Afirka ta Kudu ta kafa kwamitin bincike kan gurfanar da masu laifin wariyar launin fata

Mulkin wariya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu waɗanda aka zarga da kisan wasu mutane a lokacin mulkin wariya
  • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da kafa kwamitin binciken shari'a kan zargin katsalandan na siyasa a gurfanar da waɗanda suka aikata laifukan wariya.

Sanarwar ta zo ne shekaru talatin bayan kawo ƙarshen mulkin tsiraru fararen fata — da kuma bayan wasu waɗanda suka tsira da dangi na wadanda abin ya shafa suka maka gwamnatin Ramaphosa a kotu saboda rashin ganin an samu adalci.

Hukumar Gaskiya da Sasanci ta TRC, wadda aka kafa a 1996, ta bankaɗo muggan laifukan da aka aikata a lokacin wariyar kamar kisa da azabtarwa, amma kaɗan daga cikin waɗannan shari'o'i ne suka ci gaba zuwa kotu.

A yayin da yake sanar da kafa wannan sabon kwamitin, wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta ce Ramaphosa ya "ƙuduri aniyar tabbatar da cewa an gano haƙiƙanin gaskiya kuma an kai karshen wannan lamari."

Binciken da za a gudanar sakamakon tattaunawar sulhu ne a wata ƙara da aka shigar a kotun ƙoli da wasu iyalai da waɗanda suka tsira daga mulkin wariyar launin fata suka shigar.

Wannan gungun mutane 25 na neman diyya da ta kai dala miliyan tara, suna zargin cewa ba a taba bincikar laifukan da aka aikata a lokacin wariyar yadda ya kamata ba tun bayan rushe tsarin.

Masu shigar da karar sun hada da ɗan Fort Calata, daya daga cikin fitattun 'yan gwagwarmaya da aka fi sani da Cradock Four, wanda jami'an tsaro suka kona har lahira a shekarar 1985.

Kisan gilla da aka yi wa waɗannan mutane hudu ya tayar da hankula a faɗin kasar, inda wasu jami'an 'yan sanda shida daga bisani suka amsa aikata laifin a gaban Hukumar Gaskiya da Sasanci (TRC). An hana su afuwa daga laifin, amma ba a taba gurfanar da su a kotu ba. Dukkan su shida sun mutu daga baya.

Shekaru da dama kenan masu suka na zargin cewa jagorancin jam'iyyar African National Congress (ANC) bayan aikata laifin wariyar launin fata sun ƙulla wata yarjejeniya da tsohuwar gwamnatin fararen fata domin hana gurfanar da masu laifi. Sai dai ANC ta musanta hakan.

A ranar Laraba, fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa "zarge-zargen shisshigi mara kyau da ya jinkirta ko ya hana gudanar da bincike da gurfanar da wadanda suka aikata laifukan wariar fata sun daɗe suna gudana tun daga gwamnatocin baya."

Za a sanar da shugaban kwamitin binciken da kuma jadawalin aikin a nan gaba kadan.