Yadda shan shisha ke iya hana mata haihuwa

....

Asalin hoton, MARWAN NAAMANI/AFP/Getty Images

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga gwamnatoci da su haramta ko taƙaita amfani da sabon salo na nau'ukan tabar sigari masu ɗanɗano da ƙamshi kamar shisha da sigari mai amfani da wutar lantarki wato e-sigarrete da hookah da dai sauransu.

Hukumar ta yi wannan kira ne saboda munanan illolin da ta ce ta gano da ke tattare da sigarin ga mashayanta wajen kamuwa da cututtuka masu alaƙa da lafiyar huhu da sauransu.

Hukumar ta kuma gano cewa sabon salon sigarin masu ɗanɗano da ƙamshi ne ke jan hankalin matasa har ta zame musu jiki.

Likitoci sun yi ƙarin haske kan illar da wannan sigari mai sabon salo da danginta ke haifarwa, inda suka yi nuni da cewa sinadarin da ke cikin tabar na iya haifar da matsalar numfashi har ma idan ba a yi sa'a ba ya kai ga mutuwa.

Farfesa Maimuna Aminu Kani, ƙwararriyar likita a jami'ar tarayya ta jihar Jigawa ta shaida wa BBC cewa illar tabar tana iya yin mummunan tasiri musamman ga mata wajen ɗaukar ciki ko ga masu juna biyu.

"Shan taba a ɓangaren mata na iya janyo kansar mahaifa, wasu lokuta, a kan ga cewa idan mace mai juna biyu ta sha taba, tana iya sa jariri ya fito ɗan ƙarami ko kuma a haifi yaro lokacinsa bai yi ba." in ji farfesar.

"Kuma taba tana hana ma haihuwa saboda tana kawo ƙarancin ƙwayoyin halitta a cikin jikin namiji sannan kuma yana hana mosti na kunnuwan mahaifa wanda ake kira 'ciliary action' wanda zai zuƙo ƙwai ya shigar da shi cikin mahaifa," kamar yadda likitar ta ƙara bayani.

...
Bayanan hoto, Hoton huhu guda biyu, na hagu shi ne yadda ya kamata lafiyayyar huhu ya kasance, sai kuma na dama da ke nuna irin illar da hayaƙi ke yi wa huhu.

Ƙwarariyar ta kuma ce taba tana shiga cikin huhun mashayanta wanda sindarin nicotine da ke cikin tabar ke hana huhun yin aiki yadda ya kamata.

"Shan tabar sigari ba ƙaramar illa take da shi ba, sai a ga wanda ke shan sigari yana yawan haki, da tari wasu ma har yana kai wa ga ana shaƙa musu iska saboda tsananin shan tabar tasu ya yi nisa sosai." in ji likitar.

Farfesar ta ƙara da cewa idan tabar ta ratsa jikin ɗan'adam, tana iya karya garkuwar jikin mashayanta tare da buɗe ƙofar harbuwa da kansar huhu.

"Kusan kashi 80 cikin 100 na kansar huhu idan aka duba za a ga cewa wanda ya kamu da cutar yana shan taba ko kuma ya sha taba da tsawon lokaci." in ji Dr Maimuna.

Ta ƙara da cewa "A wasu sassa kuma na jikin ɗan'adam, shan taba na iya shafar mafitsara ko ƙoda ko hanta da dai sauransu."

Alƙaluman Hukumar lafiya ta duniya sun nuna cewa aƙalla miliyan takwas na mashayan na'ukan taban sigari ne ke mutuwa na kowace shekara.

Saboda haka ne Hukumar ta jaddada mahimmancin ɗaukar ƙwararan matakai domin yaƙar shan nu'ukan tabar haɗi da tabar da aka saba ta yau da kullum.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa idan ba a samu dokoki masu ƙarfi ba, annobar za ta ci gaba da yin tasiri tsakanin mashayanta musamman matasa da mata.