Fitattun ƴan wasan da suka yi bankwana da ƙungiyoyinsu a bana

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake kammala kakar wasan bana a fagen ƙwallon ƙafar nahiyar Turai, wasu fitattun ƴan wasa sun yi bankwana da ƙungiyoyinsu.
Waɗannan ƴan wasa dai sun zamo jigo a ƙungiyoyin nasu a shekarun da suka gabata kuma ana ganin cewa tarihi ba zai manta da tasirinsu a bunƙasar ƙungiyoyin ba.
Ga wasu daga cikin su.
Kevin De Bruyne

Asalin hoton, PA Media
Kevin De Bruyne ɗan wasan ƙasar Belgian ne wanda yake taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya kuma ya kasance kyaftin ɗin Manchester City da kuma ƙasarsa Belgium.
A ranar Talata 20 ga watan Mayu ɗan wasan ya buga wa City wasan ƙarshe a filin wasa na Etihad, a karawar da City ta doke Bournemouth da ci 3-1 a wasan gasar Firimiya.
Ɗan wasan mai shekara 33 ya shiga tarihin City a matsayin zaƙaƙuran ƴan wasan da ta yi.
Tun a watan Satumban 2015 ɗan wasan ya fara taka leda a City, kuma ya zuwa lokacin da ya yi bankwana a ranar Talata ya buga mata wasanni 283, tare da taimakawa a ci ƙwallaye 119 da kuma cin 72 da kansa.
Tsohon ɗan wasan Liverpool Jamie Redknapp ya shaida wa Sky Sports cewa: "Waye zai kusan zama abin da De Bruyne ya zama a duniyar ƙwallon ƙafa? Babu shi, shi kaɗai gayya ne."
Luka Modrić

Asalin hoton, RealMadrid/Facebook
Ɗan wasan tsakiyan Croatia ya riga ya yi sallama da magoya bayan Real Madrid a filin wasa na Santiago Bernabeu a wasan gasar La Liga na ƙarshe da ƙungiyar ta doke Real Sociedad da ci 2-0 a ranar Asabar 24 ga watan Mayun 2025.
Modric mai shekara 39 ya fara buga wa Real ƙwallo ne a 2012 bayan ya bar Tottenham, kuma daga lokacin zuwa yanzu ya lashe kofi 28 da Real Madrid ciki har da na gasar zakarun Turai shida. Ya kuma lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallo ta Ballon d'Or a 2018.
Shi ne ɗan wasan da ya fi kowanne lashe kofi a tarihin Real Madrid.
Luka Modric ya buga wa Real Madrid wasanni 590 daga 2012.
Yana dai cikin tawagar Real Madrid da za ta buga gasar Fifa Club World Cup.
Alexander-Arnold

Asalin hoton, Getty Images
Trent John Alexander-Arnold zaƙaƙurin ɗan wasan Ingila ne wanda ke tsaron baya ta gefen hagu, ko kuma wani lokacin yana buga tsakiya.
Ɗan wasan mai shekara 26 ya shafe shekara 20 a Liverpool, inda ya fara a matsayin ɗan yaro mai koyon ƙwallo a ƙaramar ƙungiyar, ya ci gaba da tasowa har ya shiga babbar ƙungiyar, ya kuma buga mata wasanni 354 ya zuwa ƙarshen kakar wasan bana.
A cikin wasanni 354, ɗan wasan ya zura ƙwallo 23 ya kuma taimaka an zura wasu 86, lamarin da ake ganin ba ƙaramar nasara ba ce ga ɗan wasan bayan.
Kwantaraginsa da Liverpool ya ƙare a ƙarshen kakar bana kuma tuntuni aka alaƙanta shi da komawa Real Madrid ta Sifaniya.
Ya buga wa Liverpool wasan ƙarshe a Anfield a karawar gasar Firimiya da ta tashi 1-1 da Crystal Palace wanda kuma shi ne wasansa na 259 a gasar.
Ɗan wasan ya sharɓi kuka bayan da aka tashi wasan, lokacin da magoya bayan Liverpool ke rera masa waƙar bankwana.
Lucas Vázquez

Asalin hoton, RealMadrid/Facebook
Lucas Vázquez ya shiga ƙaramar ƙungiyar Real Madrid ne a 2007, yana da shekara 16 a lokacin kuma daga baya ƙungiyar ta tura shi zaman aro a Espanyol.
Ya sake komawa Real a 2015, wannan karon ya shiga babbar ƙungiyar, inda ya ci gaba da taka leda har ƙarshen kakar wasan bana da kwantiraginsa ta ƙare da Real.
A tsawon shekarunsa a Real Madrid, ɗan wasan bayan Sifaniyan ya buga mata wasanni 400 kuma ya lashe kofuna 23 a Real, ciki har da na gasar zakarun turai da aka lashe da shi har sau biyar da kuma na La Liga huɗu.
Ɗan wasan ya yi bankwana da Real Madrid a filin wasa na Santiago Bernabeu a wasan gasar La Liga na ƙarshe da ƙungiyar ta doke Real Sociedad da ci 2-0 a ranar Asabar 24 ga watan Mayun 2025.