window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Fiye da motocin agaji 100 ne suka shiga a jiya - Isra'ila

    Mota ɗauke da agaji

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar sojin Isra'ila da ke kula da shigar da kayan agaji zuwa Gaza ta ce manyan motocin agaji 107 ne ɗauke da kayan agaji suka shiga Gaza a ranar Alhamis ƙarƙashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na duniya.

    To sai dai har yanzu Majalisar Dinkin Duniya ba ta tabbatar da ko kayan sun kai ga mutanen Gaza ba.

    Sojojin Isra'ila sun ce za su ci gaba da shigar da kayan agajin cikin sanya idanu.

    "Za mu ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Gaza, yayin da za mu riƙa tabbatar da cewa kayan ba su faɗa hannun Hamas ba," in ji masu kula da shigar da kayan.

    Isra'ila na zargin Hamas da sace kayan agajin, to amma ƙungiyar ta musanta hakan.

  2. INEC za ta fara amfani da fasahar AI a harkokin zaɓen Najeriya

    Masu zaɓe

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC a bayyana aniyarta na fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen gudanar da ayyukan zaɓe a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun babban kwamishinta kuma shugaban kwamitin wayar da kai da yaɗa labarai, Sam Olumekun, ta ce hukumar fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa hukumar ɗaukar matakai la'akari da bayanan da za ta samu ta hanyar fasahar.

    ''Haka kuma fasahar za ta ƙara ƙarfafa sahihancin zaɓuka ta hanyar tattara alƙaluma da kuma tantance aihinin alƙaluman zaɓe'', a cewar sanarar.

    Tuni dai hukumar ta sanar da kafa sashen fasahar ƙirƙirarriyar basirar ta AI a ƙarƙashin ɓangaren sadarwar hukumar, domin fara inganta ayyukan fasaha na hukumar, tare da kawar da matsalolin da ake fuskanta da suka shafi fasahar sadarwa.

    Hukumar ta ce a baya-bayan nan ta halarci tarukan duniya waɗanda ta ce an shirya kan tasirin fasahar AI kan zaɓukan ƙasashe.

  3. Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha kan zargin ƙage

    Sanata Natasha

    Asalin hoton, Natasha

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, saboda zargin ɓata suna da ta yi a gidan talabijin kai-tsaye.

    Gwamnatin na zargin dakatacciyar ƴarmajalisar, da ''yin ƙage, duka kuwa da ta san cewa hakan zai shafi ƙimar mutum'', tana mai kafa hujja da cewa yin hakan laifi ne da ke ɗauke da hukunci ƙarƙarshin sashe na 392 na kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Daga cikin jerin mutanen da gwamnatin da sanya a matsayin shaidun da za su tabbatar d zargin, har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

    Ɗaya ɗaga cikin tuhume-tuhumen da gamnatin ke yi wa Sanata Natasha shi ne inda ta zargi Godswill Akpabio da Yahaya Bello da yunƙurin kitsa kasheta.

    A farkon watan Maris ne da Majalisar Dattawan Najeriyar ta dakatar da sanatar har na tsawon wata shida bisa shawarwarin da kwamitin Ɗa'a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama'a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da Sanata Natasha ta miƙa wa majalisar.

  4. Hatsarin ababen hawa ya kashe mutum 1,593 a Najeriya cikin wata uku

    Hadurra

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya, (FRSC) ta ce kimanin mutum 1,593 ne suka mutu sakamakon haɗurra a cikin wata ukun farko na shekarar 2025.

    Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna samun ƙaruwar munanan haɗurran da suka haddasa rasa rayuka da raunuka.

    Hukumar ta bayar da rahoton cewa an samu haɗurra 2,650 a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris.

    To sai dai bisa ga alƙaluman an samu raguwar yawan haɗuran idan aka kwatanta da daidai wannan loacin a 2024.

    Haɗurran ababen hawa na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da asarar rayuka a Najeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma tuƙin ganganci daga ɓangaren direbobi.

  5. Amurka ta ƙaƙaba wa Sudan takunkumai saboda yaƙi

    Jagororin yaƙin Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da ƙaƙaba wa Sudan sabbin takunkumai, sakamakon zargin amfani da makami mai guba da sojojin gwamnatin ƙasar suka yi a yaƙin basasar da ke ci gaba da ƙazanta.

    Washington ta ce an yi amfani da irin waɗannan makaman ne a bara, yayin da sojojin Sudan ke tsananta hare-haren da suke kai wa yankunan da ke hannun dakarun rundunar RSF.

    Ana zargin ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi a rikicin - wanda ya barke a farkon shekarar 2023, lamarin da ya janyo abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin rikicin jin kai mafi muni a duniya.

    Kazalika takunkumin ya shafi manyan jagororin ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna, Shugaban Sojojin Ƙasar Abdel Fattah al-Burhan da abokin hamayyarsa, shugaban RSF Mohamed Hamdan Daglo, wato Hemdti.

  6. Assalamu alaikum

    Jama'a masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye muna yi muku lale maraba da wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafi domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada mu manta da tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.