Sabbin alƙawurra uku da Tinubu ya ɗauka a shekarar 2025

Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Yayin da shekara ta 2025 ke kamawa, ɗaiɗaikun mutane da kuma gwamnatoci na ɗaukan alwashi na abubuwan da suke son cimmawa a shekarar.
A Najeriya, al'ummar ƙasar sun kwashe shekaru suna fama da tsadar rayuwa sanadiyyar wasu matakai da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.
Shugaban ƙasar, Bola Tinubu a jawabinsa na karɓar mulki ya sanar da wasu manufofi - kamar na cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar naira - waɗanda suka ta'azzara tashin farashin kusan komai a ƙasar.
Sai dai a saƙonsa na shiga sabuwar shekarar 2025, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce duk da dai shekarar 2024 ta zo da matsaloli da dama ga alummar ƙasar, ya na da yaƙinin cewa sabuwar shekarar 2025 za ta zo da abubuwan farin ciki da cigaba.
A cikin saƙon nasa, Tinubu ya ce alamomi na nuna tattalin arziƙin ƙasar na farfaɗowa, duk da dai farashin abinci da magunguna sun ci gaba da zama abin damuwa ga ƴan ƙasar, inda ya yi alƙawarin a shekarar 2025, gwamnatinsa za ta bunƙasa samar da abinci da kuma inganta samar da magunguna a cikin gida domin kawo sauƙi ga farashin su.
Ya kuma kuma ce sun duƙufa wajen rage hauhawar farashin kaya daga kashi 34.6 bisa 100 da yake a yanzu zuwa kashi 15.
Shugaba Tinubu ya kuma yi wa ƴan ƙasar wasu alƙawura guda uku a cikin jawabin nasa:
Shirin samar da bashi ga mutane da masana'antu
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙara inganta hanyoyin bayar da bashi ga ɗaiɗaikun mutane da kuma masana'antu masu muhimmanci domin haɓɓaka tattalin arzikin ƙasar.
Domin cimma hakan ne gwamnatin tarayya ta ce za ta kafa kamfanin da zai riƙa tsaya wa masu neman karɓar bashi na ƙasa.
Ana sa ran kamfanin zai fara aiki a cikin wata shida na farkon sabuwar shekarar, kuma haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanin da wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati kamar bankin masana'antu, da ma'aikatar kuɗi, da kuma ɓangaren masu zaman kansu.
A cewar sa, wannan mataki zai ƙarfafa gwiwar ɓangaren hada-hadar kuɗi, da faɗaɗa hanyoyin samun bashi, da kuma goyon baya ga ɓangarorin da ba a cika mayar da hankali kansu ba, kamar mata da matasa.
Ƙarfafa kishin ƙasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa wajibi ne ƴan Najeriya su kasance ƴan ƙasa nagari kuma masu kishin ƙasar domin a cimma burukan da aka sanya a gaba da kuma sabunta fata domin ci gaban ƙasar.
Tinubu ya ce a dalilin haka ne zai bayyana dokar ƙarfafa kishin ƙasa a watanni uku na farkon shekarar 2025, wanda tuni majalisar zartarwar tarayya ta amince da ita.
Ya kuma ce zai ƙaddamar da gangamin wayar da kan ƴan ƙasa da zai bunƙasa kishin ƙasa da soyayyar ƙasa da kuma ƙara danƙon haɗin kan al'umma.
Dokar za ta kuma inganta yarda da aiki tare tsakanin alummar ƙasar mabambanta da kuma tsakanin gwamnati da al'ummar Najeriya.
Taron matasa na ƙasa
Shugaba Tinubu ya sanar da batun haɗa wani gangami na matasan Najeriya a matsayin "wani mataki na nuna aniyarmu ta tafiya tare da matasa".
Tinubu ya ce taron na kwanaki 30, zai haɗa matasa daga faɗin ƙasar domin tattaunawa da samar da mafita kan matsalolin ilimi, aikin yi, tsaro, da kuma ƙirƙire-ƙirƙire.
Dama dai Tinubu ya taɓa yin magana kan wannan shiri a jawabinsa na ranar murnar samun ƴancin kai na 2024.
A jwabinsa na sabuwar shekarar 2025, shugaban na Najeriya ya ce za a yi gangamin na farko ne a cikin watannin farko na shekarar 2025.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba ma'aikatar kula da matasa za ta sanar da matakan da za a bi wajen zaƙulo matasan da za su wakilci matasan da ke faɗin ƙasar.
Matasa dai su ne ke da kaso mafi yawa na al'ummar Najeriya, sai dai kusan za a iya cewa rashin aikin yi da ya yi katutu tsakanin matasan ya taƙaita irin gudumawar da suke bayarwa wajen ci gaban ƙasar.