window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/05/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammmed

  1. Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe jami'anta biyu a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe wasu jami'anta guda biyu bayan wasu hare-haren da aka kai a gidansu da ke yankin Khan Younis a Gaza a ranar Asabar.

    Ɗaya daga cikin jami'an nata mai aikin gadi ne a wani asibitin wucin-gadi na ƙuniyar, ɗayan kuma jami'in lalata makamai ne.

    Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce aƙalla Falasɗinawa 20 ne aka kashe a sababbin hare-haren Isra'ila a yankin.

    Sun ce daga cikinsu akwai wani ɗanjarida.

  2. Uganda ta yanke alaƙar soji da Jamus

    Gwamnatin Uganda ta sanar da yanke duk wata alaƙar soji da ƙasar Jamsu bayan rahoton zargin ambasadan Jamus da aikata wasu laifuka da ba a bayyana ba a ƙasar ta gabashin Afirka.

    Kakakin rundunar sojin ƙasa na ƙasar, Kanal Chris Magezi ne ya sanar da haka, duk da bai bayar da cikakken bayani kan dalilinsu na ɗaukar wannan mataki ba, amma ya ce matakin zai cigaba da amfani har zuwa lokacin da ƙasashen biyu za su samu maslaha.

    Mathias Schauer ne ambasadan Jamus a Uganda tun daga shekarar 2020 zuwa yanzu.

    Har yanzu dai ofishin jakadancin Jamus da ke Uganda ba ta ce komai ba.

  3. An gano gawarwakin masu wasan zamiya biyar a wani tsauni a Switzerland

    Rundunar ƴansandar ƙasar Switzerland ta ce jami'anta sun gano gawarwakin masu wasan zamni a wani tsauni da ke yankin Zermatt.

    An ƙaddamar da bincike ne a ranar Asabar bayan an lura da wasu kayayyakin masu wasan zamiya a tafiya mai nisan kimanin kilomita dubu huɗu.

    Helikwafta ce ta kai masu aikin ceton, inda suka samu nasarar ciro gawarwakin guda huɗu.

    Tuni hukumomi a ƙasar suka ƙaddamar da bincike kan gano bayanan mamatan, tare da binciken musabbabin rasuwar tasu a tsaunin.

  4. Yadda amon wuta daga rana ke barazanar haifar da katsewar lantarki a duniya?

    Rana

    Asalin hoton, NASA/SDO

    Rana takan shiga wani yanayi na yawaitar tunzuri inda takan yi amon wuta, wanda a bana ya kai ƙololuwa, kamar yada hotunan da hukumar NASA ta fitar suka nuna.

    A cikin wannan mawuyacin yanayi, iska kan ɗauki tururin zuwa duniyar bil'adama.

    Kuma irin wannan yanayi ya kan shafi fannonin fasa da ƙere-ƙere da ke nan doron duniya, har ma yana haddasa katsewar lantarki, amma baya da illa kai tsaye ga lafiyar ɗan'adam.

  5. Wike ya fice daga dukkan yarjeniyoyin sulhu da aka shiga a PDP

    Wike

    Asalin hoton, BBC Hausa

    Ministan Abuja, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce zai fice daga dukkan yarjeniyoyin sulhu da aka shiga a baya domin sulhunta ɓangarorin da suke da saɓani a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

    Haka Wike ya ce zai cigaba da gwargwarmaya, har sai "an tabbatar da adalci."

    Sai dai kuma a wannan karon, Wike ya bayyana gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda tsohon na hannun damansa ne a matsayin wanda yake rura wutar rikicin a yanzu, "saboda ƙin ɗabbaƙa wasu matakai da aka ɗauka na sulhu."

    Wike ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi mai taken, "Rikice-rikicen PDP: Matsayata."

    A cikin sanarwar ya ce daga cikin matsayar da aka ɗauka, akwai tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin babban sakataren PDP kamar yadda Kotun Ƙoli ta tabbatar, sannan mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a na ƙasa zai janye ƙarar da ya shigar kan dokar ta-ɓaci na Rivers.

    "Amma abin mamaki shi ne yadda Seyi Makinde ya haɗa baki da Gwamna Peter Mba na Enugu, inda suka yi wani taro, suka ce matuƙar ba a bar Ude Okoye a matsayin sakatare ba, za su fice daga PDP. Sannan Makinde ya sake haɗa wani taron, inda suka ƙulla cewa mataimakin babban sakataren ya zama sakataren riƙo, wanda shi ma ya saɓa da yarjejeniyar da aka ƙulla tun da farko."

    Wike ya ce abin ban haushin ma shi ne yawancin gwamnonin da suke jawo matsalolin, "na taimaka wajen samun nasararsu a zaɓe, amma ban taɓa buƙatar komai daga wajensu ba, kuma ba zan taɓa yi ba. Don haka na fice daga dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla a baya."

  6. An kama basarake bisa zarginsa da taimakon ƴanbindiga a Neja

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an tsaron haɗin sun kama wani mai unguwa a ƙauyen Guiwa da ke ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja mai suna Garba Mohammed bisa zarginsa da taimakon ƴandiga da suke addabar yankin, da ma wasu sannan jihar, wadda ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

    An kama basaraken ne tare da wasu mutum 13 a ranar Juma'a bayan samun bayanan sirri kan harkokinsu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen, inda ya ce jami'an tsaron sun samu nasara ne bayan sun kai wani farmaki domin fatattakar ƴanbindiga a maɓoyarsu.

    Ya ce an kama Garba Mohammed ne bisa zarginsa da mayar da gidansa maɓoyar ƴanbindiga, inda suke taruwa domin shirya ta'asarsu.

  7. Koguna na ƙafewa sakamakon fari a Iraqi

    Iraqi

    Asalin hoton, Reuters

    Wani jami'in gwamnati a Iraqi ya ce ƙasar na fuskantar matsalar ruwan sha, abin da ya janyo wuraren adana ruwa suka ragu matuka - bayan fari da ya afka wa ƙasar.

    Mai magana da yawun ma'aikatar samar da ruwan sha a ƙasar, ya ce ba a ga raguwar ruwa ba irin na yanzu tsawon shekara 80.

    Ƙasar dai na fama da fari, ga kuma ƙarancin ruwan sama - inda koguna biyu da ta dogara da su na Tigris da Euphrates ke ci gaba da kafewa.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Iraqi na ɗaya daga cikin ƙasashe biyar da suka fi fama da matsalar sauyin yanayi a duniya.

  8. Yadda na rikiɗe daga Baturiya zuwa Bahaushiya

    Bayanan bidiyo, Yadda na rikiɗe daga Baturiya zuwa Bahaushiya

    Sina Warncke wadda sunanta na Hausa shi ne Zinariya, ƴar ƙasar Jamus ce da ta sa kai wajen ƙwarewa a harshen Hausa, kuma ta bayyana mana al'adun Hausawa ta fi so da kuma yadda rayuwa cikin ƴan ƙabilar a Najeriya ke kasance mata.

  9. Tsohon mijina ya sake ni bayan ƙwace min kwangilar biliyoyin naira - Mansurah Isah

    Mansurah Isah

    Asalin hoton, Mansurah Isah/Facebook

    Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu, wanda ta bayyana cewa ya zo mata a wani yanayi na ba-zata, kamar almara.

    Mansurah ta ce ita aure ta yi na soyayya, domin a cewarta, "so makaho ne", amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba.

    Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda BBC ta tattauna da ita tare da tsohuwar jaruma a masana'antar, Fati Mohammad kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure.

    Da take shimfiɗa, Fati Mohammad ta ce mutane ne suke musu gurguwar fahimta, domin "shi aure ai yana da rai, kuma idan Allah ya kawo ƙarshensa, dole sai ya ƙare. Mutane da yawa aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, sai ba za a ji ba," in ji ta.

  10. 'Shirun da Amurka ta yi yana ƙarfafa wa Rasha ci gaba da kai hari kan Ukraine'

    Zelensky

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Zelensky ya ce shirun da Amurka da kuma sauran duniya suka yi, yana ƙara ƙarfafa wa Vladimir Putin ci gaba da kai wa Ukraine hari.

    Zelensky na jawabi ne bayan mummunan harin sama da Rasha ta kai ƙasar, inda aka harba kusan makaman linzami 400 da na jirage marasa matuki a Ukraine ɗin.

    Harin ya janyo mutuwar aƙalla dubban fararen-hula.

    Mista Zelensky ya ce Rasha ba za ta daina zub da jinin ƴan ƙasarsa ba har sai an matsa wa Moscow lamba.

    Jami'ar harkokin wajen Tarayyar Turai, Kaja Kallas, ta ce hare-hare da Rasha ta kai cikin dare ya nuna cewa tana son ruguza ɗaukacin Ukraine ne.

    Ta kuma yi kiran cewa a matsa wa Moscow lamba yadda ya kamata domin ta daina kai hare-hare.

  11. Ƴan Najeriya 120,000 ne suka kwarara zuwa Birtaniya a 2024 - Rahoto

    UK

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoto da ofishin kula da ƙididdiga na Birtaniya ya fitar, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu mafi yawan mutanen da suka yi tururuwa zuwa Birtaniyan a shekara ta 2024.

    Alƙaluman rahoton sun nuna cewa ƴan Najeriya 120,000 ne suka kwarara zuwa Birtaniya a 2024.

    Lamarin na nuna cewa ƙasar tana biye da Indiya da ke matsayi na farko a jerin, inda mutanen ta 240,000 suka shiga Birtaniyar.

    Rahoton ya ce batun neman aikin yi yana cikin abubuwan da ke sa ƴan Najeriya tururuwar zuwa Birtaniya.

    Dakta Ishaku Shitu Al-Mustapha, wani babban malami a jami'ar Canterbury Christ da ke birnin Landan, ya shaida wa BBC cewa neman kyautatuwar rayuwa na cikin abin da ya sa ƴan Najeriya ke ƙaura zuwa Birtaniyar.

    "Wasu ƴan Najeriya sun gaji da ƙasar, ga rashin shugabanci na gari da kuma rashin albashi mai kyau su ma suna cikin abin da ya ƴan ƙasar ke ficewa daga cikinta," in ji Dakta Al-Mustapha.

    Ya ce samun shugabanni masu kishin ƙasa da kuma tsoron Allah zai sa ƴan Najeriya su rage fita zuwa ƙasashen waje.

  12. Ambaliya ta lalata tituna da faɗuwar bishiyoyi a birnin Delhi

    Delhi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ruwan sama mai karfin gaske tafe da iska ya haifar da ambaliyar ruwa a birnin Delhi da ke arewacin Indiya, lamarin da ya lalata tituna da faɗuwar bishiyoyi.

    Wannan yanayi da ake ciki ya kuma haifar da matsalar tashi da saukan jiragen sama a babban filin jirgi da ke birnin.

    Tun da farko, hukumar yanayi ta Indiya ta gargaɗi mazauna birnin cewa za a iya fuskantar yanayi mara kyau da ba su shawarar zama a gida.

    Jihohi Punjab da Haryana da Uttarakhand duk sun fuskanci irin wannan ruwa.

  13. Sojoji sun ce sun kashe ƴan bindiga 21 a jihar Katsina

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka wasu ƴan bindiga 21 a dajin Shawu a karamar hukumar Faskari na jihar Katsina.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma ne suka samu nasarar kashe ƴan bindigar bayan kai musu hari a maɓoyarsu ranar 23 ga watan Mayu, a ci gaba da yaƙi ayyukan ɓata-garin.

    Sanarwar ta ce an samu nasarar kashe ƴan bindigar ne bayan artabu na tsawon lokaci, ciki har da waɗanda kogi ya tafi da su lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.

    Sai dai sanarwar ba ta bayar da rahoton mutuwar wani jami'in soji ba a artabun da aka yi.

    Ta kuma ce an ƙwato mamakai da harsasai da dama - ciki har da babura 40 da shanu da dama waɗanda ƴan bindigar suka sace.

    Har ila yau, sojojin sun ce samamen da suka kai ya sa ƴan bindigar tserewa tare da barin sansaninsu, inda suka fantsama cikin dazuka.

  14. Real Madrid ta sanar da ɗaukar Alonso a matsayin sabon kocinta

    Xabi Alonso

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta sanar da ɗaukar Xabi Alonso a matsayin sabon kocinta.

    Alonso wanda ya buga wa Real ɗin wasa 236 a matsayin ɗan wasanta a baya, ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku.

    A farkon watan nan ne ya sanar da cewa zai bar Bayer Leverkusen da yake jagoranta.

    Tsohon ɗan wasan na Liverpool da kuma Sifaniya, ya jagoranci ƙungiyar lashe kofin Bundesliga a bara ba tare da an doke shi ko da wasa ɗaya ba - da kuma German Cup.

    Alonso wanda yarjejeniyarsa za ta kai har 30 ga watan Yunin 2028, zai maye gurbin Carlo Ancelotti.

    Ancelotti ya jagoranci wasansa na karshe a Madrid a ranar Asabar, inda a yanzu zai zama sabon kocin ƙasar Brazil.

    Za a gabatar da Alonso wanda ya lashe Champions League a 2014 lokacin da yake buga wa Madrid kwallo - a gobe Litinin a filin atisayen ƙungiyar.

  15. Sifaniya za ta karɓi bakuncin ministocin ƙasashen Larabawa ranar Lahadi

    Spain

    Asalin hoton, Reuters

    A yau Lahadi Sifaniya za ta karɓi bakuncin ministocin ƙasashen Larabawa da Turai a wani taron samar da zaman lafiya a Gaza da mafitar kafuwar ƙasashe biyu masu cikakken iko a Gabas Ta Tsakiya.

    Ƙasashen da za su halarci taron sun haɗa da Saudiyya da Masar da kuma Turkiyya.

    Wakilin BBC ya ce gwamnatin Sifaniya, da ke yawan sukar Isra'ila, ta ce wannan taro an shirya shi ne da manufar kawo karshen zub da jini da yanayin jin-kai mai muni da ake ciki a Gaza.

    Sannan taron na fatan ganin ya samar da hanyar tsagaita wuta da buɗe kofar kai isasshen agaji da kuma cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Hamas damar sakin ƴan Isra'ila da suka rage a hannunta.

  16. 'Hare-hare ta sama da Isra'ila ke kai wa sun fi razana ni'

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Wata ƴar Isra'ila da aka yi garkuwa da ita a Gaza ta ba da labarin abin da ya rinka tsorata ta, a lokacin da take hannun Hamas, tana mai shaida cewa hare-haren sama da Isra'ila ke yi sun fi razanata.

    Naama Levy, ta faɗa wa ƴan jarida a birnin Tel Aviv a taron dandazon mutanen da ke kiran a dawo da sauran ƴan ƙasar da ake garkuwa da su cewa, tana fargabar rayukan sauran mutanen.

    Ta ce a duk lokacin da ta ji karar bam tana sake tabbatarwa kanta cewa babu tantama karshenta ya zo.

    Yayin da Isra'ila ke ci gaba da hare-hare babu ƙaƙƙautawa a Gaza, sojojin ƙasar sun ce suna nazarin rahotonni da ke cewa harin nasu ya kashe yara tara ƴan gida ɗaya.

  17. Za a kammala gasar Premier yau Lahadi

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Lahadi za a kammala Premier League, wadda za a yi karawa 10 a kuma lokaci ɗaya, kenan fafatawar mako na 38.

    An fara gasar ranar 16 ga watan Agustan 2024, kuma kawo yanzu an buga karawa 370 da cin ƙwallo 1,091, inda ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah shi ne kan gaba a cin ƙwallaye mai 28 a raga.

    Tuni Liverpool ta lashe kofin bana na 20 jimilla, irin yawan na Manchester United.

    An kuma samu ukun da suka yi ban kwana da Premier da ya haɗa da Leicester City da Ipswich Town da Southampton.

    Yanzu abin da ya rage shi ne waɗanda za su wakilci Ingila a Champions League da Europa da Conference League.

    Liverpool da Arsenal sun samu gurbin Champions League har da Tottenham, wadda ta lashe Europa League.

    Yanzu saura gurbi uku ake nema a teburin Premier da za su je babbar gasar zakarun Turai.

  18. Harin Boko Haram ya tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa a Borno

    Mayaƙan BH

    Asalin hoton, Boko Haram

    Ɗaruruwan farar-hula ne ke tserewa muhallansu a wasu garuruwan jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon harin da masu iƙirarin jihadi suka kai wani sansanin sojin ƙasar.

    Mayakan Boko Haram sun tilasta wa sojoji ficewa daga sansanin bayan kai musu hari a karamar hukumar Marte, tare da hallaka sojoji huɗu da ƙwace makamai kafin daga bisani su ƙona sansanin.

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce a baya-bayan nan mayaƙan na Boko Haram sun ɗaiɗiata ɗaruruwan ƙauyuka da munanan hare-hare.

    Sai dai duk da hakan hukumomi na cewa mutanen su koma muhallansu, duk da fargabar da ƙungiyoyin agaji suka yi kan cewa babu isasshen tsaron soji a wuraren.

  19. Rasha ta hallaka mutum 12 a wani sabon hari a Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla mutum 12 ne aka kashe sannan gommai suka jikkata a wasu jerin hare-haren jirage marasa matuka da kuma na makaman linzami da Rasha ta kai Ukraine cikin dare, a cewar jami’an ba da agaji.

    An kashe wasu yara uku a birnin Zhytomyr a yammacin Kyiv, an kuma kashe wani dattijo mai shekara 70 a birnin Mykolaiv, in ji jami’an agajin gaggawa.

    Harin na zuwa kwana guda bayan da babban birnin Ukraine, Kyiv ya fuskanci hare-hare masu muni wanda ba a gani ba tun soma mamayar Rasha.

    Harin na ranar Asabar wanda ya hallaka mutum 13 a faɗin Ukraine, ya zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawar diflomasiyya don ganin an kawo karshen yaƙin, ciki har da musayar fursunoni – sai dai Rasha ta bijirewa kiran tsagaita wuta.

  20. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Lahadi.

    Fatan kuna hutun karshen mako lafiya.

    Kamar kullum yau ma ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai kasance da ku a wannan safiya!