Auren ƴan Kannywood bakwai da suka ja hankali

Asalin hoton, Dauda Kahutu Rarara/Facebook
Shagalin bikin mawaƙi Dauda Kahutu da amaryarsa Aishatu Humaira na cigaba da jan hankali, inda ake cigaba da tattaunawa kan bikin a kafofin sadarwa musamman bayan shagalin cin abincin dare na bikin da aka yi a jihar Kano.
Abubuwan da suka ɗauki hankali sun haɗa da adon da amarya da ango suka sha, kwalliyar da aka yi a zauren walima da kuma manyan baƙin da suka halarci daurin auren da kuma walima.
Biki ne da aka yi na ƙasaita musamman ganin yadda mawaƙi Rarara ke jan zarensa a wannan lokaci har ma wasu ke kwatanta shi da shahararrun mawaƙan ƙasar Hausa da suka gabata, sanadiyyar baje-kolin basirar da yake yi a cikin waƙoƙinsa.
Ba wannan ne karon farko da jaruman masana'antar suke yin shagalin biki na ƙasaita, wanda ke ɗaukar hankalin mutane ba.
BBC ta rairayo wasu bukukuwa guda bakwai da aka yi a masana'antar da suka ja hankali.
Dauda Rarara da Aisha Humaira

Asalin hoton, FB/Dauda Kahutu Rarara
A ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2025 ce aka ɗaura auren Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa Aisha Ahmad wadda aka fi sani da Aisha Humaira a garin Maiduguri na jihar Borno.
An daɗe ana rade-raɗin akwai soyayya tsakanin ma'auratan biyu, amma a duk lokacin da aka tambaye su, sai su ce aiki ne kawai.
A shekarar da ta gabata mawaƙin ya rera waƙar 'Aisha', wadda a ciki ya baza kalaman soyayya har aka yi ta cewa da ita yake yi. Amma sai aka yi amfani da waƙar a fim ɗin jarumar mai suna 'A cikin biyu' wanda Ali Nuhu ya hau.
Dauda Kahutu Rarara fitaccen mawaƙi ne da ya daɗe yana jan zarensa, musamman a waƙoƙin siyasa, kafin daga baya ya fara rikiɗewa zuwa kafofin soyayya da wayar da kan mutane.
Masoyansa na masa kallon mawaƙin da ya fi tashe a wannan zamanin, musamman ganin yadda waƙoƙinsa suke jan hankalin mutane a duk lokacin da ya fitar da sabuwa.
Daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren akwai jiga-jigan ƴansiyasa irin su tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da Mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta Najeriya Sanata Barau Jibrin da sauransu.
Abubakar Bashir Maishadda da Hassana Muhammad

Asalin hoton, Abubakar Bashir Maishadda
Abubakar Bashir Maishadda mai shirya finafinai ne a masana'antar Kannywood wanda ake wa laƙabi da 'king of box office' saboda yadda finafinansa suka fi samar da kuɗi a sinima.
Furodusan ya aure jaruma Hassana Muhammad ne, wadda ta ja wasu finafinan kamfaninsa, ciki har da Hauwa Kulu da sauransu.
An ɗaura aurensu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris na shekarar 2022 a Masallacin Murtala da ke jihar Kano.
Maishadda ya yi aure ne a lokacin da finafinansa suke tashe a masana'antar, inda yake fitar da finafinai manya tare da jarumai mata masu tashe.
Hakan ya sa aka riƙa alaƙanta shi da jarumai mata da yawa da suke fitowa a finafinansa.
Daga cikin waɗanda aka riƙa alaƙanta shi da su akwai jaruma Maryam Yahaya, kafin daga baya ya sanar da aurensa da Hassana.
Sani Danja da Mansurah Isah

Asalin hoton, @mansurah_isah
Ɗaya daga cikin bikin ƴan Kannywood da za a daɗe ba a manta da shi ba shi ne na taurari biyu da suke tashe a lokacin da suka yi aure, wato Sani Musa Danja da Mansurah Isah.
A ranar 14 ga Yuli na shekarar 2007 ce aka yi bikin auren jaruman, inda aka gudanar da biki na kece-raini da ƙasaita.
Sani Danja ya yi tashe da farin jini wurin ƴanmata inda aka riƙa alaƙanta shi da taurari mata daban-daban, ɗaya daga ciki da ta yi fice ita ce Maryam Jan kunne, amma daga bisani ya rufe kunnensa ya zaɓi Mansurah Isah.
Sani Danja da Mansurah suna cikin ƴan fim na farko-farko da suka auri juna, kuma suka daɗe suna tare kafin auren ya mutu.
Allah ya albarkaci auren da ƴaƴa huɗu: Iman da Khalifa da Sultan sai kuma ɗan autansu Sudais.
Ummi Rahab da Lilin Baba

Asalin hoton, Lilin Baba/Facebook
Wani auren da ya janyo taƙaddama da muhawara a shafukan sada zumunta shi ne na Ummi Rahab da Lilin Baba.
Ummi ta taso cikin masana'antar Kannywood a matsayin ta hannun damar babban tauraro Adam A. Zango, tun daga fim ɗin da ta fara fitowa wato 'Ummi'.
A lokacin da auren ya taso an yi ta raɗe-raɗin cewa Zango ya yi adawa da auren, sai dai duk da haka an ɗaura auren kuma Ummi da Lilin Baba na ci gaba da zamansu a matsayin mata da miji.
Yayin da wasu ke zargin Ummi Rahab da juya wa wanda ya raine ta a masana'antar baya, wasu kuma sun zargi Zango da ƙoƙarin hana matashiyar rawar gaban hantsi.
An ɗaura auren Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar Asabar 18 ga watan Yulin shekarar 2022 a Tudun Murtala da ke jihar Kano.
Fati Muhammad da Sani Mai Iska

Asalin hoton, Multiple/Social media
Waɗanda suka daɗe suna bibiyar harkokin fim ɗin Hausa sun san irin tashen da Fati Muhammad ta yi, a matsayin ɗaya daga cikin taurari mata na farko-farko da suka haska a masana'antar Kannywood.
Wasu na ganin cewa ya zuwa wannan lokaci babu tauraruwar da ta shiga zukatan masu kallo kamar yadda Fati Muhammad ta yi a lokacin da take zamaninta.
Auren jarumar da Sani Mai Iska ya bai wa mutane da dama mamaki kasancewar an fi alaƙanta ta da wasu fitattun taurari maza.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka riƙa alaƙanta ta da su shi ne babban tauraro Ali Nuhu, bayan rawar da suka taka tare a fina-finai da dama, kamar irin su Sangaya da Mujadala.
Aurenta da Sani Mai Iska ya cigaba da jan hankali musamman ganin yadda suka bar ƙasar zuwa Birtaniya bayan auren.
Sai dai auren ya mutu daga baya, duk da cewa har yanzu ba a san takamaiman abin da ya raba su ba, duk da cewa akwai raɗe-raɗi da dama da ake yaɗawa, amma sun daɗe suna musantawa tare da cewa akwai aminci a tsakaninsu.
Ahmed S. Nuhu da Hafsat Shehu

Asalin hoton, Multiple/Social media
Ɗaya daga cikin auren da masu kallo suka fi yin na'am da shi a tarihin masana'antar Kannywood shi ne na Ahmed S. Nuhu da Hafsat Shehu.
Mutanen biyu sun kasance abin so ga mutane da dama da ke kallon fina-finan Hausa na wancan lokacin.
Hakan bai rasa nasaba da shaidar da aka yi wa Ahmed na kasancewa mai son zaman lafiya ba duk da rikice-rikicen da ake fama da su a masana'antar.
A bangare ɗaya Hafsat kan fito a yawancin fina-finai a matsayin mai sanyin zuciya da fara'a, lamarin da ya sa take burge masu kallo.
Tauraruwar ta fara tashe ne bayan fim ɗinta na Zabari na kamfanin FKD, wanda daga lokacin soyayya ta ƙullu har ta kai ga aure.
Sai dai auren bai daɗe ba, kasancewar ya rasu a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin Azare na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Hafsat ta bayyana a tattaunawarta da BBC cewa tana kewar mijinta har yanzu, inda ta ƙara da cewa ta shiga halin damuwa matuƙa da rashinsa.
Wasila Isma'il da Al'amin Ciroma

Asalin hoton, FB/Wasila Isma'il
Fim ɗin Lerawa Production da ake kira Wasila, shi ne fito da Wasila Isma'il a duniyar fim na ƙasar Hausa.
Aurenta da Al'amin Ciroma ya ja hankali sosai, duk da cewa a lokacin ba a samu yalwatuwar kafofin sada zumunta irin yanzu ba.
Auren ya ɗauki hankali ne saboda ya zo a daidai lokacin da masu kallon finafinan Hausa suke cigaba da tattaunawa game da fim ɗin 'Wasila'
Wasila Isma'il wadda ta fito a matsayin matar Ali Nuhu cikin fim ɗin 'Wasila' bayan tafka soyayya mai ratsa zukata, ta jefa masu kallo cikin jimami bayan cin amanar Jamilu da wani tsohon abokinta mai suna Moɗa.
Soyayyar Wasila da Jamilu na daga cikin soyayya mafi zafi da aka taɓa gani a duniyar fina-finan Hausa.