window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarin wasannin da zai gudana daga ranar Asabar 24 zuwa 30 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Ahmad Bawage

  1. Liverpool ta kusa kammala cinikin Florian Wirtz

    Wirtz

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta yi nisa a tattaunawar da take yi don sayen Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen.

    Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ta sake gabatar da tayi mai kyau, a yunkurinta na kammala cikin ɗan wasan.

    An bayyana cewa Liverpool ta gabatar da tayin sayen ɗan wasan mai shekara 22 kan fam miliyan 109.

    Wirtz ya nuna sha'awar komawa ƙungiyar Merseyside kafin fara kaka mai zuwa.

    A farkon watan nan ne, BBC ta ruwaito cewa Manchester City ta janye daga son sayan ɗan wasan, inda ta bayar da dalilin cewa ya yi mata tsada.

    Duk da cewa Bayern Munich ta nuna sha'awar kan Wirtz - amma ɗan wasan na tsakiya ya ce ya fi son komawa Anfield.

    Wirtz ya fara buga wa Leverkusen kwallo yana da shekara 17, inda ya zura kwallo 57 a wasanni 197 da ya buga wa ƙungiyar ta Jamus.

    Ya taimaka mata wajen lashe kofin Bundesliga karon farko a tarihi a 2024 - sannan ya zura kwallo shida a fafatawa 29 da ya yi wa Jamus.

  2. Arsenal na shirin ɗaukar Sesko

    Benjamin Sesko

    Asalin hoton, Getty Images

    Jaridu da dama na ruwaito cewa ƙungiyar Arsenal ta faɗa tsundum cikin tattaunawar ɗaukar ɗan wasa Benjamin Sesko daga RB Leipzig.

    Tuni ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Slovenia ya nuna aniyarsa ta barin ƙungiyarsa mai buga gasar Bundesliga ta Jamus.

    Arsenal na fafutikar ganin ta samu jajirtaccen mai zura ƙwallo a raga, kasancewar ta kwashe tsawon lokaci tana fama da rashin hakan.

    Sai dai idan Arsenal ɗin na son ɗaukar ɗan wasan mai shekara 21 wajibi ne sai ta fitar da zunzurutun kuɗi fam miliyan 92.5, kamar yadda jaridar The Telegraph ta ruwaito.

    A watan Janairu Arsenal ta yi yunƙurin ƙarfafa gaban nata inda ta taya Sesko da kuma Ollie Watkins na Aston Villa, sai dai an ƙi sallama mata.

    Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Mikel Arteta ta ƙare kakar wasan 2024-25 ne da kame-kame bayan ƴan wasanta na gaba Kai Havertz da Gabriel Jesus suka samu rauni a farkon shekara.

    Haka nan ma ɗan wasa Bukayo Saka ya gaza taka wa kungiyar wasanni da dama a cikin kakar sanadiyyar rauni da ya samu.

  3. 'Club World Cup sabuwar kaka ce ga Man City'

    Man City

    Asalin hoton, Getty Images

    Gasar Club World Cup na a matsayin "sabuwar kakar wasanni" ba "ci gaban kakar da ta wuce ba", a cewar shugaban ƙungiyar Manchester City Khaldoon Al-Mubarak.

    City ta gamu da koma-baya a kakar 2024-25, inda ta ƙasa lashe ko da kofi ɗaya a karon farko cikin shekara takwas - ta kare a matsayi na uku a teburin gasar Premier League.

    Sun buga wasansu na karshe a kakar wasanni ta bana da Fulham a Lahadin da ta gabata, sai dai suna cikin waɗanda za su je buga gasar Club World Cup nan da kwanaki 24 da ke tafe - za a fara gasar da aka yi wa fasali ranar 14 ga watan Yuni a Amurka.

    "Ƙungiyar za ta huta cikin sauran kwanaki da suka rage, sai su fara shirin tunƙarar kakar wasanni mai zuwa sannan su zarce zuwa gasar Club World Cup kai-tsaye," in ji Khaldoon.

    "Muna farin cikin samun damar fafatawa a gasar. Ina son sauyin da aka yi.

    "Wannan ce farawar sabuwar kakar wasanni, ba ci gaban kakar da ta gabata ba."

    Tawagar Pep Guardiola za ta tafi zuwa Amurka ne bayan lashe gasar shekara biyu da suka wuce, bayan doke Fluminese a wasan karshe a Saudiyya.

    Khaldoon ya ce City na shiri domin ganin ta fara gasar da sabuwar tawagarta.

  4. Labaran da jaridu ke wallafa wa kan cinikin ƴan ƙwallo

    Liverpool na son sama da fam miliyan 20 kan Kelleher. (Athletic)

    Napoli na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Lille dan kasar Canada Jonathan David, mai shekara 25, wanda itama Juventus ta tuntube shi. (Sky Sports)

    Chelsea ta bi sahun Juventus wajen yin wani bincike a hukumance da Sporting Lisbon kan batun neman dan wasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, wanda itama Arsenal ke nema. (Record Portuguese)

    Juventus na sha'awar sayen dan wasan gaban Real Madrid dan kasar Brazil, Endrick, mai shekara 18, a matsayin aro. (Calciomercato)

    Tsohon kocin Juve Massimiliano Allegri na shirin komawa AC Milan a matsayin koci. Dan shekaru 57 ya shafe shekaru hudu a San Siro tsakanin 2010 da 2014. (Calciomercato)

    Ipswich Town ta yi wa Chelsea tayin dan wasanta dan kasar Sipaniya, Marc Guiu, mai shekara 19 a matsayin aro a a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Fabrizio Romano).

  5. Real Madrid ta amince da yarjejeniyar sayen Alexander-Arnold

    Trent Alexander-Arnold

    Asalin hoton, Getty Images

    Trent Alexander-Arnold zai zama sabon ɗan wasan Real Madrid ranar Lahadi 1 ga watan Yuni, bayan da Liverpool ta amince da fam miliyan 10 domin ta saki ɗan wasan da wuri.

    Matakin na nufin cewa ɗan wasan baya na England zai kasance cikin tawagar da za ta buga wa Real gasar Club World Cup.

    Arnold, wanda tun da farko ya sanar da cewa zai bar Liverpool, ya amince da yarjejeniyar shekara shida.

    Idan da Liverpool ba ta saki ɗan wasan mai shekara 26 da wuri ba, da zai tafi a kyauta idan yarjejeniyarsa ta kare ranar 30 ga watan Yuni.

    Fifa ta amincewa ƙungiyoyi sayan ƴan wasa bayan buɗe kasuwar saye na ƙanƙanin lokaci daga 1-10 ga watan Yuni saboda sabuwar gasar ta Club World Cup wanda za a yi a Amurka - za a fara gasar ranar 14 ga watan Yuni.

    Alexander-Arnold ya kasance a Liverpool da ta zama ƙungiyar mahaifarsa tun yana da shekara shida.

    Ya lashe gasar Premier biyu da Champions League da Fifa Club World Cup da Uefa Super Cup da FA Cup da kuma League Cup a tsawon zamansa a Liverpool.

  6. Chelsea ta shirya biyan fam miliyan 30 kan Leam Delap

    Liam

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta shirya biyan fam miliyan 30 don sayen ɗan wasan gaba na Ipswich Town Liam Delap.

    Manchester United da Everton da Newcastle da kuma Nottingham Forest na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Delap, wanda Ipswich ke neman fam miliyan 30 a kansa, amma Man Utd na da damar sayen ɗan wasan ita ma.

    Ɗan wasan mai shekara 22 ya koma Ipswich daga Manchester City a bara kan yarjejeniyar fam miliyan 20.

    "Liam na duba makomarsa ta gaba, wanda ina ga yana da damar yin haka kuma muna goyon bayansa," a cewar kocin ƙungiyar Kieran McKenna.

    An bayyana cewa ɗan wasan ya fi son ya koma taka leda a Stamford Bridge - sai dai ana ci gaba da tattaunawa.

  7. Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

    Fernandes

    Asalin hoton, Getty Images

    Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United a mako mai zuwa, inda yake tunanin komawa Al-Hilal ta Saudiyya waɗanda suka yi masa tayin albashi mai tsoka.

    An bayyana cewa wakilan Fernandes sun gana da jami'an Al-Hilal cikin kwanaki da suka gabata domin samun mafita da za ta kai ga ɗan wasan mai shekara 30 ya koma ƙungiyar.

    Batun dai na janyo muhawara a kafofin sada zumunta a daidai lokacin da Man Utd ɗin tayi balaguro zuwa nahiyar Asiya don buga wasannin sada zumunta.

    Duk da cewa Bruno na ci gaba da ayyukansa a matsayin kyaftin ɗin United, sai dai bai fayyace komai kan makomarsa ba, abin da ya kai wasu ke ganin cewa yana daf da barin ƙungiyar.

    Sai dai wasu majiyoyi na cewa United ba ta tayar da hankalinta kan lamarin ba zuwa yanzu.

  8. Man City za ta ƙara sayo ƴan wasa kafin Club World Cup

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Manchester City, Khaldoon Al Mubarak ya yi alkawarin za su kara sayo ƴan wasa kafin a fara Club World Cup a watan Yuni.

    Gasar Premier League ta amince a buɗe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo, domin ƙungiyoyinta su kara karfi kan a fara gasar da Amurka za ta karɓi bakunci.

    City za ta buga wasan farko a cikin rukuni da Wydad ranar 18 ga watan Yuni a fafatawar da za a yi tsakanin ƙungiya 32 a karon farko.

    Tun farko ƙungiyar Etihad ta yi fatan lashe Premier na biyar a jere, sai kuma ta ci karo da kalubalen da ta sha wahala a kakar da aka kare ta bana.

    Da ƙyar da gumin goshi City ta kare a mataki na uku a ranar karshe ta rufe gasar, za ta je Champions League a baɗi.

  9. Club World Cup: Nawa ne ladan lashe kofin?

    Club World Cup

    Asalin hoton, Fifa

    Jimilla za a raba £775m tsakanin ƙungiya 32 da za su fafata a Fifa Club World Cup, kenan duk wadda ta lashe kofin za ta samu kimanin £97m.

    Ga jerin ladan da za a bai wa ƙungiya da za ta buga Fafa Club World Cup

    • Wasannin cikin rukuni: £1.5m idan ka ci wasa / £800,000 da zarar an yi canjaras
    • Zagayen ƴan 16: £5.8m
    • Zagayen kwata fainal: £10.1m
    • Zagayen daf da karshe: £16.2m
    • Waɗanda za su buga wasan karshe: £23.2m
    • Wadda ta lashe kofin: £30.0m

    Haka kuma akwai ladan halartar gasar ga ƙungiya 32.

    Sai dai ƙungiyoyin Turai za su fi samun lada fiye da sauran ƙungiyoyin nahiyoyi da za su buga Fifa Club World Cup, inda mafi yawa ƙungiya daga Turai za a bata £29.6m, karancin abin da za ta karɓa kuwa zai kama £9.9m.

  10. Gauff ta kai zagaye na uku a French Open

    Coco Gauff ta kai zagaye na uku a French Open, bayan da ta doke matashiya, Tereza Valentova ranar Alhamis a birnin Paris.

    Ƴar kasar Amurka, wadda ta yi ta biyu a gasar ta Roland Garros a 2022 ta yi nasarar cin 6-2, 6-4 cikin minti 75 a filin wasa na Suzanne Lenglen.

    Gauff, wadda karo huɗu a baya tana kai wa daf da karshe za ta fuskanci Marie Bouzkova a zagayen ƴan wasa 32 da za su rage.

  11. Chelsea na kan gaba wajen zawarcin Liam Delap

    Liam Delap

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea tana sawun gaba wajen zawarcin ɗan wasan Ipswich Town, Liam Delap.

    Masu son sayen ɗan ƙwallon sun haɗa da Manchester United da Everton da Newcastle da kuma Nottingham Forest.

    Delap yana da ƙunshin yarjejeniya ta £30m, kuma Manchester City ma tana daga cikin masu son ɗaukar matashin.

    Chelsea, wadda ta lashe Conference League ranar Laraba, ta samu gurbin shiga Champions League na baɗi, sakamakon kammala gasar Premier League a mataki na huɗu a kan teburi.

    Delap ya buga wasa 32 a Premier League a Ipswich a kakar da aka kammala da cin ƙwallo 12.

    Ipswich za ta koma buga Championship a baɗi, bayan da ta kare a matsayi na 19 a kasan teburin Premier League, kuma.za ta karɓi ɗan wasan Chelsea, Marc Guiu a musaya da Delap.

    Ɗan wasan Sifaniya ya ci ƙwallo 14 a Chelsea, wanda ya sha fama da jinya.

  12. Nawa ne ladan lashe Conference League?, Real Betis 1-4 Chelsea

    Maresca

    Asalin hoton, Getty Images

    Ladan ƙudin da za a bai wa Chelsea sakamakon doke Real Betis da lashe Europa League ya kai £2.5m, kamar yadda Uefa ta wallafa a shafinta na Intanet.

    Tun da aka fara wasannin gasar bana, Chelsea za ta samu kuɗi a gasar fiye da wanda ta lashe kofin.

    Wasannin da ta yi a gasar za ta karɓi £167,000 yayin da ta kai zagayen ƴan 16 za a bata £670,000.

    Haka kuma duk ƙungiyar da ta kai kwata fainals za a bata £1m, kuɗin kai wa daf da karshe kuwa shi ne £2m kuma da zarar ka yi nasara a zagayen daf da karshe za a bayar da £3.3m.

    Kenan ƙwazon da Chelsea ta yi a gasar ta Conference League za ta samu kusan £9-10m.

  13. Al Nassr na fatan Ronaldo zai ci gaba da taka mata leda

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Daraktan wasannin Al Nassr, Fernando Hierro ya sanar a ranar Alhamis cewar suna yin iya kokarinsu, domin Cristiano Ronaldo ya ci gaba da taka musu leda.

    Ya faɗi hakan ne bayan wasu rahotannin da aka ce ƙyaftin ɗin tawagar Portugal zai buga Fifa Club World Cup da za a fara daga 14 ga watan Yuni a Amurka.

    A makon jiya Wydad Casablanca ta musanta batun da ake cewar ta ɗauki Ronaldo, domin ya ja ragamar ƙungiyar a Fifa Club World Cup a bana.

    Ranar Litinin bayan da aka kammala gasar tamaula ta Saudiyya, Ronaldo ya sanar a X cewar ''An rufe wannan babin.''

    Hierro ya ce yaga sakon, amma Ronaldo yana da sauran ƙunshin yarjejeniya da su zuwa karshen watan Yuni, kuma suna iya kokarin ganin mai shekara 40 ya ci gaba da zama a Al Nassr.

    Ronaldo shi ne kan gaba a gasar Saudiyya da ƙwallo 24 a raga, amma Al Nassr ta kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Asia ta Champions League, bayan da ta yi ta uku a teburi.

    Za a fara gasar Fifa Club World Cup, wadda aka sauya mata fasali daga 14 ga watan Yuni a Amurka, dauke da ƙungiya 32.

    Lionel Messi zai buga gasar tare da Inter Miami da za su fafata da Al Ahly a filin the Hard Rock a Miami.

  14. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo, Daga jaridu

    Dan Burn

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta tattauna da wakilin ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres a Lisbon tare da gabatar da tayin fam miliyan 58.7 ga ɗan wasan na Sweden. (Correio da Manha - in Portuguese, external)

    Manchester United ta amince da sharudan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ipswich, Liam Delap inda take jiran hukunci daga ɗan wasan na gaba. (ESPN, external)

    Ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 40, na shirin barin ƙungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, domin cimma sabuwar kwantiragi da wata ƙungiyar gabanin soma wasannin ƙungiyoyin duniya da za a soma a ranar 15 ga watan Yuni a Amurka.(Telegraph - subscription required, external)

  15. Menene a gaban Chelsea bayan lashe Conference League?

    Maresca

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan da aka kammala gasar Premier League, Chelsea ta lashe Conference League - yanzu menene a gaban ƙungiyar ta Stamford Bridge?

    Ƙungiyar da Enzo Maresca ke jan ragama ba za ta samu hutu da yawa ba, sakamakon kalubalen dake gabanta.

    • 14 June - Club World Cup ranar da za a fara a Amurka (01:00 BST, 15 June)
    • 28 June - Za a shiga zagaye na biyu wato Knockout stages a Club World Cup
    • 13 July - Za a buga wasan karshe a Club World Cup
    • 16 August - Za a fara gasar Premier League kakar 2025/26
    • 16 September - Za a fara wasannin Champions League league kuma Chelsea za ta buga gasar a karon farko tun bayan 2022/23.

  16. Sancho da Anthony sun taka rawar gani bayan barin Man United, Manchester United

    Conference LEAGUE

    Asalin hoton, Getty Images

    Jadon Sancho da Antony sun rungumi juna bayan tashi daga wasan karshe a Conference League a Poland ranar Laraba.

    Ƴan wasan sun taka rawar gani, bayan da suka bar Manchester United suka je suka buga wasannin aro.

  17. Ba a fayyace makomar Sancho ba a Chelsea, Chelsea

    Lokacin da Jadon Sancho ya je Chelsea daga Manchester United domin buga wasannin aro ranar 31 ga watan Agusta, ƙungiyar Stamford Bridge ta yi farin ciki da ƙulla yarjejeniyar.

    Tun farko matashin wanda ya koma United kan £73m daga Borussia Dortmund a Yulin 2021 ya sha fama da kalubale a Old Trafford.

    Chelsea ta amince za ta sayi sancho kan £20 zuwa 25m - idan ta kare kakar Premier League a mataki sama da na 14 a teburi - ko kuma za ta biya United £5mdomin Sancho ya sake komawa Old Trafford.

    Sai dai Chelsea ta kare a mataki na huɗu a teburin Premier League sannan za ta je Champions League a baɗi, kuma ta lashe Conference League.

  18. Chelsea ta ɗauki dukkan kofunan gasar Uefa, Real Betis 1-4 Chelsea

    Conference League

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta kare kakar bana da katafaren kofin Conference League, kuma za ta je Champions League a badi.

    Chelsea ta doke Real Betis da cin 4-1 a Poland ranar Laraba, ta zama ta farko da ta lashe dukkan kofunan Uefa, bayan Champions League biyu da Europa biyu da Cup winn ers Cup biyu da Super Cup biyu da kuma na Conference League.

    Wannan shi ne kofin farko karkashin Enzo Maresca a Chelsea, wadda ta kare a mataki na hudu a teburin Premier League.

  19. Chelsea ta kawo karshen kaka gida da ƙungiyar Sifaniya ke yi a wasan karshe, Real Betis 1-4 Chelsea

    Zidane

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta kawo karshen kaka gida da ƙungiyar Sifaniya ke yi a wasan karshe a gasar zakarun Turai.

    Ƙungiyar Stamford Bridge ta zama ta farko da ta yi nasara a kan ta Sifaniya a wasan karshe bayan shekara 20.

    Ƙungiyoyin Sifaniya sun yi nasarar lashe wasan karshe karo 27 a gasar zakarun Turai har da na kasa da kasa.

    Kidayar ta fara daga ranar da Real Madrid ta doke Bayern Leverkusen 2-1 a karawar karshe a Champions League a Hampden, daga ciki Zinedine Zidane ya ci ƙwallo a karawar.

  20. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu

    Anthony

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta gabatar da tayinta kan Kyeftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes na Portugal mai shekara 30, sannan ta faɗa ma sa yana da wa'adin sa'o'i 72 ya yanke hukunci kan amincewa da yarjejniyar ko akasin haka. (Mail, external)

    Manchester City ta bi sahun masu fafutukar ɗan wasan Lyon mai shekara 21 daga Faransa, Ratan Cherki da ke buga tsakiya. Ana dai alakanta ɗan wasan da Liverpool da Chelsea. (Telegraph - subscription required, external)

    Everton ta bi sahun Leeds United a farautar ɗan wasan nan mai shekara 33 daga Newcastle United da Ingila, Callum Wilson, wanda ba shi da kwantiragi a hannu. (The Sun, external)

    Tottenham ta bada kofar iya sayen ɗan wasan Bayern Munich da Jamus, Leroy Sane mai shekara 29, wanda kwantiraginsa ke karewa a watan gobe.(Sky Sports, external)