window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Muna roƙon majalisa ta gudanar da binciken ɓatan bindigogi na gaba a sirri - Kayode

    ..

    Asalin hoton, NPF

    Sifeto Janar na ƴansanda Najeriya, Kayode Egbetokun ya rubuta wa majalisar dattawa wasiƙa yana roƙonta cewa binciken da za a ci gaba da yi dangane da ɓatan bindigogi 3,907 ya kasance a sirrance bisa dalilan tsaro.

    Sai a wasiƙar, sifeto janar na ƴansandan ya yi watsi da rahoton 2019 da ofishin babban mai bincike da gwamnatin tarayya ya fitar wanda ya yi ikrarin ba a san inda dubban bindigogin ƴansanda suka shiga ba ya zuwa watan Janairun 2020 inda ya bayyana rahoton da cewa cike yake da kurakurai.

    Wasiƙar wadda aka karanta ta a majalisar dattawa bayan amince wa da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 a ranar Alhamis, na zuwa ne sa'a 48 bayan wani zaman saurare da kwamitin majalisar dattawa mai binciken kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati inda rundunar ƴansandan ta yi ta nuƙu-nuƙu wajen kare kanta.

    Sifeto Janar na ƴansandan, kayode Egbetokun wanda ya kasance a wurin sauraron bahasin ranar Talata kafin daga bisani ya nemi uzuri ya bar zaman, ya soki yadda ake neman titsiye rundunar ƴansandan ƙasar a bainar jama'a.

    Ya ƙara da cewa bai dace a rinƙa tattuna irin waɗannan batutuwan a bainar jama'a ba.

  2. 'Ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da ba ma ciki'

    Vlodomyr Zalensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ba za ta amince da duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka da Rasha suka cimma kan yaƙin Ukraine ba, matsawar ba a sanya ta cikin zaman ba.

    A jiya ne Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce a lokacin zantawarsa da Putin ta waya sun amince da tattaunawa domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin.

    Yayin da yake martani kan wannan batu, Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce ''yana da kyau kowa ya fahimci cewa ba za mu yarda ayi komai yassa Rasha ta tsara ba,...''kamar yadda kamfanin dillancin labari na Reuters ya ruwaito.

    Zelensky ya ƙara da cewa bai tattauana batun Nato da Trump ba, amma ya sani cewa Amurka ba ta muradin Ukraien ta zama mamba a ƙungiyar.

    A wani labarin mai alaƙa wasu ƙasashen Turai bakwai sun fitar da sanarwa buƙatar taka rawa a duk wata tattaunawa da za a yi a kan makomar Ukraine nan gaba.

    Trump ya ce zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Saudi Arabia, inda za su tattauna a kan yaƙin, to amma kuma Fadar White House, ta nuna alamun cewa babu wani shiri na wata ƙasar Turai ta kasance a wajen taron, ciki har da Ukraine ɗin kanta.

    Sai dai duk da wannan sakataren tsaro na Amurkar ya musanta cewa hakan alama ce ta cin amanar gwamnatin Ukraine.

  3. Isra'ila ta ce dole Hamas ta saki Isra'ilawa uku masu rai a ranar Asabar

    Isra'ila ta ce dole ne Hamas ta saki aƙalla Isra'ilawa uku masu rai a ranar Asabar idan har ana so a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.

    Mai magana da yawun ƙasar, David Mercer ne ya bayyana hakan, bayan Hamas ta sanar da sakin Isra'ilawa uku a ranar Asabar ɗin.

    Tun da farko ƙungiyar ta ce za ta dakatar da sakin Isra'ilawan, bayan da ta zargi Isra'ila da karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar, saboda hana shigar da kayan buƙatu zuwa Gaza.

    Hamas ta ce a yanzu waɗannan na shiga Gaza, duk da cewa Isra'ila ta musanta hakan - tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da yaƙin idan Hamas ta ƙi saƙin Isra'ilawan.

  4. Majalisun dokoki sun amince da naira tiriliyan 54.99 a matsayin kasafin ƙasar na 2025

    Tinubu

    Asalin hoton, Jide/sanwoolu

    Majalisun dokokin Najeriya sun amince da ƙudirin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 na naira tiriliyan 54.99.

    Kasafin wanda ke ƙunshe da kasafin kuɗaɗen yau da kullum da manyan ayyuka da biyan bashi da kuma hasashen samun kuɗin da za a cike giɓin kasafin kuɗin kamar haka:

    • Kasafi hukumomi da ma'aikatu: Naira tiriliyan 3.65
    • Kuɗaɗen gudanarwar gwamnati: Naira tiriliyan 13.64
    • Kuɗaɗen manyan ayyuka: Naira tiriliyan 23.96
    • Kuɗaɗen biyan bashi: Naira tiriliyan 14.32
    • Giɓin da ke cikin kasafi: Naira tiriliyan 13.08

    A ranar 5 ga watan Fabrairu ne shugaba Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin na 2025 daga naira tirirliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, bisa dalilan samun ƙarin yawan kuɗaɗen shiga da hukumomi suka samar wa gwamnati.

    Tinubu ya nemi majalisun su amince da ƙarin yawan kasafin a wasiƙu da ya aike wa majalisun guda biyu da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta.

    Shugaba Tinubu ya ce ƙarin ya samo asali ne bayan samun ƙarin kuɗin shiga na naira tiriliyan 1.4 da huukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS ta yi da kuma naira tiriliyan 1.2 da hukumar Kwastam ta samar sai kuma naira tiriliyan 1.8 da sauran hukumomin gwamnati suka bayar.

  5. Jamus ta zargi Trump da miƙa wuya ga Rasha

    Jamus

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaro na Jamus ya zargi shugaba Donald Trump na Amurka da sassauci ko miƙa wuya ga Rasha tun ma kafin a fara tattaunawar zaman lafiya.

    Boris Pistorius, na magana ne bayan da takwaransa na Amurka ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba Ukraine ta sake samun dukkanin yankunan da ta rasa, kuma ya yi watsi da yiwuwar shigar Ukraine ɗin ƙungiyar tsaro ta Nato.

    Mista Pistorius ya kafe kan ganin dukkanin waɗannan batutuwa biyu sun kasance cikin abubuwan da za a tattauna.

    Haka kuma ya yi gargaɗin cewa Rasha za ta ci gaba da zama barazana ga tsaron Turai, koda kuwa za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine.

    Mista Pistorius ya samu goyon bayan Shugabann gwamnatin Jamus , Olaf Scholz, wanda ya yi watsi da abin da ya kira ''zaman lafiyar dole ."

  6. MTN ya bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan ƙarin kuɗin kira da na data

    MTN

    Asalin hoton, MTN/Facebook

    Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya bai wa masu amfani da layukansa haƙauri kan ƙarin kuɗin kira da na data da kamfanin ya yi a ƴan kwanakin nan.

    A farkon makon nan ne aka wayi gari da ƙarin kusan kashi 200 cikin ɗari, lamarin da ƴan ƙasar da dama suka yi Allah wadai da shi.

    To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na X, ya ce yana sane da yadda masu amfani da layukansa suka nuna damuwa bayan da suka wayi gari kwatsam da ƙarin kusan kashi 200 na kuɗin data.

    Kamfanin ya ce zai iya bayar da dalilan da suka sa ya ɗauki matakin ƙarin, to sai dai ya ce in ma ya yi hakan ba zai gamsar ba.

    ''Saboda da haka mun karɓi laifinmu, mun yi kuskure, muna bayar da haƙuri kan hakan, a kuma yafe mana'', a cewar kamfanin.

    Ƙarin dai ya tayar da ƙura a Najeriya, lamarin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar, NLC ta buƙaci al'umma su ƙaurace wa amfani da layukan manyan kamfanonin wayar daga ƙarfe 11 na safe zuwa 2:00 na rana a kullum daga yau Alhamis, 13 ga watan Fabarairu har zuwa 28 ga watan.

  7. Yau ce Ranar Rediyo ta Duniya

    ...

  8. Hamas ta ce za ta ci gaba da sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su

    Mayaƙan Hamas biyu tsaye a gefen ɗan Isra'ila da suka saki a ranar Asabar

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Hamas ta ce a yanzu za ta saki Isra'ilawa uku a ranar Asabar mai zuwa, tana mai cewa tana son ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

    Sanarwar ƙungiyar na zuwa ne bayan tattaunawar da ake yi a Gaza.

    Tun da farko ƙungiyar ta ce za ta dakatar da sakin Isra'ilawan bayan da ta zargi Isra'ila da saɓa wa yarjejeniyar wajen hana shigar da gidajen tafi-da-gidanka da man fetur da sauran kayan aiki zuwa Gaza.

    A yanzu ƙungiyar ta ce ana barin waɗannan abubuwa suna shiga Gaza.

    Isra'ila ta yi barazanar komawa yaƙi da Hamas idan har ƙungiyar ba ta saki Isra'ilawan da take garkuwa da su ba.

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya musanta cewa tattaunawar tsagaita wutar na tafiya yadda aka tsara ta.

  9. Kotu na zama kan shari'ar Najeriya da kamfanin mai na Shell a Landan

    Mai

    Asalin hoton, others

    Yau ne wata babbar kotu a birnin Landan na Birtaniya ke zaman sauraron ƙorafin farko-farko a ƙarar da Najeriya ta shigar da kamfanin haƙar man fetur na Shell kan malalar ɗanyen man fetur a yankin Neja-Delta.

    Ana sa ran lauyoyin da ke tsaya wa Najeriya za su buƙaci kamfanin Shell ya amsa laifin illar da gurɓacewar muhallin da kwararar mai ya haifar tsakanin shekarun 1989 zuwa 2020.

    Hukumomin Najeriya sun ce wannan lamari ya yi tarnaƙi ga samar da ruwan sha mai tsafta ga al'ummar yankin, da lalata gonaki da hana ayyukan kamun kifi, tare da zama barazana ga lafiyar al'umma.

    Kamfanin na Shell dai ya musanta aikata ba daidai ba.

    Kuma ya ɗora alhakin malalar man a yankin Ogoni kan ayyukan masu satar ɗanyen mai da kuma wuraren tace man ba bisa ka'ida ba.

  10. Fitaccen ɗansiyasar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya rasu

    Danzogo

    Asalin hoton, Family

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar fitaccen ɗansıyasar jihar, Alhaji Ahmadu Haruna Zago da aka fi sani da Dan Zago.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tota ya fitar ranar Alhamis da safe, ya ce marigayın - wanda shi ne shugaban hukumar tattara shara ta jihar Kano - ya rasu ne bayan fama da jinyai a asibitin Mallam Aminu Kano da ke jihar.

    Dan Zago kamar yadda aka saninsa a jihar fitaccen dan gwarwanmayar siyasa ne da ya riƙe muƙamai daban-daban a fagen siyasa.

    Cikin muƙaman da ya riƙe har da shugaban tsohuwar jamiyyar ANPP na jihar Kano, sannan shi ne tsohon mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan hakokin siyasa.

    Bayan nasarar NNPP a zaɓen gwamnan jihar a 2023, Gwamna Abba Kabir ya naɗa shi shugaban hukumar tattara shara ta jihar. Gwamnan ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da ƴan'uwan marigayin.

  11. Amurka ba ta ci amanar sojojin Ukraine ba - Sakataren tsaron Amurka

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya ce yunƙurin Amurka na sansanta Rasha da Ukraine ba ''cin amana'' ba ne ga sojojin Ukraine, da ke yaƙi da mamayar Rasha tawon shekara uku.

    Hegseth ya jaddda cewa Amurka na “son ganin Ukraine” ta shiga Nato, yana mai cewa babu ƙasar da ke goyon bayan Ukraine fiye da Amurka.

    Ya ƙara da cewa Amurka ta kashe fiye da dala biliyan 300 domin ƙarfafa dakarun Ukraine da ke fagen daga, tun bayan mamayar Rasha.

    Mista Hegseth ya ce a duniya ta yi ''sa'ar'' samun Shugaba Trump wanda a yanzu ke da damar kawo zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.

    • A jiya ne dai, Hegseth ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba a yi tunanin Ukraine za ta ci gaba da iko da yankunan da ke ƙarƙashinta a 2014 ba, yayin da ya karya gwiwar ƙasar kan fatan da take da shi na shiga Nato.
  12. APC ta ƙaddamar da sabuwar rajistar mambobinta ta intanet

    Abdullahi Umar Ganduje

    Asalin hoton, Aminu Dahiru Ahmad

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ƙaddamar da sabuwar rajistar mambobinta ta intanet da nufin samun cikakkun bayanan adadin mambobinta gabanin zaɓuƙan 2027 da ke tafe.

    APCn ta bayar da kwangilar aikin ga wani kamfani mai zaman kansa mai Tunmef Global Limited, wanda zai jagoranci gudanar da aikin.

    Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya ce shirin na daga cikin dabarun jam'iyyar na amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da matsayin jam'iyyar na wadda ta fi girma a ƙasar.

    Ya kuma yaba wa shugaban ƙasar, Bola Tinubu bisa wannan dabara ta zamanantar da abubuwa.

    ''A yanzu komai na duniya ya koma na zamani, ba wanda yake amfani da hanyar gargajiya, kasuwanci na zamani, siyasa ta zamani, rayuwa ta zamani'', in ji shi.

    “Wannan fasaha za ta tabbatar da matsayinmu na cikakkiyar jam'iyya mai rajista, idan mun ce muna da mambobi miliyan 10, to ya kamata mu samu wannan adadi. Idan aka je zaɓe, idan muna da mutum miliyan guda a Lagos alal misali, muna sa ran samun aƙalla ƙuri'a 500,000, saboda kowace jam'iyya na da irin nata manufofi''.

  13. Paul Biya: Shugaba mafi tsufa a duniya ya cika shekara 92 a duniya

    Paul Biya

    Asalin hoton, Anadolu Agency/Getty Images

    Bayanan hoto, Paul Biya ya kwashe shekara 42 yana mulkin Kamaru

    Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya ya zama shugaban ƙasar da ya fi kowane tsufa a duniya.

    Mista Biya mai shekara 92 ya kasance ɗaya daga cikin jerin shugabannin da suka fi daɗewa kan karagar mulki a faɗin duniya.

    Shugaban ya kwashe shekara 42 a kan karagar mulki, bayan ya ci gajiyar hakan daga tsohon shugaban ƙasar, Ahmadou Ahidjo - wanda ya yi murabus ya kuma miƙa masa mulki a shekarar 1982.

    Kafin ya zama shugaban ƙasa dai, shi ne firaministan Kamaru daga 1975 zuwa 1982.

    Bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban ƙasar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.

    Alamu dai sun nuna cewa shugaban ƙasar na da aniyar sake tsayawa takara a wa'adin mulki na takwas, duk kuwa da sukar hakan da a ake yi a ciki da wajen ƙasar.

  14. Ukraine ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hari cikin dare

    Jirage marasa matuƙa

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin saman Ukraine, ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hare-hare cikin dare.

    Hare-haren sun fi ƙamari a yankunan Odessa da Kharkiv, a cewar sojojin.

    Rundunar sojin saman ta kuma ce ta samu nasarar kare wasu hare-haren daga ciki, yayin da ta tabbatar da kakkaɓo 85 daga cikin jiragen.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Nato ke taro a birnin Brussels, inda ake sa ran batun yaƙin Ukraine ne zai mamaye agjandar taron.

  15. 'Mayaƙan RSF na ci gaba da harbi kan mai tsautsayi cikin fararen hula a Zamzam'

    Ƴangudun hijira a sansanin da ya fi kowane girma a Sudan, sun bayyana yadda dakarun RSF ke ta harbe-harben kan mai tsautsayi a kan fararen hula tun bayan da suka mamaye sansanin a ranar Talata.

    Wani mazaunin sansanin, ya ce mayaƙan RSF sun far wa sansanin ƴangudun hijira na Zamzam ta ko wane ɓangare, sannan suka toshe hanyar zuwa birnin El fasher, inda hakan ke nufin ba inda mazauna wurin za su iya tafiya.

    Ya ce mayaƙan na RSF sun lalata kasuwar da ke kusa da sansanin tare da tilasta wa mutanebarin gidajensu da dabbobinsu, lamarin da ke ƙara hatsarin fuskantar yunwa.

    Babban Daraktan ma'aikatar lafiya Arewacin Darfur, ya ce an kashe aƙalla mutum 10, bayan da mutum 75 suka zamu munanan raunuka, to sai dai adadin ka iya zarta haka.

  16. Kundin Guinness ya karrama ɗan Najeriya kan bajintar ɗaukar hoto

    Saidu Abdulrahaman

    Asalin hoton, Saidu Abdulrahaman/X

    Kundin Adana Abubuwan Bajinta na Duniya, 'Guinness World Record ' ya karrama wani ɗan Najeriya, Saidu Abdulrahman saboda ɗaukar ƙananan hotuna masu yawa cikin sa'a guda.

    A ranar Laraba ne wakilan kundin suka gabatar da lambar karramawar ga gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.

    Saidu Abdulrahman ya samu wannan bajinta ne a shekarar da ta gabata, bayan da ya ɗauki ƙananan hotuna 897 a cikin mintuna 60.

    Gwamnan Mai Mala Buni ya ce yana alfahari da bajintar matashin ɗan jihar, wanda ya ce yana fatan hakan zai zaburar da matasan jihar.

    Ya kuma ƙarfafa wa matashin gwiwa ya ci gaba da aiwatar da abin da yake yi domin ƙarfafa wa sauran matasa.

  17. Ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita wutar yaƙin Gaza a Masar

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotonni daga birnin Alqahira na cewa ana samun ci gaba a tattaunawa tsagaita wutar yaƙin Gaza da ake gudanar da birnin.

    Jami'an Masar sun gana da wakilan Hamas, wadda ta yi barazanar dakatar da sakin Isra'ilawan da aka tsara za ta saki kan abin ta da kira ''saɓa wa yarjejeniyar''.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa za a koma mummunan faɗa idan Hamas ta ƙi mayar da wadanfda take garkuwa da su a ranar Asabar ba.

    Masu sanya idanu kan yarjejeniyar zaman lafiyar sun ce motocin kayan agaji masu yawa sun shiga Gaza tun bayan fara aiwatar da yarjejeniyar.

  18. Majalisa na son shugaban kwastam ya yi bayani kan ƙin yi wa wasu manyan jami'an hukumar ritaya

    Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya kan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a ya gayyaci babban kwanturolun hukumar kwastom na ƙasar, Adewale Adeniyi domin ya yi mata bayani kan abin da ya sa wasu manyan jami'an hukumar suka ƙi yin ritaya duk kuwa da lokacinsu ya yi.

    Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko ya fitar, ya ce an gayyaci babban jami'in hukumar ne domin ya yi bayani kan ƙorafin da aka shigar wa kwamitin dangane da ƙin yin ritaya da wasu manyan jami'an hukumar suka yi bayan lokacinsu na hakan ya yi.

    Gidauniyar Obasi-Pherson Help ce ta shigar da ƙorafin gaban kwamitin , inda ta yi zargin cewa wasu jami'an hukumar masu muƙamin mataimakin kwanturola da masu muƙamin kwanturola sun ƙi ajiye aikinsu, bayan cikar lokacin.

    Yayin bayar da sammacin, majalisar wakilan ta ce babban kwnturolan ƙasar ne kaɗai ke da haƙƙi bayyana wa 'yan ƙasa ainihin gaskiyar wannan zargi.

    “Ƴan Najeriya sun cancanci sanin gaskiyar abin da ya faru daga bakin babban konturolan..., a wannan lokaci da mafi yawan matasanmu ke neman ayyukan yi, indai batun nan gaskiya ne, to babu adalci ace ga wasu tsofaffin da suka isa ritaya su ƙi yin hakan,'' a cewar shugaban kwamitin, Mike Etaba.

    Ya ƙara da cewa ''ba wai muna ɗaukar ɓangare ba ne, muna nazarin kowane batu ne bisa gaskiya domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka cancance shi''.

  19. Firaministan Indiya ya isa Amurka don ganawa da Trump

    Modi da Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya isa Washintong domin ganawa da Donald Trump yayin da ake tsaka da nuna damuwa kan haraje-harajen da Amurka ke ƙaƙabawa da kuma batun baƙin haure.

    Ana tunanin cewa Mista Modi na iya rage wasu shingen kasuwanci kan muhimman kayayyakin da Amurka ke shigowa da su domin daƙile duk wani ƙarin harajin da za a iya sanyawa.

    Ana kuma sa ran Shugaba Trump zai nemi Delhi ta kwashe 'yan ƙasarta da ba su da takardun izinin zama Amurka.

    Wasu alƙaluma sun ce kusan Indiyawa 700,000 ne ke Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

  20. Shirin Amurka na dakatar da tallafi na haifar da koma baya - WHO

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya ce dakatar da ba da tallafi ga ƙasashen duniya da gwamnatin Trump ta yi na haifar da gagarumar koma-baya.

    Yayin da yake jawabi a birnin Geneva, Mista Ghebreyesus ya buƙaci gwamnatin Amurka ta sake duba batun.

    Dakta Ghebreyesus ya ce hakan ya shafi yaƙin da ake da cuta mai karya garkuwar jiki da polio da ƙyadar biri da murar tsintsaye.

    A farkon makon da ya gabata ne dai gwamnatin Trump ta sanar da dakatar da bayar da tallafi ga ƙasashen waje da wasu ƙungiyoyi, ciki har da hukumar tallafa wa ƙasashe ta Amurka, USAID.

    Mista Ghebreyesus ya kuma ce dakatar da tallafin zai shafi ƙoƙarin yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV a ƙasashe 50 na duniya.