Ƴaƴan itatuwa masu matuƙar haɗari ga ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Abdalla Seif Dzungu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
- Twitter,
- Aiko rahoto daga Nairobi Kenya
'Ya'yan itace wani na'u'in ne da tsirrai ko bishiyoyi da ke furanni ke samarwa, galibi suna ƙumshe da tsabar iri a cikin su, kuma akasari suna da matuƙar ɗanɗano a baki.
Yana daga cikin muhimmin aikin tsirrai wajen watsa iri a matsayin hanyar ƙara yaɗuwarsu.
Wani lokaci amfanin 'ya'yan ita ce ba domin ɗanɗanon da suke da shi ba ne kawai ba a'a har ma ana amfani da su a matsayin magani.
To sai kuma duk da yanayin wasu 'ya'yan ita ce jan hankali, wani sa'in akan samu waɗanda ke matuƙar haɗari ga lafiyar ɗan'adam.
Waɗannan na daga cikin jerin 'ya'yan itacen da ke da matuƙar haɗari a duniya, kuma suna iya kai ga kisa.
1. Tuffan Manchineel - mai kisa

Asalin hoton, Thinkstock
Wannan wani irin tuffa (apple) ne da ake kira "coast apple" ko "tuufan mutuwa," wannan 'ya'yan itace ga shi da jan hankali amma guba ne.
A duk lokacin da aka ga wannan nau'in 'ya'yan itace yana da kyau da ƙamshi kuma ɗandanonsa tamkar da na tuffan da aka sani na asali. Sai dai wani abin mamaki da an kuskura an kai ga cin sa, nan take zai haifar da sarƙewar numfashi.
Babban ɓangaren da ke da illa a jikinsa shi wane irin ruwa mai yauƙi da ya ke fitarwa, mai kamar ƙaro.
Ɗigo ɗaya na wannan ƙaron na ƙumshe da tarin guba na'u'in phorbol da hippomane da ke iya ƙona fatar mutum har ma ya haddasa ciyo mai tsanani.
Kuma idan har aka taɓa shi ko aka ci wani sashen na wannan tuffa zai iya haifar da ciyon ciki mai tsanani da wani lokaci kan kai ga mutuwa.
Ana dai samun irin wannn tuffan a ƙasashen yankin Karebiyan da Mekziko da Amurka ta Kudu da wasu sassan kudancin jihar Florida. Sau da dama ana iya Manchineel kallon 'ya'yan itace mafi haɗari a duniya.
A cewar mujallar East Fruit, ƙabilar yankunan kan yi amfani da ruwan ƙaron wannan 'ya'yan itacen a matsayin makami. Tarihi ya nuna cewa wannan gubar ce ta yi ajalin ɗan yawon buɗe idon nan, Juan Ponce de León a shekarar 1521.
Bincike ya tabbatar da cewa ko a lokacin damina, zama a ƙarkashin bishiyar Manchinee domin fakewa daga ruwan sama yana da illa, kasancewar ruwan da ke ɗiga daga rassan bishiyar na iya cutar da fatar jikin mutum, idan ma mota ce a ƙarƙashin bishiyar kai tsaye ruwan jikin tuffan na iya narkar da fentinta tare da koɗe shi.
Ga alama wasu za su ga wannan tamkar labari ne kawai, alhali kuma zai zama babban gargaɗi ne ga waɗanda ke da damar zuwa kusa da wannan bishiyar ta Manchinee.
2. 'Ya'yan Ackee (Blighia sapida) - haɗi mai cike da guba

Asalin hoton, Getty Images
Shi kuma 'ya'yansa 'yan ƙanƙana ne kuma suna da amfai ga jiki sosai, wanda shekaru aru-aru 'yan ƙasar Jamaica na son sa har ma su kan sarrafa shi a cikin abinci.
Har wayau, kammanin wannan 'ya'yan itacen daban da yadda ya ke a zahiri. Idan har 'ya'yan Ackee sun nuna to ba su da wani lahani idan an ci, amma kuma idan yana ɗanye cike ya ke da guba da ake kira hypolycin A, wadda ke haifar da wata cuta da ake kira "Cutar amai ta Jamaica" da alamominta suka haɗa da amai da jiri da kuma dogon suma da zai iya kai ga mutuwa.
Idan 'ya'yan itacen Ackee ya nuna ya kan buɗe tamkar dai furanni inda za a iya ganin naman jikinsa mai launin rawaya, wadda alama ce da ke nuna gubar da ke cikin sa ta fita kenan kuma ana iya cin sa ba tare ya cutar ba.
Sai dai kuma duk da haɗarin da Ackee ke da shi, 'yan Jamaica na ɗaukar sa a matsayin abinci mai muhimmanci. Ana sarrafa shi a cikin abincin da ake haɗawa da kifi mai gishiri, wanda mutanen yankin ke matuƙar son sa.
Suna martaba Ackee ba wai a matsayin abinci kawai ba har ma suna ɗaukar sa wani a matsayin wani ɓangare na al'adun gargajiya da suka gada kaka-da-kakanni.
Ana kuma bayyana wannan 'ya'yan itace da mai ban mamaki wanda ya ƙumshi abubuwa biyu masu amfani da kuma haɗari, waɗanda ake dangantawa da ikon Allah da ya fi gaban mamaki.
3. Cherry

Asalin hoton, PA Media
Ko kun tuna yadda a wani lokaci idan kuna cin 'ya'yan itace ku kan tauna irin da ke cikinsa? To ku yi ƙoƙarin kaucewa haka idan kuna cin 'ya'yan cherries.
Waɗannan 'yan ƙananan 'yana itacen mai daɗin ci na ɗauke da iri a cikin sa da ke iya kisa.
Wani bincike da aka wallafa a mujallar ResearchGate, ya bayyana cewa irin da ke cikin 'ya'yan cherry na ɗauke da wata guba da ake kira hydrogen cyanide.
Idan bisa kuskure aka haɗiye 'ya'yan cikin wannan ɗan itace ɗaya ko biyu na iya cutar da lafiyarku, idan kuma aka haɗiye adadi mai yawa na 'ya'yan to fa akwai yuwar a samu bugun zuciya ko sandarewar jiki wani lokacin ma ana iya kai ga mutuwa.
4. Star Fruit

Asalin hoton, iStock
Shi dai wannan na'uin 'yan'yan itacen ana iya samun sa kusan ko'ina a duniya. Yana da zaƙi kuma ya yi kama da siffar tauraro idan an yanka shi, ga shi da farin jini ga maso amfani da shi.
Sai dai shi ma wannan nau'in 'ya'yan itacen na Star Fruits na ɗauke da guba.
Akwai wani binciken da ya tabbatar da irin waɗannan 'ya'yan itacen na iya tara duwatsu a cikin ƙodar ɗan'adam abin da ke haifar da cutar ƙoda daga baya.
Kan haka ne ma cin sa ke da babban haɗari ga waɗanda tun asali ke fama da wannan cutar.
5. Jatropha

Asalin hoton, iStock
Jatropha dai wani tsiro ne da akan samu a ƙasashen duniya masu zafi. Kuma 'ya'yan wannan tsiron launin rawa ne mai haske da ke da zaƙi, amma fa suna ɗauke da guba mai lahani da ake kira ricin da ke haddasa amai da gudawa da ciyon ciki da kuma zafin maƙogoro.
A ƙasar an sha samun lokuta da dama da ƙananan yara suka samu gubar wannan 'ya'yan itacen a jikinsu.
Wani bincike da aka wallafa Mujallar Binciken Lafiya ta Duniya ta International Journal of Medical Research and Reviews, ya tattara bayanai daga shekarun 2004 zuwa 2013 da suka gano cewa an samu ƙanan yaran da suka kamu da gubar Jatropha har sau 169.