....Daga Bakin Mai Ita tare da Bawa Mai Kada na shirin Kwana Casa'in

Bayanan bidiyo,
....Daga Bakin Mai Ita tare da Bawa Mai Kada na shirin Kwana Casa'in

Daga Bakin Mai Ita, wani shiri ne na BBC Hausa, da ke kawo muku hira da fitattun mutane a kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan mako, mun kawo muku hira da Sani Mu'azu, wanda aka fi sani da Bawa Mai Kada a cikin shirin Kwana Casa'in na gidan talbijin na Arewa24.

An haifi Sani Mu'azu a birnin Jos a cikin jihar Filato, kuma ya ce ya yi karatun firamare da na sakandire a Jos kafin ya shiga Jami'ar Jos inda ya yi karatun digiri.

Fitaccen jarumin wanda ya yi fina-finai a masana'antun Kannywood da Nollywood na kudancin Najeriya, ya ce fara ne da harkar aikin jarida kafin ya tsunduma fannin wasannin kwaikwayo da fina-finai.

Sani Mu'azu ya ce ya fara harkar fim ne, tun ma kafin a kafa Kannywood da Nollywood.

Ya ce ya rika fitowa a fina-finan Nollywood ne, saboda burinsa na canza kallon da ake yi wa Bahaushe a fina-finan kudancin Najeriya, maimakon matsayi kawai irin na mai gadi da mai gyaran takalmi ko dan garuwa.

Ya ce ba ya kallon sana'arsa ta fim a matsayin wasa, duk da yake ya yarda cewa kwaikwayon rayuwar al'umma suke yi don aika sako da fadakarwa, amma ba wasa ba.

Don haka ya shawarci matasa da cewa duk mai sha'awar shiga harkar fim, kada ya kalle ta a matsayin wasa da wani shargalle.