Bokan da ake zargi da binne mutane da ransu ya shiga hannu

Hoton Umumba Ndiagu

Asalin hoton, Nigeria Immigration Service

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta ce ta kama wani mutum da ake zargin boka ne mai suna Onyeka Nwaobu, wanda ake zargi da binne mutane da ransu a gidansa da ke Umumba Ndiagu a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Sun kama mutumin ne a kan iyakar Najeriya da ƙasar Benin lokacin da ake zargin yana yunƙurin ficewa daga ƙasar, kamar yadda bayanin hukumar ya bayyana.

Bayanin ya ce an kama shi ne a a wani wurin binciken ababen hawa da ke garin Gbaji a kan iyakar Seme.

"Mun tabbatar cewa shi ne ta hanyar takardar katin ɗan ƙasa da aka samu a cikin kayansa da kuma lokacin da ake yi masa tambayoyi," in ji bayanin.

Labarin bokan ya karaɗe Najeriya musamman shafukan sada zumunta a cikin makonnin nan bayan bidiyon da aka riƙa yadawa wanda ke nuna yadda ake binne mutane da ransu a gidan bokan a jihar Enugu, lamarin da ya girgiza al'umma.

Sai dai Nwaobu ya musanta zarge-zargen - ya ce sharri ake masa.

Yadda aka bankaɗo labarin

A collage of di blurred image of di 13-year-old kidnap victim, and di suspected ritualist

Asalin hoton, screenshot

Bayanan hoto, Ceto wannan yarinyar ƴar shekara 13 daga hannun masu satar mutane ne ya bankaɗo labarin bokan mai kashe mutane

Labarin boka Onyeka Nwaobu ya bi gari ne bayan wata yarinya ta samu nasarar tserewa daga hannunsa bayan zargin da ake yi kan cewa shi da mutanensa ne suka sace ta.

Mutanen da BBC ta zanta da su sun ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Mayun 2025 a ƙauyen Umumba Ndiagu a ƙaramar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu.

A cikin wani bidiyo da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta, yarinyar ta ce an sace ta ne a lokacin da suka je daji tare da mahaifinta domin samo itace, sai wasu mutane suka same su suka ce wa mahaifin nata ya taimaka musu duba babur ɗinsu da ya lalace.

Daga nan sai mutanen suka ci ƙarfin mahaifin nata suka ƙwace ta suka gudu da ita, inda suka ɗaure mata baki da ƙafafu.

"Sun tafi da ni sai suka saka ni cikin wani rami suka rufe da ganyaye, sai ina ta ihu, shi ne wasu ƴan bijilante da suke wucewa suka ji ƙara suka zo suka ceto ni." kamar yadda yarinyar ta bayyana a cikin bidiyon.

Bayan haka ne mutanen ƙauyen waɗanda suka fusata sai suka yi zuga suka cinna wa gidan bokan wuta - to sai dai a lokacin mutumin, wanda sunansa na bokanci shi ne Ozor Ezeani ya gudu.

Wani mutumin ƙauyen mai suna Ambrose Obieze ya shaida wa sashen harshen Ibo na BBC cewa sun ga ramuka da yawa a gidan mutumin, inda ake zargin yana binne mutane.

Bidiyoyin da aka ɗauka na kayan bokanci da tsibbace-tsibbace da aka ɗauka a gidan mutumin sun karaɗe shafukan sada zumunta.

Matakin gwamnati

Picture of a demolished building belonging to di alleged ritualist
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Enugu ta rushe gidan bokan

Daga nan ne gwamnan jihar Enugu Peter Mba ya bayar da umarnin rusa gidan bokan, inda yanzu haka katafilolin gwamnati sun mayar da wurin fili.

Jihohi da dama a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi dokar da ta bai wa gwamnati damar rushe gidan duk wani mai satar mutane.

Haka nan rundunar ƴansanda a jihar ta Engu ta yaba wa ƴan bijilante da suka ceto yarinyar daga gidan bokan tare da kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a sace ta.

Wane ne Onyeka Nwobu?

Mazauna ƙauyen sun shaida wa BBC cewa Onyeka Nwobu wani riƙaƙƙen boka ne da kowa ke tsoron shi a yankin.

Sunansa na bokanci da ake kiran sa da shi shi ne Ozor Ezeani, amma akan kira shi da 'ichie million' wato 'mai miliyoyin kudi'. Ana masa wannan laƙabi ne saboda yadda yake watsa kudi a lokacin bukukuwa a ƙauyen.

An bayyana cewa ya daɗe yana zama a ƙasar Togo kafin daga baya ya dawo ƙauyen ya ce ya zama boka.

Wani malamin addinin kirista a ƙauyen, Ikechukwu Chime ya shaida wa BBC cewa mutumin ya dawo ne da irin ɗabi'ar nan ta wasu matasa da ke cewa sun koma bin addini da al'adar kakannin-kakanninsu, to amma a cewarsa "yanzu ta bayyana cewa jini suke sha".

Tsafi da mutane ba sabon abu ba ne

Kisan mutane domin tsaface-tsafacen samun kuɗi ba baƙon abu ba ne a Najeriya, ƙasar da take da yawan matasa masu fama da rashin aikin yi.

A watan Maris, ƴansanda a jihar Rivers sun kama wani boka da ƴan korensa waɗanda aka zarga da kashe wasu yara mata ƴan shekara bakwai ƴan gida ɗaya domin yin tsafi.

Haka nan a watan Janirun 2023, ƴansanda a jihar Ogun sun kama wani boka da ƴan korensa bakwai bisa zargin sacewa da kashewa da kuma sayar da gaɓoɓin wata budurwa mai shekara 26 a garin Ijebu Ode.