window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Jami'an tsaron Najeriya sun 'kashe ƴan fashi huɗu' a Kaduna

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Masu bibiyarmu ƙarshen rahotannin kenan a wanna shafin.

    Mu haɗu da ku gobe don kawo wasu sababbin labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.

  2. Gwamnatin Najeriya ta ƙi faɗar ranar da jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja zai koma aiki

    Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli yadda jirgin ya yi aikin gwaji ranar Lahadi

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ba zai ci gaba da aiki ranar Litinin ba kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai a ƙasar suka ruwaito tun farko.

    Wata majiya a Ma'aikatar Zirga-Zirgar Jiragen Ƙasa ta shaida wa BBC Hausa cewa sai "nan gaba kaɗan" jirgin zai dawo aiki kamar yadda ministan ma'aikatar ya sanar a baya.

    A yau Lahadi ne Minista Muazu Jaji Sambo ya kai ziyarar ganin gyaran da aka gudanar a kan titin jirgin sakamakon lalata shi da 'yan bindiga suka yi a harin da suka kai a watan Maris wanda ya jawo dakatar da zirga-zirgar.

    Jirgin ya yi tafiyar gwaji daga Abuja zuwa Kaduna a yau ɗin cikin shirye-shiryen da ake yi don komawarsa aiki.

    A cewar ministan, gwamnati ta bijiro da sabon tsarin sayan tikiti mai cike da tsaro "don tabbatar da cewa an san waɗanda ke shiga jirgin a kowane lokaci".

  3. An kori manajan banki a Iran saboda ya saurari kwastoma maras mayafi

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labarai a Iran na ruwaito cewa an sallami wani manajan banki daga aiki sakamakon ya saurari wata kwastoma wadda ba ta saka mayafi ba.

    Wakilin BBC ya ce gwamnan lardin Qom ne ya bayar da umarnin sallamar manajan.

    Akasarin bankunan Iran na ƙarƙashin ikon ƙasar kuma gwamnati na buƙatar ma'ikata su aiwatar da dokar saka hijabi.

    Korar manajan bankin na zuwa ne bayan ƴar ɗan uwan jagoran addinin ƙasar ta yi kira ga duka gwamnatocin ƙasashen waje su yanke hulɗa da Iran.

    Ta yi bidiyo ne inda ta zargi gwamnatin Iran da cewa "ba ta san komai ba illa amfani da ƙarfi da kuma ƙoƙarin zama kan mulki".

  4. Jami'an tsaron Najeriya sun 'kashe ƴan fashi huɗu' a Kaduna

    Dakarun Najeriya

    Asalin hoton, KDSG

    Dakarun Sojan Najeriya sun kashe 'yan fashin daji huɗu yayin wani samame da suka kai kan sansanoninsu a Jihar Kaduna.

    Kwamashinan Tsaro na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun da ke cikin rundunar Operation Forest Sanity sun kashe mutanen ne a yankin Ƙaramar Hukumar Chikun.

    Cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi, Mista Aruwan ya ce sojoji sun bi sawun 'yan bindigar ne tare da kashe biyu daga cikinsu.

    Rahotannin sirri da gwamnati ta samu daga yankin sun bayyana cewa ƙarin biyu sun mutu sakamakon raunukan da suka ji, in ji kwamashinan, yayin da rahotannin suka bayyana sunan Dogo Mallam da Bello Mallam cikin 'yan fashin da aka kashe.

    Ya ƙara da cewa dakarun su ƙwace bindigar AK-47 da babur ɗaya da kuma harsasai.

  5. Kofin Duniya: Morocco ta cinye Belgium tare da haɗa maki hudu

    Croatia

    Asalin hoton, Getty Images

    Morocco ta bai wa Belgium mamaki bayan ta doke ta 2-0 a wasa na biyu a rukuni na shida a Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.

    A minti na 73 Morocco ta ci kwallon farko ta hannun Abdelhamid Sabiri, sannan Zakaria Aboukhlal ya kara na biyu daf da lokaci zai cika.

    Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Coutois shi ne ya yi kuren kwallon farko a bugun tazara da Sabiri ya buga masa, saura minti 17 a tashi daga wasan.

    A karawar Belgium wadda ba ta taba daukar kofin duniya ba ta je Qatar a matakin ta biyu a kan gaba a taka leda a duniyaq, biye da Brazil ta farko.

  6. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ba da umarnin tsaurara tsaro a ofisoshin INEC

    IGP Usman Alkali Baba

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya umarci kwamashinonin rundunar na jihohi da su ƙaddamar da tsarin ba da kariya ga ayyukan babban zaɓe na 2023 da ke ƙaratowa.

    Kazalika, babban sufeton ya umarce su da su tabbatar da tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa wuraren da suka dace.

    "Sufeto janar ya bayyana cewa tashin hankali da kalaman ƙiyayya da barazana da rashin jimuri da yaɗa labaran ƙarya da tsattsauran ra'ayin siyasa baraza ne ga dimokuraɗiyyarmu da tsaron ƙasa," a cewar sanarwar da Kakakin 'Yan Sanda na Ƙasa Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Lahadi.

    Tsarin ya ƙunshi yin aiki tare da sauran jami'an tsaro na ƙasar da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki don lalubo hanyoyin tsaurara tsaro a ofisoshin hukumar zaɓe ta INEC.

    A ranar 25 ga watan Fabarairun 2023 za a fara kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen da 'yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da 'yan majalisar tarayya da na jihohi.

    Haka nan, IGP Alkali ya nemi jama'ar gari su taimaka wa jami'an tsaro "a yunƙurinta na kare rayuka a lokacin da kuma bayan zaɓen 2023".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Sarkin Musulmi ya buƙaci Miyetti Allah ta taimaka wa gwamnati kan matsalar tsaro

    Sarkin musulmi

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

    Yayin da yake magana a Abuja babban birnin ƙasar lokacin bikin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar, sarkin Musulmin ya ce al'ummar Fulani makiya masu son zaman lafiya ne.

    Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci, ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar da su yi ƙoƙarin taimaka wa gwamnati wajen magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

  8. An rantsar da Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar Osun

    Adeleke

    Asalin hoton, Shina Abubakar

    An rantsar da Sen. Ademola Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar Osun.

    Babban Alkalin Alkalan jihar Justice Adepele Ojo ne ya rantsar da sabon gwamnan tare da mataimakinsa a filin wasa na Osogbo babban birnin jihar.

    Yayin da yake jawabi bayan shan rantsuwar kama aikin mista Adeleke ya ce zai gyara abin da ya kira ''rashin adalci'' da cin hanci ko wasu tsare-tsare da gwamnatocin da suka gabata suka aikata wa al'umar jihar.

    Ya ƙara da cewa “Ina so in faɗa cewa tun daga fannin ilimi da lafiya da ɓangaren ma'adinai, da fannin noma da tituna da ruwan sha ba za su ƙara zama matsalolin jiharmu ba kamar yadda suke a baya''.

    A watan Yuli ne mista Adeleke na jam'iyyar PDP ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar, inda ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa gwamna mai ci Adegboyega Oyetola na jam'iyyar APC.

  9. Hatsarin mota ya kashe mutum uku tare da jikkata tara a Ogun

    FRSC

    Asalin hoton, others

    Mutum uku sun mutu yayin da wasu tara suka jikkata sakamakon wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a daidai jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    A cikin wata sanarwa da hukumar kiyaye aukuwar hadura ta ƙasa reshen jihar Ogun ta fitar ta ce hatsarin ya auku ne ranar Asabar sakamakon gudun wuce kima tare da fashewar taya, lamarin da ya sa motar ta kubce wa direban.

    Babban kwamandan hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta jihar Ogun Ahmed Umar, ya shawarci masu amfani da ababen hawa da su riƙa lura da tayoyin ababen hawarsu da inji da wuta (signal) da sauran abubuwan da suka kamata a kowanne lokaci, kafin su fara amfani da su.

    Ana dai yawan samun haɗuran mota a kan titunan Najeriya, lamarin da ake yawan dangantawa da rashin kyawun hanyoyi da tukin ganganci da kuma gudun wuce kima daga ɓangaren direbobin ƙasar.

  10. NDLEA ta kama dilan ƙwaya da ya yi niyyar zuwa Saudiyya

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar Hana sha da Fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta ce ta kama wani dilan ƙwaya da ta daɗe tana nemansa ruwa a jallo.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama mutumin ne a lokacin da yake ƙoƙarin safarar hodar ibilis - maƙare cikin takalma - zuwa ƙasar Saudiyya

    Haka kuma hukumar ta ce ta ƙwace hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogiram huɗu daga wani mutum da ya koma ƙasar daga Brazil.

    A makon da ya gabata ma hukumar ta kama wata bazawara da ta yi yunƙurin tafiya da hodar ibilis zuwa Saudiyya a cikin takalmanta.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Shugaban ƙasar da ya shafe shekara 43 a kan mulki ya sake cin zaɓe

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Equatorial Guinean Teodoro Obiang Nguema Mbasogo mai shekara 80 a duniya ya sake lashe zaɓen ƙasar.

    Mista Obiang -wanda ya fi kowanne shugaban ƙasa daɗewa a kan karagar mulki - ya lashe zaɓen da kashi 95 cikin ɗari na kuri'un da aka kaɗa a zaɓen da ka gudanar makon da ya gabata.

    "Zaɓen ya sake tabbatar mana da nasara'' in ji mataimakin shugaban ƙasar Teodoro Nguema Obiang Mangue - wanda ɗa ne ga shugaban ƙasar.

    An samu 'yan takara a jam'iyyun adawa a zaɓen, to amma dama ba a yi tunanin za su iya cin zaɓen ba.

    'Yan adawa a ƙasar na zargin shugaban da naɗa danginsa a manyan muƙaman gwamnatinsa.

    Mista Obiang ya karɓi mulkin ƙasar a shekarar 1979 bayan juyin mulkin soji.

    A shekarar 1968 ne dai ƙasar ta samu 'yancin kai inda kawo yanzu ta yi shugabannin ƙasa biyu Francisco Macias Nguema sai kuma mista Obiang.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama na zargin shugabannin biyu da take haƙƙin bil adama.

  12. SERAP ta kai gwamnatin Najeriya ƙara kotun ECOWAS

    SERAP

    Asalin hoton, SERAP

    Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta ta kai ƙarar gwamnatin ƙasar gaban kotun ECOWAS saboda kasa binciken batun bututan da ake zargin satar mai da su tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022.

    ƙungiyar na so gwamnatin ƙasar ta binciko tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu kan batun a gaban kotu.

    Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan aka gano bututu 58 da ake amfani da su wajen satar man, bayan da aka ja su zuwa tsakiyar teku, inda ake loda man a manyan jiragen ruwa domin sayar da shi.

    Najeriya dai ta dogara ne kacokan kan ɗanyen mai da take haƙowa kuma kuɗaɗen shigarta na cikin matsala saboda satar man, kamar yadda jami'ai ke faɗa.

  13. Hikayata 2022: Labarin 'Al'ummata'

    A wannan makon mun kawo muku labarin ‘Al’ummata’ wanda ya zo na uku a gasar rubutu ta mata zalla ta BBC Hausa wato Hikayata.

    Maryam Muhammad Sani ce ta rubuta ta kuma karanta da kanta.

    Bayanan sautiLatsa lasafikar da ke sama domin sauraron labarin
  14. Jami'an shige da fice sun kama 'yan ci-ranin Chadi da Togo 33 a Najeriya

    .

    Asalin hoton, others

    Jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya reshen jihar Ogun ta kama 'yan ci-ranin Chadi da Togo 33 a wasu yankunan jihar biyu.

    Rahotonni sun ambato babban kwantirola mai lura da jihar Yakubu Jibrin na cewa waɗanda ake zargin ba su da takardar izinin shiga Najeriya sannan ba sa ɗauke da ko wacce irin shaida.

    Ya kuma alkawarce cewa za a mayar da mutanen ƙasashensu bayan an yi tuntuɓa tsakanin ƙasashen nasu na asali da kuma gwamnatin Najeriya.

  15. Abin da ke janyo zubewar haƙora lokacin tsufa

    Shin kun san dalilin da yake sa haƙoran mutum ke zubewa a lokacin da ya tsufa? Kuma me mutum zai yi domin magance haka?

    Dakta Isah Tijjani Dawaki da ke asibitin Mallam Aminu Kano ya amsa wadannan tambayo tare da ƙarin bayani

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  16. An yanke wa mutumin da aka kama da katin zaɓe 101 hukuncin shekara ɗaya

    katiun zaɓe

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce kotun majistare da ke Sokoto ta yanke wa wani mutum mai suna Nasiru Idris da aka kama da tarin katin zaɓe 101 hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta ta Tuwita, ta ce a 'yan makonnin da suka gabata jami'an 'yan sanda sun kama mutane a wurare daban-daban a faɗin ƙasar ɗauke da katunan zaɓe masu yawa.

    Ta ce a ɗaya daga cikinsu ne 'yan sanda suka kammala bincike a kansa tare da gurfanar da shi a gaban kotu, inda kuma kotun ta yanke masa wannan hukunci

    Haka kuma hukumar ta INEC ta ce nan gaba kaɗan ne za a gurfanar da mutanen da aka kama da tarin katunan zaɓen a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

    A cikin sanarwar hukumar ta ce za ta yi taron wayar da kai da duka kwamishinonin zaɓe na jijohi 36 na fadin ƙasar daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa biyu ga watan Disamba.

    A ƙarshen ganawar ne hukumar za ta sanar da ranakun da za ta fara raba katinan zaɓe a faɗin kasar.

    Haka kuma hukumar ta yaba wa 'yan ƙasar bisa hakuri da fahimta da suka nuna, musamman ga waɗande ke buƙatar a sauya musu katunan da waɗanda ke son a sauya musu wurin rajistar

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. 'Yan sanda sun kama matashi kan zargin yi wa yaro fyade har ya mutu

    'yan sanda

    Asalin hoton, Nig. Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wani matashi da take zargi da yi wa wani ƙaramin yaro mai shekara biyar fyade, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yaron.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya sanya wa hannu ya ce an kama matashin mai shekara 36 bayan da shugaban ƙungiyar ci gaban al'umar yankin ya kai ƙorafin matashi zuwa ofishin 'yan sanda.

    “Bayan samun rahoton sai shugaban 'yan sanda na ofishin ya yi gaggawar tura jami'an tsaro inda nan take suka kamo wanda ake zargin'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    “A yayin da aka tuhumi wanda ake zargin ya tabbatar wa da 'yan sanda cewa shi mai neman maza ne dalilin da ya sa kenan ya haike wa yaron''.

    Tuni dai kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun sashen binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan jihar domin faɗada bincike.

  18. Ana ci gaba da aikin ceton waɗanda zabtarewar ƙasa ta rutsa da su a Italiya

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Masu aikin ceto a Italiya na ci gaba aikin zaƙulo wadanda zabtarewar ƙasa ta rutsa da su a a tsiburin Ischia ranar Asabar.

    Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutum guda, yayin da har yanzu ba a ga mutum 11 ba. Nan gaba kaɗan ne a yau 'yan majalisar dokokin ƙasar za su yi zaman gaggawa domin tattauna batun.

    A jiya Asabar ne ruwan sama mai ƙarfin gaske tare da zabtarewar ƙasa suka ɗaiɗaita garin Casamicciola da ke kan tsauni.

    Shi ma tsiburin Ischia mai yawan jama'a, waɗanda suka gina gidaje ba bisa ƙa'ida ba, na daga cikin inda aka samu ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasar.

  19. Samar da makamin nukiliya mafi girma a duniya ne burinmu - Kim Jong-un

    Kim Jong-un

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce aniyar ƙasarsa ita ce samar da makamin nukiliya mafi girma a duniya.

    Mista Kim ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da kafar yaɗa labaran ƙasar, a daidai lokacin da yake bayani kan ƙaddamar da makamin nukiliya da na linzami masu cin dogon zongo da ƙasar ta ƙera a farkon watan nan.

    Ya kuma raɗa wa makamin suna da 'Gwarzon ƙasa' haka kuma ya nuna tare da tabbatar da ƙarfin ƙasar a wannan fanni.

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya dai ya haramta gwajin irin wannan makamin, kuma Amurka ta buƙaci Koriya ta Arewan da ta sauya matsayinta kan wannan, sannan kuma ta jira abin da zai biyo baya.

  20. Maraba

    Masu binmu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi da ake cikin hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan an tashi lafiya, yau ma kamar kullum za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa Najeriya da sauran sassan duniya.

    Haka kuma kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.