Ana zargin wata mata da kashe jaririn kishiyarta da guba a jihar Kaduna

Asalin hoton, STRINGER
A Najeriya, rundunar 'yan sandan kasar ta damke wata mata da ke kauyen Malari a yankin karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, bisa zargin kisan wani jinjirin kishiyarta dan wata uku da haihuwa.
Al'amarin ya auku ne a makon da ya gabata a gidan da matar ke zaune tare da kishiyar tata, yayin da uwar jinjirin ta shiga bandaki, ta bar yaron shi kadai a waje. Tana dawowa sai ta tarar da jaririn nata a hannun uwar gidan.
Kakakin 'yansandan jihar DSP Mansir Hassan, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Mayu:
''Akwai wata mata mai suna Maryam Ibrahim tana da dan da jariri dan wata uku, wadda tana da kishiya suna zaune a gida daya, sai ta dan shiga bayi, fitowa kenan ta bar yaron a waje sai ta zo ta tarad da kishiyarta mai suna Zaliha tana rike da yaron.''
''Bayan ta amshi yaron sai ta ga kumfa na fitowa daga bakin yaron da kuma yanayin nau'inshi yana canzawa. Wannan ya sa aka garzaya da yaron asibiti, inda kafin a garzaya da shi ma asibitin Allah Ya amshi rayuwarshi.
Mai magana da yawun 'yansandan ya yi wa BBC karain bayani da cewa, bayan sun samu wannan labari ne suka tura jami'ansu inda suka yi nasarar kama wannan mata Zaliha, wadda bayan bincike ta tabbatar musu da kanta cewa, ta ba wannan yaro ne maganin asid ya sha domin ta kashe shi saboda kishi.
DSP Hassan ya ce, ''Abin da ya tabbatar mana bayan bincike shi ne, akwai kanin shi mai gidan wanda ya sayo mata asid din bayan ta gaya mishi cewa ita fa ba ta sha'awar ganin wannan yaron.
''Wannan ta sa shi wannan yaro Lawal Muhammad ya sayo mata wannan asid ya kawo mata,wanda shi wannan Lawal Muhammad muna nan mun zurfafa bincike in Allah Ya yarda za mu kama shi nan ba da jimawa domin mu gurfanar da shi a gaban kuliya.
'Yansandan sun ce a binciken da suka yi kafin wannan lamari sun gano cewa da farko ana samun dan sabani tsakanin ita Zaliha wato uwargida da amaryar tata wadda wannan ita ce haihuwarta ta farko, to amma daga baya an samu maslaha msatalar ta ragu sun sasanta.
Kakakin ya ce, '' Kusan abubuwan sun zo sun lafa, wanda ba mu sani ba ashe ita kwanton-bauna take yi domin ta tabbatar da cewa ta kawar da jaririn da ta haifa.''
''Duk wasu bayanai da muke nema tana ba mu hadin kai kuma da mun kammala bincike in shaa Allahu za mu gurfanar da ita a gaban kotu domin ta amsa hukunci daidai da laifin da ta aikata.
''Hakazalika shi ma kanin mijin wanda shi ne ya sayo mata wannan magani ya ba ta domin ta ba wannan yaro ta kashe shi, shi ma muna nan mun baza jami'anmu in Allah Ya yarda ma za mu kama shi.'' In ji shi.