window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Rufewa

    Masu bibiyar shafin kai-tsaye na BBC Hausa, nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya na yau Juma'atu babbar rana.

    Dafatan za a yi hutun ƙarshen mako lafiya.

    Mu kwana lafiya.

  2. Musulman Rohingya fiye da 400 sun mutu cikin teku a watan Mayu- MDD

    Musulman Rohinhgya

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya ta ce Musulman Rohingya 427 ne suka mutu a lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka wani teku mai cike da haɗari a cikin wannan watan.

    Hukumar ta UNHCR ta ce yanayin jinƙai mai muni da ake ciki a Myanmar da Bangladesh ne ya tilastawa alummar marasa rinjaye da ke fuskantar zalunci ficewa domin neman mafaka a wasu wuraren.

    MDD ta ce wani jirgin ruwa ɗauke da mutane 267 da suka baro sansanin ƴan gudun hijira a Bangladesh ya nutse a farkon watan Mayu, da yayi sanadiyyar mutuwar da dama, sai mutane 66 ne kawai suka tsira.

    Jirgi na biyu kuwa da ya taso daga Myanmar ya nitse kwana ɗaya bayan na farkon, inda mutane 226 suka mutu.

  3. Alƙaluman laifuka a Afrika ta kudu sun ƙaryata iƙirarin Trump na kisan fararen fata - Ministan ƴan sanda

    akwatin gawarwaki a Afrika ta Kudu

    Ministan ƴansanda a Afirka ta Kudu ya ce alƙaluman laifuffuka da aka fitar a baya-bayan nan ya ƙaryata iƙirarin yi wa farar fata ƴan kasar kisan ƙare dangi.

    Senzo Mchunu ya ce a tsakanin Janairu da Maris, biyar cikin mutum shida da aka kashe a gonaki baƙar fata ne, ɗaya ne farar fata.

    Shugaba Donald Trump ne ya tado da iƙirarin yi wa farar fata manoma kisan ƙare dangi ba tare da bayar da hujja ba a ganawarsa da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

    Wannan ne karon farko da aka fayyace alƙaluman laifuka na Afirka ta Kudu ta hanyar yin bayani kan rukunin mutanen da laifukan suka shafa, sai dai ministan ya ce hakan ya zama dole saboda zarge-zargen da aka yi na baya-bayan nan.

  4. An kama matar da ake zargi da kai harin wuƙa a tashar jirgin ƙasa a Jamus

    tashar jirgin ƙasa a Hamburg da ke Jamus

    Asalin hoton, Reuters

    An kai wa mutane dayawa harin wuƙa a babbar tashar jirgin ƙasa da ke birnin Hamburg a Jamus.

    Hukumar kashe gobara ta ce mutane 12 sun jikkata, uku daga cikinsu suna cikin halin rai a hannun Allah.

    Ƴan sanda sun ce sun kama wata mata ƴar shekara 39 da ake zargi ita ta kai harin.

    Ƴan sanda sun ce suna gani ta kai harin ne ita kaɗai, sai dai suna ci gaba da bincike.

    Zuwa yanzu dai ba su bayyana ko mene ne dalilinta na kai harin ba.

  5. An soma musayar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine

    Fursunoni Ukraine da Rasha ta saki

    Asalin hoton, Volodymyr Zelensky/X

    Rasha da Ukraine sun soma gagarumin musayar fursunoni, inda a yanzu dukkaninsu suka miƙa mutane 390 cikin waɗanda aka kama lokacin yaƙin.

    Ministan tsaron Rasha ya ce mutanen da aka saki daga ɓangarorin biyu sun haɗa da fursunonin yaƙi 270, yayin da sauran 120 kuma fararen hula ne.

    Wannan shi ne matakin farko na shirin musayar fursunoni 1000 daga ƙasashen biyu wanda aka amince da shi a wata tattaunawa ta kai tsaye a makon da ya gabata.

    Wannan zai kasance musaya mafi girma tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

    Shugaba Zelensky ya ce yana sa ran za a ci gaba da musayar a kwanakin ƙarshen mako.

    Ya bayyana musayar fursunonin a matsayin abu ɗaya tilo mai muhimmanci da ya fito daga tattaunawar makon da ya gabata a Turkiyya, inda ya zargi Rasha da toshe sauran abubuwan.

  6. Sanatocin Katsina sun amince Dikko Radda ya zarce

    Yan siyasa a Katsina

    Zaɓaɓɓun sanatoci da ƴan majalisar tarayya a jihar Katsina ƙarƙashin jami'yya mai mulki ta APC sun sanar da amincewa da kuma tabbatar da gwamnan jihar Umar Dikko Radda a matsayin ɗan takarar jami'yyar a zaɓen 2027.

    Sanatocin ta bakin ɗaya daga cikinsu, Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua a cikin wani bidiyo da suka fitar, ya ce sun gamsu da salon mulkin gwamnan, wanda hakan ya sa suka amince da ci gabansa a matsayin ɗan takararsu.

    Sanatan ya ce sun yaba da ƙoƙarin gwamnan wajen ci gaban jihar, musamman saboda cika alƙawuran da ya yi wa al'ummar ƙasar da ya shafi ci gabansu kamar tsaro da ilimi da noma wanda ya sa suka gamsu da shi.

    Sanatocin sun kuma yi kira ga al'ummar jihar ta Katsina da su goyi bayansu, su kuma ƙara bai wa gwamnan goyon baya a tsare-tsarensa da ke da nufin kawo ci gaba a jihar.

    Ko a jiya alhamis ma gwamnonin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki sun amince da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar a zaɓen 2027.

    Hakan na zuwa ne kusan shekara biyu bayan hawansu mulki, wanda ya sa masana ke ganin wani muhimmnin saƙo ne ga masu hamayya walau dai a cikin jam'iyyar ko kuma a wajen ta domin su sake shiri.

  7. Jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya koka kan Sudan ta Kudu

    Masu ɗauke da bindiga a Sudan ta kudu

    Asalin hoton, AFP

    Babban jami'in kula da haƙƙin bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya koka kan mawuyacin halin da ake fuskanta a ƙasar Sudan ta Kudu, sakamakon karin tashin hankali da ake samu tsakanin dakarun gwamnati da kuma ƙungiyoyin ƴan tawaye.

    Volker Turk ya ce ya kamata duka ɓangarorin su kai zuciya nesa su kuma bi sharuɗɗan da aka gindaya a yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a shekara ta 2018.

    Ƙungiyar agaji ta Medicine Sans Frontières ta ce sama da fararen hula 80,000 da suka yi gudun hijira zuwa ƙasar Habasha na fuskantar mummunar barazana ga lafiyarsu.

    Rikice-rikicen na kwanakin nan dai sun yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama inda wasu dubbai kuma suka rasa matsugunansu.

  8. Jami'ar Harvard ta maka gwamnatin Donald Trump a kotu

    Jami'ar Harvard ta maka gwamnatin Donald Trump a kotu kan matakin da ta ɗauka na haramta mata ɗaukar ɗaliban ƙasashen waje.

    A cikin ƙarar da aka shigar gaban kotun, Harvard ta ce matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Amurka, kuma zai yi mummunar tasiri kan jami'ar.

    Ta zargi gwamnatin ƙasar da ramuwar gayya kan jami'ar, sakamakon ƙin sadaukar da ƴancinta da ta yi.

    Gwamnatin Trump ta zargi Harvard da rura wutar tashin hankali da ƙyamar Yahudawa da kuma haɗa kai da jam'iyyar kwamunisanci ta China.

    Ƙasashen China da Jamus dai duk sun nuna adawa da matakin na gwamnatin Amurka.

  9. An kama matar da ake zargi da kashe jinjirin kishiyarta da guba

    , Muhammad Rabiu

    Asalin hoton, Kaduna Police

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce ta kama da tsare wata mata mai suna Zaliha Shu'aibu bisa zargin kashe ɗan kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa da maganin ƙwari.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansur Hassan ya fitar, al'amarin ya faru ne a ranar 13 ga watan nan na Mayu a gidansu da ke ƙauyen Malari a ƙaramar hukumar Soba.

    Sanarwar ta ce shaidu sun ce uwar yaron dai ta fita daga ɗakinta domin shiga banɗaki lokacin da kishiyar tata ta shigar mata ɗaki kuma bayan ta koma ɗakin ne ta ga kishiryar rungume da ɗan nata.

    Bayan ta miƙa mata jaririn ne sai uwar ɗan ta fahimci yadda kumfa ke fita daga bakin yaron nata sannan kuma akwai rauni a wuyansa, inda yaron ya kece da kuka.

    Bayan bincike, rundunar ƴansandan ta ce matar ta tabbatar da cewa ta aikata laifin ne da taimakon ƙanen mijinta wanda shi shi ne ya bata gubar da ta yi amfani a kan jaririn. Ƙanen mijin dai ya gudu ba a kai ga kama shi ba tukunna.

  10. Ana sa ran Rasha da Ukraine za su fara musayar fursunoni

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran cewa Rasha da Ukraine za su fara musayar fursunoni a tsakaninsu, bayan da suka cimma matsaya mafi muhimmanci tun bayan fara yaƙin.

    Ɓangarorin biyu sun ce za su yi musayar fursunoni 1,000, bayan tattaunawarsu ta farko kai tsaye da aka yi cikin sama da shekaru uku a birnin Istanbul.

    Da Moscow da Kyiv dai ba su tabbatar da fara musayar fursunonin ba amma ana tunanin za a ɗauki kwanaki da dama ana yi.

    A wani ɓangare kuma, ministan harkokin wajen Rasha ya yi watsi da yiwuwar fadar Vatican ta sake karɓar baƙuncin wani zagaye na tattaunawar kai tsaye, lamarin da ya ci karo da ra'ayin da shugaban Amurka Donald Trump bayyana a baya.

  11. Za a haramta wa Yair Golan shiga rundunar sojin Isra'ila bisa zargin zagon ƙasa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila, Isra'ila Katz, ya ce za a haramtawa wani babban ɗan siyasar adawa, Yair Golan, shiga aikin dakarun ko-ta-kwana na rundunar tsaron ƙasar, bayan kakkausar sukar da ya yi a baya-bayan nan kan yadda gwamnati ke gudanar da yaƙin Gaza.

    Mista Katz ya zargi Mista Golan, da yi wa gwamnatin Isra'ila zagon ƙasa bayan ya ce gwamnati na aika sojoji su kashe jarirai a Gaza a matsayin abin sha'awa.

    Mista Golan ya mayar da martani da cewa zai ci gaba da yin duk abin da zai iya domin tabbatar da tsaron Isra'ila ,inda ya ce Mista Katz ya je ya ci gaba da yi wa firaministan Isra'ila Benyamin Natanyahu fadanci.

    Tun da farko Mista Netanyahu da kansa ya zargi wasu ƙawayen Isra'ila da ƙarfafa gwiwar Hamas bayan sukar da suka yi kan yadda Isra'ila ke gudanar da yaƙin Gaza.

    Hukumomi a Gaza dai sun ce aƙalla mutane 16 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai daga tsakar daren ranar Alhamis zuwa safiyar Juma'a.

  12. Ba ni da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 - Yahaya Bello

    .

    Asalin hoton, Yahaya Bello

    Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ba ya sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa domin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 mai zuwa.

    Yahaya Bello ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Michael Ohiare ya fitar, inda a ciki ya ce Yahaya Bello ya yi mamakin ganin wani faifan bidiyon da ake yaɗawa na yaƙin zaɓensa na 2022, amma ake cewa ya fara kamfe ne na zaɓen 2027 kamar yadda jaridun Najeriya suka ambato.

    Sanarwar ta ce, "yayin da muke bayyanawa ƙarara cewa Yahaya Bello ba shi da burin takarar shugaban ƙasa a 2027, muna ƙara jaddada matsayarmu na goyon bayan sake zaɓar Tinubu a 2027'', in ji shi.

    Mista Ohiare ya bayyana masu yaɗa labarin da ''masu yaɗa ƙarya'', waɗanda ba su da aikin yi sai ƙirƙirar ƙarya da yaɗa ta.

    Yahaya Bello dai ya yi takarar shugabancin ƙasa 2023, kodayake ya daga baya ya janye a lokacin zaɓen fitar da gwani.

  13. Gwamnan Akwa Ibom ya bayyana aniyarsa ta komawa APC

    Gwamnan Akwa Ibom/X

    Asalin hoton, Pastor Umo Eno

    Bayanan hoto, Gwamnan Akwa Ibom, Pastor Umo Eno

    Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya umarci duka kwamishinoninsa da sauran mutanen da ya naɗa muƙamai a gwamnatinsa su koma jam'iyyar APC tare da shi ko su sauka daga muƙamansu.

    Gwamna Eno - wanda ɗan jam'iyyar PDP ne - ya bayar da umarnin a ranar Alhamis lokacin zaman majalisar zartaswar jihar, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ambato.

    An dai ɗauki makonni ana raɗe-raɗin cewa gwamnan zai fice daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC.

    “Ba sabon labari ba ne ficewata daga jam'iyyarmu, idan ma ba ku sani ba, ya kamata a ce yanzu kun sani,'' in ji shi.

    Gwamnan ya faɗa wa kwamishinonin nasa cewa ba dole ne su bi shi zuwa jam'iyyar APC ba, amma su kwana da sanin cewa ba zai ci gaba da aiki da su ba, matsawar suna jam'iyyar da ba tasa ba.

    Mista Eno ya ce duk da yana ƙaunar PDP, ba ya hango nasarar jam'iyyar a zaɓuka masu zuwa, sakamakon rigingimun da jam'iyyar ke ciki.

    “Ina son PDP, kuma ina son zama a cikinta, amma a bayyane take ƙarara cewa babu wani ma'auni da zan iya auno wa kaina nasara a zaɓukan da ke tafe..,'' in ji shi.

    Idan Mista Eno ya koma APC zai kasance gwamnan PDP na biyu da ya koma APC cikin ƙasa da wata biyu.

    A cikin watan Afrilu ne gwamna jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya fice daga PDP zuwa APC.

    Wani abu da masana ke ganin gagarumar barazana ce ga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP..

  14. Trump ya ce zai ƙaƙaba harajin kashi 25 kan wayoyin iPhone

    Wayoyin iPhone

    Asalin hoton, APPLE

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ƙaƙaba harajin kashi 25 kan wayoyin iPhone da ba a ƙera a cikin ƙasar ba.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce yana son ganin an riƙa ƙera wayoyin a Amurka, ''ba Indiya ko wani wuri a duniya ba'.

    Tuni dai hannayen jarin kamfanin Apple ya fara sauka.

    Kamfanin na Apple ya zaɓi a Indiya a matsayin wurin da zai riƙa ƙera wayoyinsa domin kauce wa harajin China.

  15. 'An kashe ƴan bindiga sama da 13,000 a lokacin Tinubu'

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Facebook

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa dakarun ƙasar sun kashe ‘ƴan ta’adda da masu aikata ta’asa a ƙasar sama da 13,543 a yankin arewa maso gabashin ƙasar tun bayan hawan shugaban ƙasar kan mulki kimanin shekara biyu da suka gabata.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoto kan nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a ɓangaren tsaro, wanda mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayar a ranar Talata.

    Haka gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa an ƙwato tare da lalata makamai sama da 11,118 a tsakankanin lokacin a yankin na ƙasar.

    Ribadu ya ƙara da cewa iyalan ƴan Boko Haram da ISWAP sama da 124,408, sun miƙa wuya, sannan an ƙwato alburusai sama da 252,596.

    Yankin arewa maso gabas dai ya ƙunshi jihohin Borno da Adamawa da Yobe da Bauchi da Gombe da Taraba, kuma yanki ne da ya shafe sama da shekara 10 yana fama da rikice-rikicen Boko Haram wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.

  16. Ana buƙatar aƙalla motocin agaji 600 a kowace rana a Gaza - MDD

    Motocin agaji

    Asalin hoton, Reuters

    Kamar yadda muka bayar da rahoto, sojojin Isra'ila sun ce motocin agaji 100 ne suka shiga yankin Gaza a a ranar Alhamis.

    To amma mota nawa ake buƙata domin wadatar agajin a Gaza?

    Kafin fara yaƙin, kusan mota 500 ne ke shiga Gaza a kowace rana, ɗauke da abinci da magunguna da abincin jarirai da kayan aikin asibiti.

    To sai dai bayan fara yaƙin adadin ya yi matuƙar raguwa.

    A yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana buƙatar aƙalla mota 600 na kayan agaji a Gaza, domin magance matsalolin jin ƙai a yankin.

    Mota 100 a kowace rana ''ba za ta wadatar'', a abincin da ake bukata a Gaza ba, kamar yadda jami'in Hukumar Kula da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, Antoine Renard ya shaida wa BBC a farkon makon nan.

    Isra'ila ta sha musanta samun ƙarancin abinci a Gaza.

  17. Ba ma so a miƙa Hamdiyya ga jami'an ƴansanda - Amnesty

    Hamdiyya Sharif

    Asalin hoton, FB/Abba Hikima

    Bayanan hoto, Hamdiyya Sharif

    Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta soki matakin da hukumomi ke shirin ɗauka na miƙa matashiyar nan da aka gano a jihar Zamfara, Hamdiyya Sharif ga jami’an ƴansanda.

    Shugaban ƙungiyar Mallam Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa bayanan da suke samu shi ne kwamishinan ƴansanda jihar Zamfara ya nace sai an mayar da Hamdiyya Sharif ga hukumar ƴansandan Sokoto, maimakon ba ta kulawar likitoci, wanda a cewarsa shi ta fi buƙata a halin yanzu.

    ''Mu yanzu abin da muka fahimta a taƙaice shi ne kenan an kamata, ko kuma sun riƙe ta'', in ji shi.

    Mallam Isa Sanusi ya yi kira ga hukumomin Najeriya su bai wa matashiyar kariya saboda yadda rayuwarta ke cikin ''barazana''.

    A yammacin ranar Laraba ne aka gano Hamdiyya Sherif a wani ƙauye cikin jihar Zamfara, bayan ɓatan-dabo da ta yi a ranar Talata a jihar Sokoto.

    A bayanan da wata makusanciyar Hamdiyya ta yi wa BBC, ta ce wasu mutane ne suka sace matashiyar tare da yi mata wata allura, lamarin da ya kai ga fita daga cikin hayyacinta, inda daga baya ta tsinci kanta cikin wani daji a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

    Sanarwar Amnesty ta ce “yanzu haka rayuwar Hamdiyya Sharif na cikin haɗari, kuma wajibi ne hukumomin Najeriya su ba ta kariya”.

    Hamdiyya na fuskantar shari’a a kotu, inda gwamnatin jihar Sokoto, da ke arewa maso yammacin Najeriya ke tuhumar ta da zargin yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan ta yi wani bidiyo tana sukar gwamnati kan rashin ɗaukan matakan da suka dace kan matsalar tsaro.

    Sokoto na cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

    Ƙauyuka da dama sun yi ƙaura sanadiyyar kashe-kashen wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa duk da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi wajen yaki da matsalar.

    Amnesty International da lauyoyin Hamdiyya na nuna yatsa ga gwamnatin jihar Sokoto, wadda suka ce tana ƙoƙarin rufe bakin masu suka, lamarin da suka ce ya saɓa tsarin ƴancin fadin albarkacin baki.

  18. Ƙungiyar ƴantawayen Myanmar ta ɗauki alhakin kisan wani tsohon Janar

    Wata ƙungiyar ƴantawaye ta cikin gari a Myanmar ta ɗauki alhakin kashe tsohon babban janar soji na ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar 'Golden Valley Warriors' ta fitar, ta ce ta kai wa Cho Tun Aung hari ne saboda yadda yake tallata gwamnatin mulkin sojin da ke faɗa da ƙungiyoyi masu rajin dimocraɗiyya da mayaƙan ƙungiyoyin tawaye na ƙabilu a ƙasar.

    Rahotonni sun ce an harbi tsohon Janar din har sau hudu a ƙirjinsa a wajen gidansa da ke Yangon.

    Tun bayan ƙwace mulki a wani juyin mulki shekara huɗu da suka gabata, gwamnatin mulkin sojin Myanmar ke gudanar da wani yaƙin basassa mai sarƙaƙaiya da ƙungiyoyin ƴan tawaye.

  19. Dubban gidajen mai na ci gaba da rufewa a arewacin Najeriya

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban gidajen mai a Najeriya na ci gaba da dakatar da sayar da mai a sassa daban-daban a yankin arewacin ƙasar, sakamakon ƙaruwar asarar kuɗaɗe da suka ce suna yi.

    Masu gidajen mai sun bayyana cewa rashin tabbas ko yawan sauyawar farashi da sauran matsaloli ne ke tilasta musu ɗaukar matakin.

    Abdullahi Idris, mataimakin shugaban ƙungiyar masu samar da mai da gas ta Najeriya, wato NOGASA ya shaida wa BBC cewa mafi yawan gidajen man arewacin Najeriya ba sa iya cin riba, sai dai faɗuwa.

    ''Ana sayo mai daga Legas kan naira 835, ko 840 a kan kwace lita, sannan ka biya kuɗin mota, kowace lita a kan naira 50 zuwa Abuja, ko 55 zuwa Kano da Kaduna, to za ka ga farashin ya ƙure, ribar ba ta wuce naira 10'', in ji shi.

    ''To wannan naira 10 kuma idan ka haɗa galibi ba ta wuce naira 500,000, to idan wani aikin gyara ya taso a gidan mai, kuma ka biya kuɗin sauran hidimomin gidan mai, sai ka ga ta ƙare'', kamar yadda ya bayyana.

    Mataimakin shugaban ƙungiyar ta NOGASA ya ce a kudancin Najeriya ba a fuskantar wanann matsalar, saboda masu saro man ba su da yawa, kuma kuɗin motarsu bai fi naira 15 ba, don haka suna samun ribar fiye da naira 100, saɓanin arewa.

  20. Ana ƙoƙarin kuɓutar da masu haƙar ma'adinai kusan 300 a Afirka ta Kudu

    Mamallakan wata mahaƙar ma'adinai a Afirka ta Kudu sun ce suna ƙoƙarin kuɓutar da masu haƙar ma'adinai kusan 300 da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa.

    Kamfanin Sibanye Stillwater da ke aiki a mahaƙar ya ce duka masu haƙar ma'adinan da ke mahaar Kloof a kusa da Johanesberg ba sa cikin wani hatsari, kuma ana sa ran ceto su nan ba da jimawa ba.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun bayar da rahoton cewa ɓaraguzai ne suka lalala ramukan mahaƙar, lamarin da ya maƙalar da masu aikin a ciki a ranar Alhamis da daddare.

    A shekarar 2024 mutum 42 ne suka mutu a Afirka ta Kudu sakamakon ruftawar mahaƙar ma'adinai.