...Daga Bakin Mai Ita tare da mawaƙi Ahmad Delta
Cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun tattauna da Ahmad Idris Abdulkarim da aka fi sani da Ahmad Delta.
An haifi mawaƙin a garin Warri na jihar Delta da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Yayi karatunsa na furamare da sakandire a jihar Delta, kafin ya tafi jihar Sokoto da nufin faɗaɗa karatunsa, kodayake haƙarsa a ta cimma ruwa ba, sakamakon wasu matsaloli.
Ahmad Delta ya ce ya fara waƙa ne a Sokoto lokacin wani biki a gidan su wani abokinsa, inda aka gayyaci wani mawaƙi, wanda bai je wurin bikin da wuri ba, kan haka ne ya gwada sa'arsa kuma ya ga zai iya, daga nan ya fara waƙa.
Ya ce waƙoƙinsa da suka fi shahara sun haɗa da waƙar Mafarki, da Na Ci Dubu, da kuma Lubiya.
Amma ya ce waƙar da ta fi burge shi ita ce Mafarki saboda yadda ta taɓo wani ɓangare cikin rayuwarsa.
Ma'aikata:
Ɗaukar bidiyo: Fatawul Mohammed