...Daga Bakin Mai Ita tare da Zainab ta Labarina
Daga Bakin Mai Ita, shiri ne da ke tattaunawa da taurarin fina-finan Hausa da wasu fitattun mutane, domin yin bayani game da rayuwarsu ta yau da kullum.
A shirin na wannan makon mun yi hira da Nana Firdausi Yahaya, wadda ta fito a matsayin matar Al'ameen a cikin shirin Labarina, kuma take ci gaba da taka rawa a finafinan Hausa masu dogon zango da dama.
Ta ce asalinta 'yar ƙasar Jamhuriyar Nijar ce, amma ita da iyayenta suna zaune ne a jihar Sokoto da ke Najeriya.
Ta yi makarantar Furamarenta da na Sakandire a jihar Sokoto.
Nana Firdausi ta ce ta shigar masana'antar Kannywood ne ta hanyar wani ɗan'uwanta da ya kaita wajen Aminu Saira, wanda shi ne Ubangidanta a masana'antar.
Zainab ta ce fim ɗinta na farko da ta fara fitowa shi ne Labarina.