnatar da dukiyoyi.
Wasu gwamnatocin jiha a arewacin ƙasar irin su Kano, da Yobe, da Kaduna, da Jigawa, da Katsina, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga, bayan samun rahotonnin tashin hankali da sace dukiyoyi a lokacin zanga-zangar.

Jihohin da har yanzu ke ƙarƙashin dokar taƙaita zirga-zirgar.
Jihar Yobe: A ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya ce a yanzu an sassauta dokar taƙaita zirga-zirga, wadda yanzu ta koma daga ƙarfe 6:00 na maraice zuwa 6:00 na safe.
Jihar Kano: Bayan nazarin dokar, gwamnatin jihar ta sassauta ta, inda yanzu ta koma daga ƙarfe 6.00 na yamma zuwa 6.00 na safe, har zuwa lokacin da gwamnati za ta sake nazarin dokar. Hakan na nufin al'ummar jihar na da dama fita harkokin kasuwancinsu na tsawon wuni guda, sai dai babu zirga-zirga bayan wannan lokaci.
Jihar Kaduna: Mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar, Manir Hassan ya tabbatar wa BBC cewa an sassauta dokar, wadda a yanzu ta koma daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na maraice.
Jihar Plateau: Cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ya fitar, ya ce dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon sa'o'i 24 da aka sanya a birnin Jos, an sassautata, inda ta koma 12 na rana zuwa 6:00 na maraice. Hakan na nufin mazauna jihar za su iya zarga-zirga na tsawon sa'o'i shida a wuni.
Jihar Jigawa: Mai magana da yawun gwamnan jihar, Hamisu Muhammad Gumel, ya ce an ɗage dokar a ƙananan hukukomi 19 na jihar.
Sai dai ya ce a wasu ƙananan hukumomin takwas dokar ta koma daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 5:00 na asuba.
Ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin wannan doka su ne: Dutse, Gumel, Hadejia, Kazaure, Roni, Babura, Birnin Kudu, kuma Kiyawa.
'Dokar ta jefa ni cikin wahala'
Wani yaron shago mai suna Nazifi a Kano ya ce tsawon kwanakin da aka ɗauka ana aiwatar da dokar a birnin Kano ya sha matuƙar wahala, saboda a cewarsa kullum sai ya fita sannan yakan samo abin da za su sanya a bakin salati shi da mahaifiyarsa da kuma ƙannensa.
"A kullum idan na fita kasuwa, nakan samu naira 1,000 zuwa 1,500. Waɗannan kuɗi su nake amfani da su wajen saya mana abincin da za mu ci, sannan na biya kuɗin adaidata sahu," in ji shi.
"Amma da aka rufe kasuwanni, na shiga yanayi. Mun sha wahala saboda babu abin da za mu ci. Da farko na fara karɓo bashi a shagunan unguwarmu, amma daga baya sai suka daina ba mu bashin."
Ya ƙara da cewa: "A yanzu idan zan gaya wa jama'a halin da na shiga a waɗanann kwanaki sai wani ya ɗauka ƙarya nake yi. Ba zan iya bayanin halin da na shiga ba."
"Na ma yi jinya a lokacin dokar, amma saboda ba ni da kuɗin zuwa asibiti haka na haƙura. Da a ce ina fita da zan samu kuɗin da zan je asibiti har ma na sayi magani."
Ya ci gaba da cewa mutane masu sana'a irin tasa, a yanzu da aka buɗe kasuwanni, duk abin da suka samu zai kasance biyan bashin abin da suka ci a lokacin dokar.
Usman Muhammad, wani direban adaidaita sahu ne a Katsina, ya kuma ce ko a yanzu, kasuwanni ba su cika, don haka ya ce babu fasinjoji sosai a kan titi, duk kuwa da sassauta dokar.
Ya ƙara da cewa wannan hali ya jefa shi cikin matsi, saboda yana da iyalai da dama da suka dogara da shi.
Muhammad ya ce: "Bayan saka dokar a Katsina, duka abincin da na ajiye a gida sai da ya ƙare, a wasu lokutan maleji kawai muke yi.
"Bayan janye dokar, da na fito da babur ɗina, na hau titi amma kuma babu fasinja, haka na koma gida ba tare da samun kuɗi masu yawa ba.
"Ina roƙon gwamnati ta tausaya mana, su janye dokar nan a faɗin jihar don mu ci gaba da sana'armu."
'Mun yi asarar biliyoyin nairori lokacin dokar'
Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar Singa a Kano, Alhaji Musa Ibrahim, ya ce sun tafka babbar asara, da ta kai kimanin naira biliyan biyu zuwa uku, sakamakon sanya dokar a Kano.
Ya ƙara da cewa, akwai wani shago da ake cinikin da ya haura naira miliyan 300 a kowace rana, kuma akwai shaguna masu yawa irin wannan a kasuwar.
Ya ci gaba da cewa: "Mun samu mummunan koma baya a kasuwancinmu lokacin dokar."
"Mun yi asarar cinikin fiye da naira biliyan biyu zuwa uku a waɗannan kwanaki," in ji shugaban kasuwar Singa da ke Kano.
Wannan al'amari ya shafi kowa a kasuwar, kama daga masu shaguna zuwa waɗanda ke aiki a kasuwar."
Alhaji Musa ya ce in ban da wannan doka da asarar da za su tafka za ta iya zarta haka, saboda watakila ɓata-gari za su iya shiga kasuwar domin sace dukiya.
Saboda a cewarsa ya samu bayanan da ke nuna cewa wasu ɓata-gari na shirin afka wa kasuwar domin fasa shaguna, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba sakamakon dokar.