...Daga Bakin Mai Ita tare da El-Mu'az Muhammad Birniwa

Bayanan bidiyo,
...Daga Bakin Mai Ita tare da El-Mu'az Muhammad Birniwa

Daga Bakin Mai Ita, wani shiri ne na BBC Hausa, da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan mako, mun kawo muku hira da El-Mu'az Muhammad Birniwa, fitaccen mawaƙi a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood.

An haifi tauraron ɗan asalin Birniwan jihar Jigawa, a unguwar Kaji cikin jihar Kaduna, ya kuma yi karatun kimiyya a sakandire kafin ya shiga harkar kasuwancin gidaje da filaye.

Ya ce ya shiga masana'antar Kannywood ne ta hanyar ƙungiyar marubuta ta ANA, musamman ɓangaren da ya shafi harkar waƙoƙi.