Ko an maye gurbin Saratu Daso a Kannywood shekara guda bayan rasuwarta?

Asalin hoton, Daso Instagram
Shekara kwana, in ji ƴan magana inda kwanci-tashi fitacciyar jarumar Kannywood ɗin, marigayiya Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso take cika shekara ɗaya cur da rasuwa.
A ranar Talata, 9 ga watan Afrilun 2024, ana tsaka da shirye-shiryen ƙaramar Sallah ta rasu.
Jarumar ta yi rasuwa ce ta fuju'a, domin an kwanta da ita lafiya ƙalau, amma aka wayi gari ba tare da ita ba.
Daso jaruma ce mai taka rawa daban-daban a masana'antar fim ta Kannywood, inda ta ƙware taka rawar rigima da rashin haƙuri, da kuma rawar barkwanci a wasu lokutan.
Ba ƴan uwa da iyalai ba ne kaɗai suka yi rashin marigayiyar, domin akwai almajirai da marayu da take ɗawainiya da su.
Sannan kuma, bayan ƴan uwanta da marayu da almajirai, ita kanta masana'antar da ta fito da ita duniya akwai rawar da ake ganin ita kaɗai take iya takawa, wanda hakan ya sa wasu suke tunanin akwai giɓin da ta bari wagege.
Wane irin giɓi Daso ta bari a Kannywood?

Asalin hoton, Daso Facebook
A game da irin giɓin da ta bari a masana'antar Kannywood, fitaccen mai shiryan fina-finai a Kannywood, Alhaji Naziru Auwal, wanda aka fi sani da Ɗan Hajiya ya ce giɓi ne babba wanda da wahala a iya mayewa.
Ya ce, "Hajiya Daso mutum ce wadda take taka rawa ta musamman a fim wanda ba kowa ba ne yake iya takawa. Idan ka duba kusan fim ɗinta na ƙarshe shi ne fim ɗina mai suna Umarni. Mun yi zango na farko da ita ne sai Allah ya yi mata rasuwa."
Ya ce duk da cewa a lokuta da dama idan aka samu irin haka ana musanya jarumi ne, "amma na yi iya dubawar da zan iya, amma har ga Allah ban samu abin da nake so ba, sai dai kawai kwatantawa, haka kawai na haƙura na kashe fitowar. Don haka gaskiya ta bar mana babban giɓi, fatanmu shi ne Allah ya mata rahama," in ji shi.
Shi ma Habibu Maaruf Abdu, mai shairhi kan finafinai, ya amince da hakan, inda shi ma ya ce akwai giɓi babba da marigayiyar ta bari wanda shi ma yake ganin zai yi wahala a iya cikewa nan kusa.
Me ya sa har yanzu ba a maye gurbinta ba?
A game da abin da ya sa har yanzu ba a iya cike gurbinta ba a masana'antar, Ɗan Hajiya ya ce akwai bambancin jaruman baya da na yanzu.
"Gaskiya yawanci yadda masana'antar take a yanzu, jaruman da suka yi gwagwarmaya a baya sun fi na yanzu riƙe fim ɗin a matsayin sana'a. Sun bambanta da na yanzu, inda wasu ke yin fim ɗin kawai wataƙila saboda yana ba su sha'awa. Irin su Hajiya Daso da gaske suke yi fim, kuma komai take yi da gaske take yi. Za ka ga ko almajiran da take ciyarwa sun yi rashinta sosai."
A nasa ɓangaren, Malam Habib Ma'aruf ya ce a harkar fim dama ba a samun makwafin duk wani gwani a lokaci guda cikin sauƙi.
"Ba za a iya samun ƙwararre a rana ɗaya ba. Ita Daso ta jima tana taka rawa a fim, wanda hakan ya ba ta damar samun ƙwarewa ta musamman akan irin rawar da take takawa. Kana ganinta a fim za ka shiga shauƙi saboda ka san za a yi abin dariya, ko makirci, ko masifa, da dai sauran irin rawar da take takawa," in ji shi.
Masanin harkokin finafinan ya ce rasuwar jarumar ya baiwa wasu jaruman dama su nuna irin baiwar da Allah ya ba su a wannan ɓangaren, "misali Adama ta Daɗin kowa, amma dai ba su kai ƙwarewar Daso ba."
Haka kuma mai sharhin ya ƙara da cewa akwai buƙatar a samu irin ƙarin jarumai irin su Daso, "In muka duba za mu ga Daso tana taka rawar babbar mace, musamman mahaifiya. To, yawanci labaran finafinan Hausa suna buƙatar irin wannan fitowar. Saboda haka akwai buƙatar a samu jarumai ƙwararru da za su taka irin rawar don ƙara wa finafinai kyau.
"Misali, fim mai dogon Zango mai suna Umarni, wanda shi ne fim ɗin Daso na ƙarshe, an nuna ta a matsayin uwa wadda take kishi da matar ɗanta. Ta ƙara wa fim ɗin armashi sosai saboda yadda ta yi aikinta cikin ƙwarewa."
A ƙarshe Habibu ya yi kira ga masu shirya finafinai da su ƙara ƙoƙari wajen yin finafinai masu inganci. "Su daina yin finafinai kwaikwayon India ko waɗanda aka taɓa yin irinsu a baya."
A game da abin da yake tunawa game da ita, musamman ganin irin rawar da take takawa a finafinai, Naziru Ɗan Hajiya wanda ya yi aikace-aikace da ita ya ce mutumiyar kirkice mai cika alƙawari.
"Ba ta da faɗa, mutumiyar kirki ce, mai sauƙin kai da haƙuri da cika alƙawari. Lokacin da muke fim ɗin umarni - a lokacin azumin da ta rasu ne - sai ta roƙi alfarmar za ta riƙa tafiyar ƙarfe 5 na yamma saboda abincin almajirai da take dafawa. Rabuwarmu ta ƙarshe ta kira ni ta ban shawara game da aikin da muka yi, sannan ta yi addu'a."