Ra'ayi Riga: Kan dawowar hare-haren Boko Haram
Duk da cewa hukumomi a Najeriya sun daɗe suna cewa dakarunsu na hadin gwiwar ƙasashe makwabta sun raunana ƙungiyar Boko Haram, hare-haren da ƙungiyar ke kai wa cibiyoyin sojin Najeriya sun ƙaru sosai a baya-bayan nan.
A ranar 8 ga watan Afrilun 2025, gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa game da dawowar hare-haren Boko Haram da kuma ƙaruwar sace-sacen mutane.
Ya ce ƙungiyar na ƙoƙarin dawowa inda sau da dama ta kai hari kan sansanonin sojoji da kashe fararen hula.
Mayaƙan na Boko Haram sun sauya salo daga kai hari a ƙauyuka da wuraren farar-hula, zuwa ƙaddamar da hari a cibiyoyin soji a jihar Borno.
Hari na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai wa barikin soji ta garin Marte a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda kuma rahotanni ke cewa mayaƙan Boko Haram sun kwashi makamai da kuma fatattakar sojojin barikin.
Wannan ne maudu'in da shirin na wannan mako ya tattauna a kai.