Matashiyar da ta zama Injiniya don magance matsalar rashin wuta a garinsu

.

Asalin hoton, NOLWAZI ZULU

Matashiyar Injiniya Nolwazi Zulu ta ce tun tana ƙarama ta yanke shawarar za ta yi ''wani abu'' domin magance matsalar yawan ɗaukewar wuta da ke addabar al'ummar yankinta.

A yanzu da take shekara 25 Misis Zulu na zaune a wani ƙauye a lardin Kwazulu-Natal da ke gabashin Afirka ta Kudu.

Kamar dai sauran al'ummar ƙasar lardinsu na fama da yawan ɗaukewar wutar lantarki tun shekarar 2008.

Wanna kuma na faruwa ne sakamakon babbar tashar wutar lantarkin ƙasar da kuma sauran tasoshin da ke amfani da ma'adinin coal na fama da ƙarancin ma'adinin.

A ƙoƙarin da take wajen magance wannan matsala tare kuma da ƙoƙarin magance gurɓata muhalli, a yanzu gwamnatin ƙasar na yunƙuri wajen inganta harkokin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a faɗin ƙasar.

Domin cimma haka ana buƙatar ƙarfafa gwiwwa ga kamfanonin samar da lantarki mai amfani da hasken rana.

.

Asalin hoton, ART SOLAR

A yanzu ƙasar na buƙatar ƙarin megawat 1,000 na wutar lantarki daga hasken sola domin samar da wuta ga gidaje akalla miliyan ɗaya a ƙasar.

A yanzu kashi 11 cikin 100 ne na wutar ƙasar ke zuwa daga tashar lantarkin ƙasar.

Kashi 0.9 ne kawai na wutar ke zuwa da hasken rana, a ƙasar da ke samun hasken rana na tsawon sa'o'i takwas zuwa 10 a rana.

Kamfanin da ya yi nasarar samun aikin samar da wutar solar shi ne kamfanin 'Art Solar' kamfani ɗaya tilo na cikin ƙasar dake samar da wutar mai amfani da hasken rana.

A kamfanin ne kuma misis Zulu ke aiki, yayin da take ci gaba da karatun diploma a fannin samar da wutar lantarki a jami'ar fasaha ta birnin Durban.

Misis zulu ta ce faya-fayan sola za su taimaka wajen samar da wuta a gidajen da ke yankunan karkara.

.

Asalin hoton, ART SOLAR

''Ina son buɗe reshen kamfanin Art Solar a Ulundi (ƙauyen da ta taso), domin samar da lantarki ga ƙauyena'', in ji misis Zulu. ''Yana da rahusa da sauƙi, kuma zai magance mana matsalar ɗaukewar lantarki da muke fama da ita, zai sauya rayuwar mutane da dama.

'An buɗe Kamfanin samar da wutar lantarki na 'Art Solar' shekara 12 da suka gabata, inda yake ƙera faya-fayan sola ƙarƙashin wani kamfanin ƙasar Jamus mai suna Bosch. A yanzu kamfanin na samar da faya-fayan sola ga ƙasar da ma sauran ƙasashen duniya, tare da haɗin gwiwwar kamfanin Talesun na ƙasar Jamus.

Babban manajan kamfanin Viren Gosai ya ce buƙatar gwamnati da wutar sola, ya taimaka wa kamfaninmu wajen samun ƙwarin gwiwwar buɗe sabon wuri da zai ba mu damar samar da faya-fayan sola 650,000 a shekara.

.

Asalin hoton, ZOLA ENERGY

A ƙasashen yankin gabashin Afirka kamar Tanzaniya akwai wani kamfanin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai suna 'Zola Electric' da ke ƙoƙarin magance matsalar wutar lantarki da ke damun ƙasar.

Baya ga haɗa faya-fayan solar domin samar wa ƙasar wuta, kamfanin na son kafa wutar sola mai cin gashin kanta domin samar da wutar ga garuruwa da ƙauyukan ƙasar.

Babban manajan kamfanin na Zola Bill Lenihan ya ce suna buƙatar su faɗaɗa bincike game da samar da wutar lantarki musamman a nahiyaer Afirka

Ya ƙara da cewa a yanzu da ake ƙoƙarin kauce wa amfanin da makamashi mai gurɓata muhalli, mutane sun fara tunanin cewa dogara da hanya ɗaya wajen samar da wutar lantarki ba zai zama mafita gare mu ba.

Idan muka koma Afirka ta kudu Jay Naidoo, wani tsohon minista ne ƙarƙashin mulkin shugaba Nelson Mandela, ya daɗe yana da tunanin samar da wutar lantarki mai cin gashin kanta musamman ga mazauna yankunan karkara.

.

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce ''manufarmu ita ce ƙarfafa wa mazauna karkara musaman mata da matasa domin inganta tattalin arzikinmu''.

Har yanzu wutar lantarki matsala ce, kuma matsalar tana kawo cikas ga ci gaban al'ummarmu.

''Matuƙar al'ummar tana da wutar lantarki da take buƙata, hakan zai sa al'ummarmu su samu sana'o'i wanda hakan kuma zai taimaka wajen inganta tattalin arzikinmu''.

Ƙungiyoyin kare muhalli a Afirka ta Kudu sun daɗe suna kiraye-kirayen amfani da lantarkin da ba ya gurɓata muhalli.

.

Asalin hoton, MAKOMA LEKALAKALA

"Mun kasa cimma zuba jari a harkar wutar sola," in ji daraktar ƙungiyar Earthlife, Makoma Lekalakala.

Ta ƙara da cewa ''ya kamata a ce yanzu mun wuce matsalar ɗaukewar wutar lantaraki a ƙasarmu''.

"A maimakon haka sai muka tsaya muna ɓata lokacinmu muna tutiya da arzikin ma'adinin coal''.

''Ya kamata a ce mun daɗe da fara amfani da wutar sola'' kamar yadda ta ce.

To sai dai ma'aikatar ma'adinai da makamshi ta ƙasar ta ƙi cewa komai ba game da waɗannan kalamai.

A yayin da kamfanin 'Art Solar' ke shirin ƙara yawan faya-fayan sola da yake samarwa, misis Zulu ta ce tana farin ciki yadda kamfanin ke shirin buɗe reshe a kauyenta.