'Ina da shekara 17 aka cire min mahaifata ba tare da na sani ba'

Asalin hoton, Bongekile Msibi
Wata mata a Afirka Ta Kudu ta shaida wa BBC cewa, an cire mata mahaifa ba tare da saninta ba bayan ta haihu ta na da shekara 17 a lokacin.
Bongekile Msibi, ta ce ba ta tashi sani ba sai bayan shekara 11 a lokacin da take kokarin ganin ta kara haihuwa.
Matar 'yar shekara 48 da haihuwa, na daga cikin matan da aka cire wa mahaifa ba tare da saninsu ba a wani asibiti, in ji hukumar daidaiton jinsi.
Hukumar ta ce daga cikin binciken da ta gudanar bayan an kawo mata bayani a kan matar da aka cirewa mahaifar, sai da ta je asibitoci 15.
Wata kungiyar kare hakkin dan adam ce ta kai karar hukumar saboda yawan korafin da ta samu a kan ana cire wa mata mahaifa ba tare da sanin su ba.
Har yanzu ma'aikatar lafiya ta kasar ba ta ce komai ba a kan batun, to amma an ce Ministan Lafiyar kasar Zweli Mkhize, ya kira wani taro tare da hukumar daidaiton jinsi don tattaunawa a kan batun.

Bongekile Msibi, ta ce "Wata rana bayan na farfado sakamon haihuwa da na yi, sai na kalli kasan cikina, sai na tambayi wadanda nake tare da su cewa ya na ga bandeji mai yawa a kan cikina"> /* sc-component-id: sc-bdVaJa */ .sc-bdVaJa {} .rPqeC{overflow:hidden;display:-webkit-box;display:-webkit-flex;display:-ms-flexbox;display:flex;background-color:#F2EFEC;-webkit-flex-direction:row;-ms-flex-direction:row;flex-direction:row;-webkit-flex-wrap:wrap;-ms-flex-wrap:wrap;flex-wrap:wrap;box-sizing:border-box;} /* sc-component-id: sc-bwzfXH */ .sc-bwzfXH {} .coLDbX{width:100%;height:100%;object-fit:cover;object-position:50% 50%;position:absolute;background-size:cover;background-position-x:50%;background-position-y:50%;background-image:url('https://c.files.bbci.co.uk/assets/6a016b63-1515-413f-8920-3cb30d472862');} /* sc-component-id: sc-htpNat */ .sc-htpNat {} .kUePcj{max-width:743px;width:45%;position:relative;min-height:200px;-webkit-flex:1 1 auto;-ms-flex:1 1 auto;flex:1 1 auto;} /* sc-component-id: sc-bxivhb */ .sc-bxivhb {} .huvKBR{max-width:100%;position:absolute;bottom:0;right:0;color:#ffffff;background:#000000;opacity:0.7;font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;padding:5px;word-wrap:break-word;} @media (max-width:599px){.huvKBR{font-size:12px;line-height:16px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.huvKBR{font-size:13px;line-height:16px;}} @media (min-width:1008px){.huvKBR{font-size:12px;line-height:16px;}} /* sc-component-id: sc-fjdhpX */ .sc-fjdhpX {} .kexypQ{font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;color:#222222;} @media (max-width:599px){.kexypQ{font-size:16px;line-height:20px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.kexypQ{font-size:18px;line-height:22px;}} @media (min-width:1008px){.kexypQ{font-size:16px;line-height:20px;}} /* sc-component-id: sc-jzJRlG */ .sc-jzJRlG {} .fsaFRi{list-style:none;padding:0px;margin:0;} /* sc-component-id: sc-cSHVUG */ .sc-cSHVUG {} .dibKIM{max-width:100%;margin-right:20px;} .dibKIM:last-of-type{margin-bottom:8px;} .sc-jzJRlG > .dibKIM{display:inline-block;} .dibKIM > p{margin:0;} /* sc-component-id: sc-kAzzGY */ .sc-kAzzGY {} .UkXjf{font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;font-weight:bold;color:#1380A1;display:inline-block;} .UkXjf:first-child{margin-left:0px;margin-right:8px;} .UkXjf:last-child{margin-left:8px;margin-right:0px;} @media (max-width:599px){.UkXjf{font-size:32px;line-height:36px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.UkXjf{font-size:36px;line-height:40px;}} @media (min-width:1008px){.UkXjf{font-size:32px;line-height:36px;}} /* sc-component-id: sc-kpOJdX */ .sc-kpOJdX {} .iqxmph{display:block;margin-top:15px;font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;} .iqxmph > strong{font-weight:bold;} @media (max-width:599px){.iqxmph{font-size:15px;line-height:18px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.iqxmph{font-size:15px;line-height:20px;}} @media (min-width:1008px){.iqxmph{font-size:14px;line-height:18px;}} /* sc-component-id: sc-dxgOiQ */ .sc-dxgOiQ {} .deooVo{font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;color:#222222;margin:2px 0 0 0;} @media (max-width:599px){.deooVo{font-size:16px;line-height:20px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.deooVo{font-size:18px;line-height:22px;}} @media (min-width:1008px){.deooVo{font-size:16px;line-height:20px;}} /* sc-component-id: sc-kEYyzF */ .sc-kEYyzF {} .koizFp{width:45%;position:relative;margin:0;padding:15px 20px 25px 10px;word-wrap:break-word;box-sizing:border-box;-webkit-flex:1 1 auto;-ms-flex:1 1 auto;flex:1 1 auto;} /* sc-component-id: sc-kkGfuU */ .sc-kkGfuU {} .gXOHTF{font-family:Helvetica,Arial,sans-serif;color:#222222;font-weight:bold;} @media (max-width:599px){.gXOHTF{font-size:20px;line-height:24px;}} @media (min-width:600px) and (max-width:1007px){.gXOHTF{font-size:26px;line-height:30px;}} @media (min-width:1008px){.gXOHTF{font-size:24px;line-height:28px;}}
Hysterectomy:Removal of womb or part of it
Tubal ligation:Fallopian tubes blocked or sealed

Ta ce "Na bar asibitin bayan kwana biyar da haihuwata, 'yata lafiyayya ce, amma kuma akwai katon tabo a cikina".
Bongekile Msibi, ta ce ba ta tashi sanin ainihin abin da aka yi mata ba sai bayan shekara 11.
Komai ya bayyana saboda tana son kara haihuwa.
Ta ce ta rinka shan maganin hana daukar ciki, don haka a tsawon lokacin ba ta ganin al'adarta.
Bongekile Msibi ta ce "Da na fuskanci ina son kara haihuwa sai na je wajen likita, ya duba ni, sannan ya bani ruwa na sha, daga nan sai ya shaida mini cewa ba ni da mahaifa".
Ta ce ta yi matukar kaduwa gami da mamaki, sannan sai taga abin ma kamar wasa saboda ta taba haihuwa.
Daga nan sai ta yi tunani ta ce idan har an cire mata mahaifa, to lallai a lokacin da aka yi mata aiki aka cire mata 'yarta ne.
I want a baby so badly. When I saw a pregnant colleague this week I could not stand it"

Ta ce "Abin da suka yi mini sam bai dace ba kuma ba daidai ba ne".
Ta ce daga nan sai ta je wajen 'yan jarida, sannan ta wuce ma'aikatar lafiya, sai kuma ta koma asibitin da aka yi mata tiyata aka cire mata yarinyarta ta samu likitan da ya yi mata aikin.
Sai likitan ya ce mata ba zai ba ta hakuri ba, saboda ya cire mata mahaifa ne don ya ceci rayuwarta.
Ta ce "ban gane abin da yake kokarin fada mini ba, kuma babu wata shaidar hakan a asibitin".
Bongekile Msibi ta ce ba ita kadai aka yi wa hakan ba, bincike ya gano cewa akwai wasu matan 47 da aka cire wa mahaifar, wasu an shaida musu cewa an cire musu mahaifa ne saboda suna dauke da cuta mai karya garkuwar jiki, to amma ita ba ta da komai don haka me yasa aka yi mata hakan?
Matar ta ce, likitan ya shaida mata cewa wai ta sanya hannu a kan takardar amincewa a cire mata mahaifa.
Bongekile Msibi ta ce: "Sai na cewa likitan ni ban sanya hannu ba, saboda a lokacin ina karama ta yaya zanyi na gane me ake so na cike?
Likitan ya ce wai mahaifiyarta ma ta sanya hannu a irin wannan takardar amma ta ce ita sam ba ta sanya hannu ba.
Bongekile Msibi, ta ce "Wannan labarin ya sauya mini rayuwa".


Ta ce daga karshe sai rabuwa suka yi da saurayin da zai aure ta saboda shi yana matukar bukatar haihuwa, ga shi ita kuma babu dama.
Ta ce idan ta hadu da likita sai a tambayeta me take so?
Bongekile Msibi, ta ce "Hankalina na tashi musamman idan na ga wata kawata na da juna biyu".
Ta ce "yata yanzu haka na son 'yar uwa ko dan uwa, don haka sai muka yanke shawarar cewa bari mu samo da daga kan titi sai muka dauko ya kuma zama nawa".
Bongekile Msibi, ta ce har yanzu tana da kwan haihuwa don haka tana ganin sai asibitin da ya cire mata mahaifa ya biya mata a dauki kwanta a saka wa wata a mahifarta don a samar mata da da.
Ta ce bai kamata a bar likitoci su ci gaba da aikata wannan dabi'a ba saboda kawai mata ba su da wani cikakken 'yanci.
"Ya kamata likitoci su sani su kansu suna da iyaka, bai kamata suna daukar rayuwar mutane marar amfani ba," in ji Bongekile Msibi.
Ta ce "Ina kuma so likitan da ya cire mini mahaifa ya ba ni hakuri".
Bongekile Msibi ta ci gaba da cewa "Ba zan taba manta wannan abu ba, musamman idan naga tabon da aka bar mini a jikina".