..Daga Bakin Mai Ita tare da Abubakar Sani (Ɗan Hausa)

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
..Daga Bakin Mai Ita tare da Abubakar Sani (Ɗan Hausa)

Cikin shirinnmu na Daga bakin Mai Ita a yau mun kawo muku hira da fitaccen mawaƙin Kannywood, Abubakar Sani da aka fi sani da Ɗan Hausa.

An haifi mawaƙin a unguwar Gwale da ke birnin Kano. Ya yi karatunsa na Furamare da Sakandire duka a birnin na Kano, sannan ya samu shaidar diploma a jami'ar North West, kafin ya wuce Jami'ar Bayero inda ya samu digirinsa na farko a fannin aikin Jarida.

Ɗan Hausa ya ce ya fara waƙa ne sadaniyyar zamansa a kamfanin Iyan Tama Multimedia, kafin na ya yi wasanni a diramar dandamali.

Mawaƙin ya ce ya yi waƙƙai masu yawa, kuma akwai dadama cikinsu da yake ganin su fi samun ɗaukaka, ciki akwai waƙar Bazar Banzar Bazara da Jinjinar ƴa ga Gyale da Tutar So da Dawayya da Guɗa da sauramsu.

Abubakar Sani ya ce abincin da ya fi so a duniyar nan shi ne tuwo.

''Ai ni zan iya cin tuwo da safe da rana da kuma daddare, kawai da na samu canjin miya, musamman ɗumame'', in ji shi.

Ɗan Hausa ya ce babban burinsa a yanzu shi ne ƴaƴansa su samu tarbiyya mai kyau, domin su yi alfahari da shi a matsayin uba nagari