Mohammed Sinwar: Wane ne shugaban Hamas a Gaza da Isra'ila ke iƙirarin kashewa?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Yahya Kanakrieh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Aiko rahoto daga Reporting from Jordan
Firaminstan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya bayar da sanarwar a ranar Laraba cewa sojojin ƙasarsa sun kashe shugaban Hamas Mohammed Sinwar, ɗaya daga cikin mutanen da Isra'ila ke nema ruwa a jallo, kuma ɗan'uwa ga shugaban ƙungiyar Yahya Sinwar.
Sai dai har yanzu ƙungiyar ta Hamas ba ta tabbatar ko musanta iƙirarin ba.
Wane ne Mohammed Sinwar?
Mutane da dama sun yi amanna cewa Mohammed Sinwar na daga cikin manyan masu zartaswa a Gaza tun lokacin da aka kashe Yahya Sinwar, wanda shi ne tsohon shugaban ƙungiyar Hamas da ake zargin ya tsara yadda aka kai hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da suka haddasa yaƙin Isra'ila da Gaza. Daga bisani sojojin Isra'ilar suka kashe shi a watan na Oktoba.
Baya ga Yahya, Isra'ila ta kuma kashe Mohammed Deif, wanda shi ne kwamandan dakarun ƙundumbalar na Izzedine al-Qassam Brigades.
Wannan ya faru bayan fiye da watanni 19 da soma yaƙin, da kuma tattaunawar da ake ci gaba da yi game da musayar fursunonin yaƙi da waɗanda ɓangarorin biyu ke garkuwa da su.
Ana ganin Mohammed Sinwar a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin sojojin Izzedine al-Qassam Brigades, kuma yana da ƙarfin faɗa a ji a yankin na Gaza.
A baya ya taɓa riƙe shugabancin ƙungiyar tare da ɗa'uwansa Yahya, abin da ya ƙara fito da sunansa har ma ake hasashen shi ne ya fi dacewa ya gaje shi.
An kwashe shekaru Isra'ila na neman hallaka shi, inda ta gwada hakan aƙalla har sau biyar sai dai ba ta yi nasara ba. An kuma alaƙanta shi da da hannu a garkuwa da Gilad Shalit, wani sojan Isra'ila da kuma taka rawa wajen haddasa yaƙin da ake ci gaba da gwabazawa a Gaza.
Babu dai wani cikakken bayani game da asalin Muhammed Sinwar cewa ya fito ne daga ƙabilar Larabawa kuma kuma Falasɗinawa.
Wannan kuwa bai rasa nasaba da matsayinsa na soji da kuma al'adarsa ta rashin yawan fitowa akai-akai, kamar yadda wani ɗan jarida Bafalasɗine ya shaidawa BBC.
Ga abin da muka sani game da shi.
Ɗan'uwa ne ga Yahya Sinwar

Asalin hoton, Anadolu via Getty
An haifi Mohamed Sinwar a 1975 a binrinin Khan Younis. A lokacin yayansa Yhaya Sinwar na da shekara sha uku. Rikici ya sa iyayensu sun baro ƙauyensu da ke kusa da Ashkelon a shekarar 1948 inda suka koma da zama a kudancin birnin Gaza.
A shekarar 1991, an ɗaure Mohammed Sinwar a gidan yarin Isra'ila na Ketziot har tsawon wata tara saboda zargin sa da "ayukan ta'addaci".
A cewar jaridar the Jerusalem Post, Mohammed ya ƙara samun ƙwarin gwiwa da zimma tun daga lokacin da Hamas ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila a shekarar 2000 zuwa yanzu. Kamar dai ɗan'uwansa Yahya, shi ma Mohammed Sinwar ya yi suna a lokaci da shi Yahya ke zaman jarun a kurkukun Isra'ila.
Ya samu alaƙa da manyan kwamandojin Hamas da suka yi aiki a tare, cikin su har da Mohammed Deif, Saad al-Arabid, da wasu jagorori da suka bunƙasa ƙungiyar ta Hamas, in ji jaridar.
Jami'an gwamnatin Isra'ila sun ce Mohammed Sinwar na cikin waɗanda ake zargi da yin garkuwa da sojan nan Bayahude Gilad Shalit a 2006, abin da ya yi sanadiyyar aka saki ɗan'uwansa Yahya, bisa yarjejeniyar musayar fursunoni Falasɗinawa1,027.
Mohammed Sinwar ya shafe gomman shekaru yana faman ɓuya domin kaucewa sojojin Isra'ila daga kama shi ko kashe shi.
Ana bayyana shi da 'Inuwa'
Ya daɗe a haka, har ma hakan ya sa aka yi masa laƙabi da "Inuwa". Daga lokacin ya ci gaba da samun gogewa har hakan ya ba shi damar fito da tsare-tsare da dama a rundunar mayaƙan Hamas
Da yawa ba su san Mohammed Sinwar ba sai lokacin da sojojin Isra'ila suka fitar da wa i bidiyonsa a 2023 yana tuƙa mota a hanyar ƙarƙashin ƙasa da Hamas ta gina a Gaza.
Ya fi Yahya zama maras tausayi'
Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa wata majiyar rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana Mohammed Sinwar ya fi ɗa'uwansa zama "maras tausayi".
"Ba za a taɓa samun wani babban abu da sojojin Hamas suka tsara fiye da shekaru 25 ba tare da hannun Mohammed Sinwar ba. Ya zama kwamanda Khan Younis, muƙami mafi girma, inda ko da kwamandan da ya gaje shi yana biyayya ga manufofinsa
Tattaunawar sulhu kan fursunoni da waɗanda aka yi garkuwa da su
Kafafen yaɗa labaran ƙasashen Larabawa da Isra'ila sun sha yin rahotanni tattaunawar baya-bayan nan game da tsagaita wuta a Gaza "ba ta ruguje gaba ɗaya ba" amma shi kansa Mohammed Sinwar "da ke cikin tattaunawar ya fi nuna tsauri fiye da ɗan'uwansa marigayi Yahya.
Sun kuma ruwaito cewa Mohammed na cikin masu tattaunawa da Isra'ila domin sakin fursunoni Falasɗinawa da dakarun Isra'ila da ake garkuw da su," kuma ya taka gagarumar rawa wajen gina hanyar ƙarƙashin ƙasa a Gaza.
Sake farfaɗo da Hamas

Asalin hoton, EPA
Jaridar Wall Street Journal, ta ruwaito cewa Mohammed na sake farfaɗo da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta hanyar ɗaukar sabbin mayaƙa a yankin Zirin Gaza, abin da ya ƙara zafafa rikicin da ya sa Isra'ila ke kai hare-haren".
Jaridar ta bayyana cewa "kisan Yahya Sinwar ya karya lagon ƙungiyar Hamas, amma yaƙin da ake yi a Zirin na Gaza ya nuna Hamas ta sake samun sabbin mayaƙa da ke da karkashi a yaƙin kuma waɗanda ake ganin sake farfaɗowar ƙungiyar na iya tsawaita rikin na Zirin Gaza."
Jaridar ta ruwaito sojan Isra'ila Mnjo Janar Amir Afifi na cewa, "yekuwar ɗaukar sabbin mayaƙa da ci gaba da gudanar da yaƙin a ƙarƙashin jagoranci Mohammed Sinwar na zama wasu sabbbin ƙalubalai ga Isra'ila," inda ya ce "yadda Hamas ke bunƙasa cikin sauri ya fi yadda dakarun sojin Isra'ila ke murƙushe ta "
Afifi ya kuma ce Mohammed Sinwar ne "ke tafiyar da kome" kuma shi ne "gimshiƙin farfaɗowar Hamas". Ya ce bayan mutuwar Yahya Sinwar, membobin ƙungiyar da ke zaune a ƙasashen waje sun "samar da wani tsarin shugabanci na haɗaka a maimakon zaɓen sabon shugaba, amma kuma mayaƙan Hamas a Gaza ba su bayar da goyon baya inda suke tafiyar da ƙungiyar da kansu a ƙarƙashin shugabancin Mohammed Sinwar".