Gane Mini Hanya: Tare da shugaban riƙo na PDP Umar Damagum
Babbar jam'iyyar hamayya a Nijeriya, PDP, ta ce ƙasar ta fi ƙarfin duk wani mutum, kuma ƙarfi, kuɗi ko barazana, ba sa taɓa dawwamar da mulki.
Shugaban jam'iyyar na riƙo, Ambasada Umar Iliya Damagum, ya ce duk yawan manyan 'yan siyasa da jam'iyya mai mulki za ta tara, a ƙarshe dai 'yan Nijeriya ne za su kaɗa ƙuri'a don zaɓar mutumin da zai shugabance su a 2027.
Yana wannan bayani daidai lokacin da jam'iyyarsa ke fuskantar koma-baya, saboda yawan sauyin sheƙa da wasu ƙusoshin PDP ke yi, ciki har da gwamna zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Ya kwatanta faɗuwa zaɓe da ajali, wanda ya ce a mafi yawan lokuta ba ya sallama. A zantawarsa da abokiyar aikina Raliya Zubairu cikin filinmu na Gane Mini Hanya, Ambasada Damagum ya fara da bayani kan yadda ya ji da yawan sauyin sheƙar.