Manyan 'yanbindiga shida da aka kashe lokacin Tinubu

Asalin hoton, Social media/multiple
A daidai lokacin da ake fargabar mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya, wasu na ɗiga alamar tambaya kan me ya sa ake kwan-gaba-kwan-baya a yaƙin.
A tsakanin watan Maris zuwa watan Afrilu, an fuskanci hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, waɗanda ake zargin tsagin Boko Haram na ISWAP da kaiwa, ciki har da waɗanda suka kai sansanin sojoji.
Wannan ya sa masana suke ganin lamarin na da ɗaga hankali musamman ganin ƴan ƙungiyar suna amfani da jirage marasa matuƙa, sannan suna amfani da nakiyoyi da suke birnewa a ƙasa.
Haka kuma masana suna ganin raba hankalin sojojin da suke aikin yaƙi da matsalolin tsaro ya taimaka wajen kasa daƙile matsalar, domin an kwaso wasu manyan makamai da ma sojoji daga arewa maso gabas, aka mayar da su arewa maso yamma domin yaƙi da ƴanbindiga da suma suke cin karensu babu babbaka wajen kisa da garkuwa da mutane domin kuɗin fansa.
Tun fara mulkin Shugaba Bola Tinubu ne jami'an tsaro da gwwamnati suke sanar da samun nasara kan ƴanbindiga, tare da bayyana sunayen waɗanda suka kashe daga cikin manyan jagororin ƴanbindigar a baya, wanda ke alamta samun nasara, duk da cewa wasu na cewa akwai sauran rina a kaba.
A wata maƙala da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya fitar, ya ce daga hawan Tinubu zuwa yanzu jami'an tsaron ƙasar sun kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su aƙalla guda 11,250.
Wannan ya sa BBC ta yi nazari, tare da tattaro wasu manyan ƴanbindiga shida da aka kashe a lokacin mulkin shugaba Tinubu waɗanda suka gawurta.
Ali Kachalla
A watan Disamban shekarar 2023 ne jami'an tsaron Najeriya suka kashe fitaccen ɗanbindiga, Ali Kachalla.
Ali Kachalla, wanda ake kira da Ali Kawaje fitaccen ɗanbindiga da ke alaƙa da Boko Haram, wanda ya yi suna wajen addabar mutanen yankin Kuyambana da Ɗansadau da ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Haka kuma yana shiga wasu yankunan jihohin Kaduna da Neja da Kebbi da Nasarawa, sannan shi ne ya taɓa ɓaro jirgin saman sojin Najeriya a jihar Zamfara a shekarar 2021.
Tun farko, a watan Nuwamban shekarar 2022, rundunar tsaron Najeriya da sunan wasu manyan ƴanbindiga da take nema ruwa a jallo, kuma Ali Kachalla yana ciki, kafin aka samu nasara a kansa.
Boderi Isiyaku

Asalin hoton, KDSG
A watan Fabrailun shekarar 2024 ne sojojin Najeriya na runduna ta ɗaya suka sanar da kashe ɗanbiga, Boderi Isyaku.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna na wancan lokacin, Samuel Aruwan ne ya sanar da labarin a lokacin, inda ya ce an kashe shi bayan musayar wuta tsakaninsa da sojoji a yankin Bada da Riwaya da ke tsakanin ƙaramar hukumar Chikun da Igabi.
Isiyaku Boderi ne ɗanbindiga da ya kitsa garkuwa da ɗalibai 39 daga kwalejin gwamnatin tarayya ta koyon aikin gona a Kaduna. Kuma sojoji sun samu nasarar hallaka shi ne a watan Agustan 2024.
Haka kuma Boderi ne ya kitsa kai hari a cikin kwalejin horas ta hafsan sojojin Najeriya wato NDA da sace ɗaliban jami'ar Greenfield da ke Kaduna.
Halilu Sububu

Asalin hoton, Social media
A watan Satumban shekarar 2024 ne jami'an tsaron Najeriya suka kashe ƙasurgumin ɗanbinga Halilu Buzu wanda aka fi sani da Halilu Sububu wanda ɗan asalin ƙasar Nijar ne bayan dogon lokacin sojojin ƙasar ne nemansa ruwa a jallo bayan ayyana shi a matsayin ɗan ta'adda.
Sojojin dai sun samu nasarar kashe shi ne bayan ɗauki ba ɗaɗi tsakaninsu da gungun ƴanbindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanci a ƙananan hukumomin Zurmi da Anka.
Ana kiransa Halilu Buzu ko kuma Halilu Sububu ko kuma Kachalla Halilu Tubali.
Shi ne shugaban ƴanfashin daji da ke arewa maso yamma baki ɗaya da ke kisa da satar jama'a, sannan ya yi fice wajen fataucin manyan makamai da haƙar ma'adinai da safararsu zuwa ƙasashen waje.
Ɗangote
A watan Afrilun 2024 ne shi ma fitaccen ɗanbindiga Ɗangote ya cimma lokaci a jihar Katsina.
Fitaccen ɗanbindigar ya mutu ne bayan musayar wuta da ya yi da ƴan dabar Kachalla Ɗanƙarami da aka fi sani Gwaska bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a jihar Katsina.
Ɗangote ya fi yin fice ne a yankunan da ke tsakanin jihohin Katsina da Zamfara kafin rikicin na cikin gida ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Isuhu Yellow

Asalin hoton, Nigeria Police, Zamfara Command
A watan Maris ne shekarar 2025 ne kuma jami'an tsaron Najeriya suka sanar da kashe fitaccen ɗanbindiga Kachalla Isuhu Yellow, wanda aka fi sani da Ɗan-Isuhu.
Isuhu Yello ya yi fice wajen garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ne a yankunan jihar Zamfara da wasu yankunan jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa shi ma an kashe shi ne a sanadiyar rikicin cikin gida, wanda ya daɗe a tsakanin dabar Isuhu da wasu ɓangarorin.
Ɗan-Isuhu ƙani ne ga Ado Aleiro kuma sun daɗe suna takun-saƙa da rikice-rikice a tsakaninsu da wasu ɓangarorin.
Ɗan-Isuhu ya fi yin fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
Yana cikin manyan ƴanbindiga da ke kai miyagun hare-hare musamman a tsakanin ƙananan hukumomin Tsafe da Gusau a jihar Zamfara. Sannan galibin yankunan kudancin Katsina irin su ƙananan hukumomin Faskari da Funtua da Malumfashi da Bakori da wani yanki na Danja duk shi ne yake da iko da su. Duk hare-haren da ake yi a yankunan, ko dai shi ya kitsa su, ko shi ya kai da kansa tare da yaransa."
Damuna
A watan Maris na shekarar 2024 ne jami'an tsaron Najeriya suka sanar da samun nasara kashe ɗanbiniga, Damuna.
Damuna ya yi fice wajen garkuwa da mutane domin kuɗin fansa a yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya.
An tabbatar da kashe shi ne bayan shekara da aka fara kuskuren sanar da kashe shi a rikici tsakaninsa da ɗanbindiga gawurtacce Dogo Giɗe.
Ya mutu a sanadiyar raunukan da ya ji a sanadiyar harbinsa da jami'an tsaron ƙasar suka yi bayan sun yi musayar wuta a Zamfara.