Batun goyon bayan tazarcen Tinubu zalamar mulki ce - PRP

Asalin hoton, prp.com.ng
Daya daga cikin jam'iyyun adawa a Najeriya wato PRP, ta yi alawadai da amincewar da kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyyar APC mai mulki, da gwamnonin jam'iyyar, da 'yan majalisar dokoki na kasa na jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki suka yi wa shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, domin ya sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara ta 2027.
Jam'iyyar PRP ta bayyana fargabar, cewa wannan mataki wata zalamar mulki ce kawai, wadda ta fayyace aniyar jam'iyyar APC ta neman ci gaba da mulki karfi da yaji ta hanyar wani goyon baya na musamman da aka tsara, maimakon a bari jama'ar kasa su bayyana ra'ayinsu game da takarar shugaban kasar a zaben da ke tafe.
Kwamred Muhammed Ishak, shi ne sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PRP, ya shaida wa BBC cewa sanin kowa ne ba wani dadin salon mulkin jam'iyyar APC ake jiba a Najeriya saboda irin wahalhalu da tsadar rayuwa da rashin tsaro ga tabarbarewar tattalin arziki ga kuma uwa uba cin hanci da rashawa da ya yi katutu a kasar.
Ya ce," To bisa la'akari da wannan hali da ake ciki ace wai har jam'iyyar APC mai mulki ace ta fara taro har ma tana tabbatar da takarar shugaban kasa Tinubu wannan ai wasan kwaikwayo ne ma."
Kwamred Muhammed Ishak, ya ce," Duk da shugaban kasar yana da 'yancin neman wa'adin mulki karo na biyu, 'yan kasa musamman talakawa wanda su ne suka fi yawa a kasarnan, sune idan suka ji dadi za su bashi damar ya sake tsayawa takara ba wai wasu tsiraru da ake damawa da su a gwamnati bane za su taru su ce wai sun bashi damar sake tsayawa takara, talakawa suke da iko don sune masu zabe."
" Abin takaicin ma shi ne duba da halin da kasa ke ciki, ace wai su 'yan jam'iyyar APC batun sake tsayawar Tinubu shi ke gabansu tun yanzu wanda shekara ta biyu ma za a shiga a mulkin, ai abin da ya kamata su'yan jam'iyyar ta APC za su mayar da hankali a yanzu shi ne yadda za a magance matsalar tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma inganta jin dadi da walwalar 'yan kasa, amma ba wai a fara maganar takara ba tun yanzu."In ji shi.
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PRP, ya ce," Shi shugabanci ba wai labari bane, abin da ake nema a cikinsa sakamako mai kyau, duk wani da ake gani ana zaba a ko ina a duniya ana zabarsa ne domin yazo ya magance wata matsala da ake ganin shi ne zai iya magance ta, to amma a shugabanci irin na yanzu a Najeriya abin ba haka bane."
Ya ce,"Ya kamata su 'yan jam'iyyar ya APC su sani cewa taron da suka yi suka ce suna goyon bayan shugaba Tinubu ya sake tsayawa takaraba shi zai hana idan an zo zaben 2027 a kayar da shi da ma jam'iyyar tasu."
Kwamred Muhammed Ishak, y ace" Ba wai karfin 'yan adawa ne zai kayar da shugaban kasa ba kawai, karfin talakawa wanda sune za su fito su zabi zabinsu wanda suke ganin zai musu abin da suke so."
A baya bayannan dai tururuwa zuwa APC da 'yan'adawar ke yi na ƙara jefa manyan jam'iyyun da ke da ƙarfin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda tuni PDP da Labour da NNPP suke auka cikin rikicin shugabanci.
'Yansiyasar da ke sauya sheƙar kan bayyana dalilai daban-daban na komawa wata jam'iyya, amma masana sun sha bayyana cewa rashin alƙibla da kuma niyyar bauta wa masu zaɓe ne ke jawo sauye-sauyen jam'iyya a siyasar Najeriya.
A kodayaushe APC na farin ciki da bugun ƙirjin cewa ayyukan da take yi masu kyau ne ke ci gaba da janyo yan'adawa cikinta