window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 01/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa kai-tseye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin na yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Amnesty ta yi Allah wadai kan gurfanar da masu zanga-zanga

    ..

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty a Najeriya ta yi tir da kama tare da gurfanar da mutanen da aka kama da masu zanga-zangaa gaban kotu.

    Amnesty ta ce kama mutanen ya saɓa wa dokokin kare haƙƙi na ƙasa da ƙasa.

    "Yunƙurin gwamnatin Bola Tinubu na gurfanar da ƙananan yara kan zargin cin amanar ƙasa na nuna halin yin watsi da tanadin doka," in ji Amnesty cikin wata sanarwa a shafukan sada zumunta.

    "Jefa ƙananan yaran cikin mawuyacin hali kawai saboda sun shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa ɗaya ne daga cikin yunƙurin tauye 'yancin yin taro.

    "Wajibi ne Bola Tinubu ya sake su nan take kuma ba tare da wani sharaɗi ba."

    Ƙungiyar ta ƙara da cewa jami'an tsaro sun kama 12 'yan ƙasa da shekara 16 a jihar Katsina "kawai don sun fito titi a ranar zanga-zangar".

  3. Ina so a bi kadin tauyen haƙƙin da aka yi wa ƙananan yara - Peter Obi

    fff

    Asalin hoton, Peter Obi/Facebook

    Jagoran jam'iyyar adawa ta LP a Najeriya, Peter Obi ya yi kira ga mahukuntar ƙasar, musamman ministan shari'a da rundunar 'yansanda da DSS da kuma hukumar kare haƙƙin bil-adama su gudanar da cikakken bincike kan ''azabtarwar da aka yi wa ƙananan yaran da aka gurfanar a gaban kotu bisa zargin cin amanar ƙasa.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Obi ya ce bidiyon yaran da aka yaɗa a gaban kotu abin tayar da hankali ne.

    ''Halin da yaran ke ciki na yunwa da galabaita abn tayar da hankali ne ga duk wani mai hankali a ƙasar nan'', in ji shi.

    A yau ne dai 'yansandan Najeriya suka gabatar da wasu mutane ciki har da ƙananan yara a gaban kotu bisa zargin laifuka masu yawa ciki har da cin amanar ƙasa, kimanin wata uku bayan kamasu.

    Yadda aka gabatar da yaran ya janyo ka-ce-na-ce a faɗin ƙasar, musamman yadda aka ga wasu daga cikin ƙananna yaran cikin mawuyacin hali.

  4. Shirin da Amurkawa ke yi na zaɓar shugaban ƙasa

    'Yarmajalisar wakilai a Amurka, Ilhan Omar, ta faɗa wa BBC yadda alƙaluma ke sauyawa tsakanin Kamala Harris ta jam'iyyarsu ta Democrat, da kuma Donald Trump na Republican.

    Da take magana da Haruna Ibrahim Kakangi a jihar Minnesota ta Amurkar, Ilhan ta bayyana yadda suke aikin neman ƙuri'un Amurkawa.

    A ranar Talata ne dai za a kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  5. Kotu ta bayar da umarnin ƙwace dala miliyan biyu da wasu kadarori masu alaƙa da Emefiele

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin kammala ƙwace wasu kuɗi kimamin dala miliyan biyu daga wajen tsohon gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele.

    Yayin da yake yanke hukuncin, alƙalin kotun mai shari'a, Dehinde Dipeolu ya kuma bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori bakwai masu alaƙa da tsohon gwamnan na CBN, da kuwa wasu takardu mallakar hannayen jari.

    Mai shari’a Dipeolu ya ba da umarnin ne bayan buƙatar hakan daga lauyoyin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC.

    Kotun ta ƙwace kadarorin ne bayan da ta ce tsohon gwamnan na CBN ya kasa alaƙanta abin da ta kira 'halastaccen samunsa' a lokacin da yake aiki da bankin Zenith da kuma CBN da kuma mallakar kadarorin.

    Haka kuma kotun ta ce mista Emefiele ya kasa gabatar da takardun da ke nuna cewa kadarorin mallakarsa ne.

    A ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata ne kotun ta bayar da umarnin wucin gadi ga EFCC na ƙwace kuɗin da suka kai dala miliyan 2.045 da kadarorin bakwai da takardun mallakar hannayen jarin bayan sauraron ƙarafin da lauyoyin hukumar suka gabatar mata.

  6. Atiku ya soki gwamnatin Najeriya kan gurfanar da 'ƙananan yara' a gaban kotu

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook

    Jogaran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin ƙasar, kan abin da ya kira gurfanar da ƙananna yara a gaban kotu domin yi musu shari'a.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce ya damu da bidiyon yaran da aka nuna ''bayan yunwa ta yi musu illa, a inda aka tsare su''.

    ''Wannan abu na tayar da hankali ya tunamin da zaluncin 'yan aƙidar Nazi, tare da ƙara fito da yadda gwamnati ke wasarere da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ƙananan yara'', in ji Atiku Abubakar.

    Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ƙananan yara cikakken 'yancin mutuntawa, amma abin mamakin sai suka rasa hakan a Najeriya, a cewar Atikun.

    ''Ina mamakin mutumin da ke iƙirarin kare dimokraɗiyya, har ya jagoranci zanga-zanga a baya, amma a yanzu yake barazana ga waɗanda ke yunƙurin nuna damuwarsu kan halin da suka shiga sakamakon manufofinsa masu tsauri'', in tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar.

    Ya ƙara da cewa ƙananan yaran -waɗanda su ne suka fi cutuwa kan manufofin gwamnatin Tinubun na da damar gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama.

  7. Fiye da mutum miliyan 66 sun kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen Amurka

    'Yan takara

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutum miliyan 66 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen wuri na shugaban ƙasar Amurka, kamar yadda na'urar bibiyar ƙuri'un na jami'ar jihar Florida ya bayyana.

    Na'urar bibiyar ƙuri'un ta nuna cewa kashi 38.4 cikin 100 na waɗanda suka kaɗa ƙuri'ar 'yan jam'iyyar Dimokrats ne, yayin da jam'iyyar Republican ke da kashi 36.2 na ƙuri'un.

    Yayin mafi yawan jihohin Amurka suka bayar da damar zaɓen wuri, a hukumance ba za a fara ƙidaya ƙuri'un ba har sai ranar zaɓen wato 5 ga watan Nuwamba.

    Waɗannan alƙaluma na jihohi 26 ne da suka bayar da bayanan masu rajistar 'yan jam'iyya, inda hakan ke nufin rabin adadin ƙuri'un zaɓen wurin aka ƙidaya.

    Masu zaɓe da daban-daban ne suka kaɗa uri'un a karon farko a wurare daban-daban da aka tanada domin zaɓen.

  8. Ba za mu janye ƙudurin gyaran haraji daga majalisa ba - Tinubu

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce ba zai janye ƙudurin dokar gyaran haraji daga gaban majalisar dokokin ƙasar ba, duk kuwa irin irin ce-ce-ku-cen da ƙudirin ya janyo a ƙasar.

    Ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ne ta fara bayyana damuwa tare da watsi da ƙudirin saboda a cewarsu ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohin arewacin ƙasar,

    Haka ma ita ma majalisar tattalin arzikin ƙasar a zamanta na ranar Alhamis ta yi kira ga shugaban ya janye ƙudirin.

    Majalisar tattalin arzikin, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, tare da gwamnonin jihohin ƙasar 36 a matsayin mambobi ta bayar da shawarar janye ƙudirin, domin bayar da isasshen lokaci na tattaunawa da tuntuɓar juna a tsakanin masu ruwa da tsaki kan harajin.

    To sai dai cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Juma'a, ta ce shugaban ya ji duka koken da ake yi game da ƙudurin da buƙatar janye shi da ake yi, to sai dai ya ce ƙudirin - wanda tuni aka fara muhawara a kansa a majalisar - ba za a janye shi ba, sai dai ya ce a iya yin wasu gyare-gyare a lokacin muhawarar majalisar da kuma jin ra'ayin jama'a.

    Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasar bai aike da ƙudurin gaban majalisar ba, har sai da ya kafa kwamitin wanda kuma ya yi aiki na tsawon shekara guda yana tattara ra'ayoyi game da ƙudirin daga wajen masu ruwa da tsaki a fannin fannin arziki daga duka ɓangarorin ƙasar.

    ''Shi wannan ƙudiri da ke gaban majalisa, an aika shi domin kawo gyara a fannin yadda ake tafiyar da karɓar haraji a ƙasarmu''.

  9. Isra'ila ta yi ɓarna a ofishin kula da ƴan gudun hijira a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Shugaban ofishin ayyukan ƴan gudun hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya a Falasɗinu ya ce sojojin Isra'ila sun yi mummunar ɓarna a ofishin hukumar da ke sansanin ƴan gudun hijira na gaɓar yamma da kogin Jordan da suka mamaye.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Philippe Lazzarini ya ce ofishin wanda ke a sansanin Nur Shams kusa da Tulkarm, ba za a iya amfani da shi ba.

    Mista Lazzarini ya ce harin na sojojin Isra'ila ya kuma lalata hanyoyi, da wuraren samar da ruwan sha, da wutar lantarki. A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta musanta cewa ta yi barna a wajen.

    A ranar Litinin ne majalisar wakilan Isra'ila ta Knesset ta zartar da dokar hana gwamnatin ƙasar aiki da UNRWA kuma ta ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

  10. 'Abin damuwa ne irin yawan ma'aikatan lafiya da ake kashewa a Lebanon'

    Ma'aikatan agaji

    Asalin hoton, Labanese Red Cross

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta damu matuka kan adadin ma'aikatan lafiyar da ake kashe wa a hare-haren da Isra'ila ke kai wa Lebanon.

    WHO ta ce ta kaɗu bayan samun labarin kashe jami'an lafiya fiye da 100 a hare-hare fiye da 50 da aka kai.

    Ta ce adadin zai iya fin haka saboda akwai waɗanda aka kashe ba a wajen aiki ba.

    Isra'ila dai na zargin Hezbollah da amfani da motocin ɗaukar marasa lafiya wajen jigilar mayaƙansu da kuma maƙamai a asibitoci.

    WHO ɗin ta ce samun lafiya hakki ne na kowa da kowa a Lebanon.

  11. Mutum fiye da 200 sun rasa ransu a ambaliyar Spain - Jami'an agaji

    Ambaliya

    Asalin hoton, Valencia City Council

    Jami'an agaji a Sifaniya sun ce kawo yanzu mutum fiye da 200 sun rasa ransu sakamakon ambaliyar da ta afku a wannan makon.

    Har yanzu akwai mutane da dama da ba a gansu ba a yankin Valencia bayan da ƙaruwar ruwan ya tursasawa mutane maƙalewa a gidajensu da kuma wuraren aiki.

    Dubban ƴan sa-kai ne suka bi sahun sojojin ƙasar da ma jami'an agaji wajen ceto mutanen da ambaliyar ta shafa musamman a wuraren da ɓaraguzan gine-gine suka toshe hanyoyi.

    An yi gargaɗin fuskantar ambaliya a kudancin ƙasar saboda ruwan saman da ake tafkawa.

  12. Gidauniya ta fara tattara asarar da ƴan kasuwa suka yi sanadiyar rashin wuta domin neman diyya

    Lantarki

    Asalin hoton, NIGERIA ELECTRICITY

    Ƴan kasuwa da masu ƙananan sana'o'in na ci gaba da lissafa yawan asarar milyoyin naira da suka tafka sakamakon katsewar lantarki na kwana goma da aka samu a wasu jihohin arewacin Najeriya.

    Dangane da haka ne, wasu ƙungiyoyi suka soma koƙarin haɗa kan jama'a musamman ƴan kasuwa don neman diyya daga wajen gwamnati, sakamakon asarar da suka yi.

    Gidauniyar Jino mai rajin kare haƙƙi da fafutikar tabbatar da adalci da shugabanci nagari, ta ce ta soma tattara bayanai da yawan asarar da aka tafka a waɗannan jihohi domin bin hanyoyin da suka dace wajen neman diyya.

    Ta ce hakan na cikin wani ƙoƙari na taimakon mutanen da ake ganin wannan yanayi na iya durƙursar da su har abada.

    Matsalar ta katsewar lantarki dai ta faru ne sakamakon lalata layin da ke bai wa yankin arewacin Najeriya wuta a Shiroro zuwa Kaduna wanda ƴan bindiga suka yi.

  13. Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabon maƙami mai linzami

    Koriya

    Asalin hoton, Reuters

    Koriya ta Arewa ta ce makami mai linzami da ta harba a ranar Alhamis wani sabon samfurin makami ne mai suna Hwasong-19.

    Makamin ya yi nisan da ba a taɓa ganin irinsa ba a baya bayan nan, kuma an ba da rahoton cewa yana da iya kaiwa ko ina a cikin Amurka.

    Ƙaddamar da makamin na zuwa ne yayin da kwanaki kaɗan ya rge a gudanar da zaɓen shuganan Amurka. Gwamnatocin Amurka a baya sun yi ƙoƙarin ganin shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi watsi da shirinsa na nukiliya, amma ya bayyana cewa ba shi da niyyar yin hakan.

  14. Manchester United ta naɗa Amorim a matsayin sabon kocinta

    Amorim

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta tabbatar da naɗa Ruben Amorim a matsayin sabon kocin ƙungiyar.

    Kocin mai shekara 39, wanda ɗan ƙasar Portugal ne, zai fara ne aiki ne daga ranar 11 ga Nuwamban 2024, bayan ya sanya hannu a kwantiragin aiki zuwa shekarar 2027.

    Yanzu dai tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Ruud van Nistelrooy ne ke kocin riƙon ƙwarya, kuma zai ci gaba da riƙon har zuwa lokacin da Amorim zai fara aiki.

    Amorim ne koci na shida da zai horar da ƙungiyar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya, bayan shekara 26 yana horar da ƴan wasan ƙungiyar. Sannan akwai wasu guda huɗu da suka yi riƙon ƙwarya.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce, "Ruben na cikin zaƙaƙuran masu horar da ƴanwasa da suke ganiya a turai a yanzu."

    Wasan farko da Amorim zai fara a ƙungiyar shi ne wasan Manchester United da ƙungiyar Ipswich a ranar 24 ga Nuwamba, sannan a ranar 28 ga Nuwamba zai jagoranci ƙungiyar domin fafatawa da Bodo/Glimt a gasar Europa.

  15. Gwamnatin Najeriya ta tuhumi yaran da aka kama a zanga-zanga da cin amanar ƙasa

    Zanga-zanga

    Gwamnatin Najeriya ta gabatar da mutum 76 a babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a bisa zargin cin amanar ƙasa.

    An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a Najeriya a tsakani 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

    Sai dai daga cikin waɗanda aka gabatar a gaban mai shari'a Obiora Egwuatu ɗin, akwai wasu ƙananan yara da shekarunsu bai kai 18 ba, har da ma masu shekara 14, kamar yadda takardar ƙarar da BBC ta gani ya nuna.

    Ana tsaka da sauraron ƙarar ne, yara huɗu daga cikin waɗanda ake zargin suka yanke jiki suka faɗi, wanda ya sa dole alƙalin ta dakata domin a duba su.

    Daga nan sai aka fara kiran su ɗaya bayan ɗaya, ana karanta musu laifin da ake zargin sun aikata da Ingilishi, sai a fassara musu da Hausa, laifuka da suka ce ba su aikata ba.

    Wasu masu fafutika da suka zanta da BBC a harabar kotun sun ce wasu daga cikin yaran da aka kama, sun kasance a tsare na sama kwana 80.

    Daga cikin tuhumar da ake musu, akwai cewa "sun sanya tare da ɗaga tutar Rasha, suna rera waƙoƙin juyin juya-hali tare da kira ga Rasha ta kawo ɗauki a Najeriya."

  16. Ba don gudunmuwar Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban ƙasa – Sunday Dare

    APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa da wayar da kan al'umma, Sunday Dare ya ce ba don gudunmuwar Tinubu ba, da Muhammadu Buhari bai samu nasarar lashe zaɓe ba a zaɓen 2015.

    Dare ya bayyana hakan ne a shirin talabijin na Channels, inda ya ce, "idan ka kalla irin rawar da Tinubu ya taka wajen kafa jam'iyyar da Buhari ya yi takarar, zan iya cewa tabbas ba don gudunmuwar Tinubun ya bayar ba, da Muhammadu Buhari ba zai samu nasara a zaɓen ba," in ji shi.

    Sunday Dare wanda tsohon minista ne a zamanin mulkin Buhari, ya ƙara da cewa sun yi aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar Buhari a zaɓen 2015 da 2019, inda ya ce, "mutane da dama sun bayar da gudunmuwa, kuma kowa da irin rawar da ya taka a zaɓen."

    Ya ƙara da cewa, "yanzu zamanin Tinubu ne, kuma a shirye yake saboda yana da dukkan ƙwarewar da ake buƙata, kuma a shirye yake na yanke wasu matakan da shugabannin baya ba su ɗauka ba."

    A ƙarshe ya ce akwai buƙatar a yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa cire tallafin man fetur da sauran wasu tsare-tsaren da ya ɗauka domin inganta tattalin arzikin ƙasar.

  17. Shugaban ƙasar Botswana ya amince da shan kaye bayan jam'iyyarsu ta yi shekara 58 a mulki

    Bostwana

    Asalin hoton, AFP

    Masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar Bostwana sun kayar da babbar jam'iyya mai mulki a ƙasar Botswana mai suna Democratic Party (BDP) wadda take mulki tun shekarar 1966 a ƙasar, inda a zaɓen na bana, jam'iyyar ta BDP ta samu nasarar kujerar majalisar ƙasar guda huɗu kacal

    Jam'iyyar Umbrella for Democratic Change (UDC) ce za ta maye gurbinta bayan samun nasarar lashe mafi yawan kujeru.

    Tuni shugaban ƙasar na jam'iyyar BDP, Mokgweetsi Masisi ya kira jagoran jam'iyyar UDC, Duma Boko, a wayar tarho ya taya shi murma, tare da amincewa da zaɓin mutane.

    Ya ƙara da cewa, "zan ba ku duk gudunmuwar da kuke buƙata domin a samu nasarar miƙa mulki cikin lumana," kamar yadda ya bayyana masa a hirar tasu ta waya.

    Mokgweetsi Masisi ya bayyanawa manema labarai cewa jam'iyyar ta tafka kura-kurai, inda ya ƙara da cewa, "zan sauka daga mulki cikin mutunci, sannan in miƙa mulki kamar yadda doka ta nuna. Na amince da zaɓin mutane."

    A nasa ɓangaren, jagoran UDC, Boko ya ce wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga siyasar ƙasar.

    "Ban taɓa tunanin zan ga irin wannan ranar ba, inda za a samu cauyin mulki cikin lumana," in ji wata ɗaliba mai shekara 23, kamar yadda ta shaida wa Reuters, sannan ta ƙara da cewa sun gaji da jam'iyyar BDP a ƙasar, shi ya sa suka canja ta.

  18. Hare-haren Hezbollah sun kashe mutum bakwai a Isra'ila

    Hezbollah

    Asalin hoton, AFP

    Wasu hare-haren rokoki guda biyu da Hezbollah ta kai a arewacin Isra'ila sun kashe aƙalla mutum bakwai, kamar yadda hokumomi suka bayyana.

    A harin wanda ya auku a kusa da garin Metula, wanda ke maƙwabtaka da Lebanon, an kashe wasu manoma; ɗaya ɗan asalin ƙasar, huɗu kuma ƴan asalin ƙasar Thailand ne.

    Harin na biyu ya kashe wata mata da wani babban ɗanta a kusa da Kibbutz Afek a kusa da birnin Haifa.

    Hezbollah ta ce ta harba rokokin ne zuwa arewacin ƙasar domin jami'an tsaron Isra'ila da suke jibge a yankunan.

  19. An ba waɗanda ambaliya ta shafa a Spain tallafin dala miliyan 270

    Sifaniya

    Asalin hoton, David Ramos/Getty Images

    Shugaban gwamnatin yankin Valencia na Sifaniya, Carlos Mazon, ya sanar da bayar da tallafin dala miliyan dari biyu da saba'in ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a farkon makon nan.

    A yanzu dai an tabbatar da ambaliyar ta kashe mutane kusan ɗari da sittin.

    Ana sa ran adadin zai ƙaru yayin da wasu da dama suka ɓata kuma har yanzu ba a iya tantance cikakken tasirin bala'in ba.

    A kudancin birnin Jerez an kwashe ɗaruruwan iyalai daga gidajensu yayin da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya ƙara kaimi.

  20. Japan da EU za su ƙulla ƙawancen tsaro

    A yau Juma'a ne ake sa ran Japan da Tarayyar Turai za su sanar da wani sabon ƙawancen tsaro a lokacin da babban jami'in kula da harkokin waje na EU Josep Borrell ya gana da ministan harkokin wajen Japan Takeshi Iwaya.

    Sabon ƙawancen na da nufin ƙara haɗin gwiwa a fannin tsaro ta internet da tsaro a yayin da ake fuskantar ƙaruwar barazanar sojojin China a Asiya.

    Bayan tattaunawarsa a Tokyo, Mr Borrell zai tafi Koriya ta Kudu, inda ake sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan damuwa game da Koriya ta Arewa.