Amfanin cire takalmi lokacin shiga ɗaki ga lafiyar ɗan'adam

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan mutum ya shiga cikin gida da talkami, ba datti kaɗai ba ne ke shiga gidan.
  • Marubuci, Manal Mohammed
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, My Conversation

Mahaifiyata ta kasance ta saka min doka ta cire takalmi yayin shiga cikin gida. Ba ta la'akari da ko ma waye zai ziyarce gidanmu ba, ko da a ce baƙo ne ko makwabci, dole ne sai sun cire takalmi kafin shiga cikin gida.

Lokacin da nake ƙarama, na yi tunanin mahaifiyata na da tsauri. Amma lokacin da na fara fahimtar kaina na fara girma, shine na gane cewa ba tsafta kaɗai take yi wa haka ba, harda ma saboda lura da lafiyarmu.

Tsafta tabbas tana da mahimmanci. Amma idan ana maganar takalma, abin da yake haɗari shine datti wanda ba za a iya ganinsa ba wanda ke taruwa a ƙasan takalmanku.

Pia unaweza kusoma:

Takalman da aka sa a waje galibi suna daukar ƙwayoyin cuta da ƙwayoyin baktiriya da ke haifar da matsalolin lafiya.

Idan aka yi la'akari da yawan wuraren da ake takawa da takalmanka da suka haɗa da banɗakuna da titi da asibitoci da lambuna da dai sauransu, za a fahimci cewa tabba, aka kwasan ƙwayoyin cuta daga takalmi.

A cewar wani bincike da Jami'ar Arizona a Amurka ta gudanar, kashi 96% na takalma suna ɗauke da baktiriya mai suna coliform, wanda ake samu a cikin fitsari.

Abin mamakin kuma kashi 27% na takalma na ɗauke da ƙwayar cutar baktiriya na E. coli, wanda ke haifar da cututtuka mafi haɗari ga mutane.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a iya tafiya ba takalmi a cikin gida ko kuma a saka talkamin da aka ware domin sakawa cikin gida.

Yayin da wasu nau'ikan baktiriya na E. coli ba su da haɗari ga mutane, wani nau'in baktiriya mai suna Shiga, wanda ke haifar da gudawa mai jini, yana iya haifar da yanayi mai haɗari da ake kira hemolytic uremic syndrome—cuta da za ta iya haifar da gazawar ƙoda kuma a ƙarshe ta kai ga mutuwa.

Yara ƙasa da shekaru biyar suna cikin haɗari mafi girma saboda tsarin garkuwar jikin su da bai cika ba, da kuma yadda suke yawan sa hannayensu a baki.

Koyaya, baktiriyar E. coli ba shi ne kawai ƙwayar cutar da zai iya kasancewa a cikin gida ba, musamman a cikin ɗakin zama.

Takalma suna iya kasancewa ɗauke da ƙwayoyin baktiriya ta Clostridium, wanda ke haifar da gudawa da wasu lokuta cututtuka masu tsanani.

Ba ƙwayoyin cuta ba kaɗai

Haɗarin lafiya ba ya tsaya ne kawai ga baktiriya ba.

Takalman da aka saka aka fita da su suna ɗauke da sinadarai masu haɗari da kuma ƙwayoyin cuta masu tayar da hankali.

ƙwayar cutar Plumbi, wanda ake samunsa a cikin yawan ƙura ko a ƙasar yankunan birane, wata cuta ce mai haɗari da za ta iya shafar ci gaban kwakwalwar yaro kuma ta haifar da matsalolin tunani na dindindin.

Bugu da ƙari, sinadaran pollen na iya manne wa da takalma, wanda zai iya haifar da rashin lafiyar numfashi da kuma matsalolin allergies ko da a cikin gida.

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pollen na iya manne wa da takalma, wanda zai iya haifar da rashin lafiyar numfashi da kuma matsalolin allergies ko da a cikin gida.

Abin da ya kamata a fi damuwa da shi shine, hanyoyin tituna na ɗauke da sinadarai masu hadari da zasu iya haifar da ciwon daji. Wani bincike da aka yi a Amurka ya gano cewa waɗannan sinadarai na iya shiga cikin gidaje kuma su taru cikin kura a cikin gida.

To, wane ne ya fi fuskantar wannan haɗari?

Yara da dabbobi ne suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cuta daga takalma masu datti da aka shiga da su cikin gida.

Yara na yawo, wasu na rarrafe suna wasa a ƙasa, kuma sau da yawa suna saka hannayensu a bakinsu. Dabbobi kuma suna lashe ƙafafunsu bayan sun yi yawo a wurarai da dama.

Tsaftataccen ƙasa ne lafiyar gida

Cire takalma kafin shiga cikin gida shine ɗaya daga cikin matakai mafi sauƙi da tasiri wajen kare lafiyar iyali.

Kuma aiwatar da wannan mataki ba shi da wahala kwata-kwata, cire takalmi ne kawai kafin a shiga cikin gida wanda idan aka yi, an raba cikin gidan da ditti da kuma ƙwayar cuttutuka,