window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarin wasannin da zai gudana daga ranar Asabar 24 zuwa 30 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Ahmad Bawage

  1. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo, Daga jaridu

    Kaoru Mitoma

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ta yi imanin dan wasan Brighton da Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 28, zai iya zama madadin Wirtz. (Sky )

    Everton ta tattauna da dan wasan Ipswich da Ingila na 'yan kasa da shekara 21 Liam Delap, mai shekara 22, kan komawa kungiyar a bazara kuma suna sha'awar dan wasan Liverpool da Scotland Ben Doak, mai shekara 19. (Guardian)

    Real Madrid na kallon dan wasan Liverpool da Argentina Alexis Mac Allister a matsayin wanda zai maye gurbin dan kasar Croatia Luka Modric, mai shekara 39, wanda zai bar Bernabeu a bana. (Fichajes)

    RB Leipzig ta tuntubi sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta game da yiwuwar siyar da dan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko mai shekaru 21. (Sky Sports )

  2. Real ta ci wasan da take ban kwana da Ancelotti da Modric, Real Madrid

    Ancelotti Modric

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta doke Real Sociedad 2-0 a wasan mako na 38 a La Liga a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

    Shi ne wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda take ban kwana da Carlo Ancelotti da kuma Luca Modric.

    Bayan da aka kammala wasannin La Liga na kakar nan, Ancelotti zai koma horar da tawagar Brazil, shi kuwa ƙyaftin, Modric, zai bar Real Madrid da zarar an ƙare Club World Cup da za a buga daga watan Yuni a Amurka.

    Real ta kare a mataki na biyu a teburin La Liga da maki 84 da tazarar maki ɗaya tsakani da Barcelona, wadda ta ɗauki La Liga, za ta je Athletic Bilbao ranar Lahadi a wasan karshe.

  3. Djokovic ya zama na uku da ya lashe ATP na 100, Ƙwallon tennis

    Djokovic

    Asalin hoton, EPA

    Novak Djokovic ya zama na uku da ya lashe ATP na 100, sakamakon da ya doke Hubert Hurkacz a wasan karshe a Geneva Open ranar Asabar.

    Mai shekara 38, wanda ya shiga gasar da aka kammala a Switzerland, domin fuskantar French Open kan ganiya, yayi nasarar cin 5-7, 7-6 (7/2), 7-6 (7/2) a wasan da suka yi awa uku da minti biyar.

    Djokovic ya bi sawun Jimmy Connors da Roger Federer cikin waɗanda suka yi wannan ƙwazon a baya.

    Djokovic zai fara buga French Open da zai kara da Mackenzie McDonald ranar ko dai litinin ko kuma Talata.

  4. Real Madrid ta kare kakar nan a mataki na biyu a La Liga, Real Madrid 2-0 Sociedad

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta kare kakar bana ta La Liga a mataki na biyu a kan teburi, bayan da ta doke Real Sociedad 2-0 a wasan mako na 38 ranar Asabar.

    Kylian Mbappe ne ya ci ƙwallayen.

    Da wannan sakamakon Real Madrid wadda ta kammala wasanninta da maki 84 ta ci wasa 26 da canjaras shida da rashin nasara shida.

    Tuni dai Barcelona ta lashe La Liga na bana, kuma na 28 jimilla, wadda take da maki 85, sai a ranar Lahadi za ta buga wasan karshe a gidan Athletic Bilbao.

  5. McTominay ya zama kashin bayan Napoli bayan barin Man United

    Scott McTominay

    Asalin hoton, Getty Images

    Scott McTominay ya zama gwarzo a Napoli da cin ƙwallaye da yawa a bana - sai dai ya faɗi kasa yana sharɓar kuka, sakamakon da ƙungiyar ta lashe Serie A na kakar nan.

    McTominay ya fara ci wa Napoli ƙwallo a minti na 12 da fara tamaula a karawa da Cagliari daga baya tsohon ɗan wasan Manchester United, Romelu Lukaku ya kara na biyu a fafatawar.

    Wannan sakamkon ne ya sa Napoli ta lashe Serie A na bana kuma na huɗu jimilla, Inter Milan ta yi ta biyu.

    Bayan da aka tashi daga karawar, sai a sanar da McTominay mai shekara 28 a matakin fitatcen ɗan wasan Serie A na kakar nan.

  6. Forest ta hana Neville shiga filinta da yin sharhin wasanta da Chelsea ranar Lahadi

    Neville

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai shari da bayanan wasanni a Sky Sports, Gary Neville ya sanar cewar Nottingham Forest ba za ta barshi ya shiga filin wasa na City Ground ba a wasan da za ta kara da Chelsea a Premier League ranar Lahadi.

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da tawagar Ingila ya ce an sanar da shi cewar Forest ta ce ba zai samu shiga wasan da aka tsara zai yi wa Sky Sports sharhi da bayanan karawar ba.

    Tuni mai shekara 50 ya ce ba shi da wani zaɓi, illa ya hakura da zuwa filin a karshen mako.

    Neville ya caccaki shugaban Forest, Evangelos Marinakis a kafarsa ta sada zumunta a X, sakamakon da ya shiga fili ya je ya yi magana da koci, Nuno Espirito Santo bayan tashi 2-2 da Leicester City a watan nan.

  7. Sunderland ta samu tikitin shiga Premier League, Sheff Utd 1-2 Sunderland

    Sunderland

    Asalin hoton, Rex Features

  8. Real Madrid na cin Sociedad a wasan karshe a La Liga, Real Madrid 1 - 0 Sociedad

    Real Madrid tana cin Real Sociedad 1 - 0 a wasan karshe a kakar La Liga ta bana a Santiago Bernabeu.

    Kylian Mbappe ne ya ci ƙwallon.

  9. Man City za ta buga wasa mafi mahimmaci a bana - Guardiola

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City za ta karkare wasan kakar bana a Premier League ranar Lahadi a karawar da Pep Guariola ya ce wasa ne maki mahimmaci a bana da za su kara.

    City za ta je Fulham da sanin cewar watakila ko canjaras ta yi za ta je Champions League a badi.

    City wadda ta lashe Premier League huɗu a jere, sai kuma a bana ta ci karo da koma bayan da ta kai ake rububin neman gurbin babbar gasar tamaula ta zakarun Turai a kakar nan da ita.

    Kociyan ƙungiyar Etihad ya ce idan har suna son zuwa Champions League a baɗi, ya zama wajibi su samu maki a Craven Cottage ranar Lahadi.

    Bayan da City take mataki na ukun teburi da maki 68, Newcastle ce ke biye da ita da maki 66, iri ɗaya da na Chelsea da Aston Villa da kuma Nottingham Forest mai 65.

    City za ta fuskanci Fulham ba tare da Mateo Kovacic, sakamakon jan katin da aka yi masa a wasan Bournemouth ranar Talata.

    John Stone ne kaɗai ke jinya a City, yayin da ake sa ran Rodri ya shiga karawar daga baya.

  10. Espirito na jin daɗi da ake neman gurbin Champions League tare da Forest

    Nuno Espirito Santo

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Nottingham Forest, Nuno Espirito Santo ya ce yana jin daɗi da ake takarar neman gurbin Champions League a baɗi tare da Nottingham Forest.

    Ranar Lahadi a wasannin karshe da za a buga har da fafatawa tsakanin Forest da Chelsea, kuma duk wadda ta yi nasara za ta je buga babbar gasar zakarun Turai, domin wakiltar Ingila a baɗi.

    Chelsea mai maki 66 ta biyar a teburi iri ɗaya da na Aston Villa ta shida da tazarar maki ɗaya tsakani da Forest ta bakwai - Newcastle ce ta huɗun teburi.

    A kakar da ta wuce da ƙyar da gumin goshi Forest ta samu damar ci gaba da zama a Premier League, sai kuma take cikin masu neman Champions League a kakar nan.

  11. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa

    Garnacho

    Asalin hoton, Getty Images

    Wakilan Garnacho na shirin tattaunawa da Manchester United domin tattauna makomar dan wasan na Argentina bayan da aka yi watsi da shi a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da Tottenham ta yi. (Telegraph)

    Ita ma Manchester United da alama za ta siyar da dan wasan tsakiyar Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a wani yunkuri na rage matsin lamba a kungiyar. (Sun)

    Dan wasan tsakiyar Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, zai gwammace ya koma Liverpool maimakon Bayern Munich idan ya bar Bayer Leverkusen a bazara. (Athletic)

  12. Flick zai ci gaba da jiran Araujo ya koma kan ganiya kan baɗi, Barcelona

    Ronald Araujo

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Barcelona, Hansi Flick ya ce yana fatan mai tsaron baya, Ronald Araujo zai koma kan ganiya kan fara kakar baɗi, bayan da ɗan kasar Uruguay ya yi kasa a ƙwazo da fama da jinya, hakan ya sa ake tantama kan makomarsa.

    Mai shekara 26 ya yi fama da jinya kusan rabin kakar nan, wanda yake ta kokarin ganin ya koma kan ganiya, an zargi rashin ƙwazonsa a wasan da Inter Milan ta doke Barcelona 4-3 a Champions League a daf da karshe a Italiya a bana.

    Jita-jita a Sifaniya na cewar Araujo zai bar Barcelona a karshen kakar nan, duk da cewar ya tsawaita kwantiraginsa a 2025 kan zai ci gaba da taka leda a Barcelona kaka shida nan gaba.

    Haka kuma Flick ya bayar da tabbacin cewar Lamine Yamal zai saka hannu kan kunshin yarjejeniyar ci gaba da wasa a Barcelona.

    Flick ya lashe La Liga da Copa del Rey da Spanish La Liga a kakarsa ta farko a Barcelona.

  13. David Moyes yana murna bayan mayar da Everton kan ganiya, Premier League

    David Moyes

    Asalin hoton, Getty Images

    David Moyes ya ce yana cike da murna, bayan da ya mayar da Everton kan ganiya tun bayan da ya koma ƙungiyar da horar da tamaula.

    Everton za ta kare a mataki na 13 a teburin Premier League a kakar nan, duk sakamakon da zai kasance a wasan da za ta je Newcastle United ranar Lahadi a St James Park.

    Moyes ya karɓi ƙungiyar a lokacin da take fuskantar barin Premier League karkashin Sean Dyche, amma yanzu tana sama-saman teburi, sannan a karshen mako Everton ta yi ban kwana da Goodison Park.

    Yayin da Everton za ta buga wasan kare mutunci ranar Lahadi, ita kuwa Newcastle na neman gurbin zuwa Champions League a baɗi.

    Ƙungiyar da Eddie Howe ke jan ragama tana mataki na huɗu a kan teburin Premier League da maki 66, iri ɗaya da na Chelsea ta biyar da Aston Villa ta shida da tazarar maki ɗaya tsakani da Nottingham Forest.

  14. Watakila Ronaldo ya buga Club World Cup na bana, World Club Cup

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino ya ce ana kan tattaunawa kan yadda Cristiano Ronaldo zai buga Club World Cup a bana.

    Ƙungiyar Ronaldo, Al-Nassr ta Saudiyya ta kasa samun gurbin shiga wasannin da aka bunkasa da ƙungiya 32 za su kece raini a Amurka.

    To sai dai Infantino ya ce Ronaldo mai shekara 40, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar nan zai iya buga sabuwar gasar da aka sauya mata fasali.

    Abokin hamayyar Ronaldo wato Lionel Messi zai buga gasar da za a fara daga 14 ga watan Yuni, wanda ke Inter Miami ta Amurka.

    Infantino ya ce ''Watakila Ronaldo ya buga wa wata ƙungiyar da za ta kara a Club World Cup a bana.''

    Ronaldo ya koma Al-Nassr a 2022 bayan barin Manchester United, yayin da kwantiraginsa zai kare a Saudiyya ranar 30 ga watan Yuni.

    Wannan shi ne karon farko da za a buga Club World Cup da ƙungiya 32, maimakon takwas da ake yu a baya can.

    Tuni dai Fifa ta amince a fara cinikin ƴan wasa daga 1 zuwa 10 ga watan Yuni, domin ƙungiyoyi su kara karfi wajen fuskantar Club World Cup.

  15. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu

    Cunha

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu kofar dan wasan Wolves da Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, a bude take, don komawa Manchester United a bazara duk da rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin Turai a kakar wasa mai zuwa. (Sky Sports)

    Golan Aston Villa Emiliano Martinez, mai shekara 32 na shirin barin kungiyar, inda kungiyoyin Saudiyya da Manchester United ke zawarcin dan wasan na Argentina. (Teamtalk)

    Aston Villa, da West Ham da Leeds suna zawarcin dan wasan tsakiya na Southampton da Portugal na 'yan kasa da shekara 21 Matheus Fernandes, mai shekara 20. (Football Insider).

  16. Potter na fatan West Ham za ta doke Ipswich Town, Premier League

    West Ham

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan West Ham United, Graham Potter na fatan ƴan wasansa za su doke Ipswich Town ranar Lahadi a wasan karshe a Premier League.

    West Ham tana saman Tottenham, wadda ta lashe Europa League da kuma Manchester United a teburin Premier League na kakar nan.

    Idan har West Ham ta haɗa maki uku ranar Lahadi, kenan za ta hau kan Wolverhampton zuwa mataki na 14 - kuma za ta samu karin ladan da zai kai £3million.

  17. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu

    Wirtz

    Asalin hoton, Getty Images

    Al Hilal na shirin bayar da fan miliyan 100 don daukar Bruno Fernandes daga Manchester United, Florian Wirtz ya fi son ya koma Liverpool a kan Bayern Munich, yayin da Emiliano Martinez ke shirin barin Aston Villa.

    Za a ba Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes wa'adin mako mai zuwa don yanke shawarar ko yana son barin kulob din, inda Al Hilal ke tayin kusan fan miliyan 100 kan dan wasan na Portugal, mai shekara 30, wanda zai rika samun kusan fan miliyan 65 a shekara a Saudiyya. (Mail)

    Bayern Munich na iya sake yin wani sabon yunkuri don daukar Fernandes din duk da cewa kudin da United ke so sun mata yawa. (Teamtalk)

    Dan wasan gefe na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, na iya barin Manchester United a wannan bazarar bayan da ya ji takaicin rawar da yake takawa a karkashin kocin kungiyar Ruben Amorim. (ESPN)

  18. Tottenham za ta taka rawar gani a baɗi - Postecoglou, Premier LEAGUE

    Postecoglou

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai horar da tamaula, Ange Postecoglou ya yi wa magoya bayan Tottenham alkawarin cewar zai mayar da ita kan ganiya, bayan da ya lashe Europa League, daman ya ce a kaka ta biyu ya kan lashe kofi.

    Dubban magoya baya sun yi wa Tottenham tarbar girma ranar Juma'a a wata buɗaɗiyar mota a lokacin bikin ɗaukar kofi a karon farko a tarihi tun bayan shekara 17, sakamakon cin Manchester United 1-0 ranar Laraba a birnin Bilbao a Sifaniya.

    To sai dai Tottenham tana ta 17 a kasan teburin Premier League, ɗaya daga rashin ƙwazo mafi muni a tarihin ƙungiyar.

    Ranar Lahadi Tottenham za ta buga wasan karshe mako na 38 da Brighton & Hove Albion.

  19. Ƴan wasan Real Madrid da za su kara da Sociedad a La Liga, Gasar La Liga mako na 38

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta bayyana ƴan wasan da za su fuskanci Real Soceidad a wasan mako na 38 a La Liga ranar Asabar.

    Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da Barcelona ta lashe kofin, ita kuwa Sociedad tana ta t1 a teburin da maki 46.

    Wasan da aka buga tsakanin Real Madrid da Real Sociedad a bana:

    2024/2025

    Copa del Rey ranar Talata 1 ga watan Afirilu

    • Real Madrid 4-4 Sociedad

    Copa del Rey ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu

    • Sociedad 0-1 Real Madrid

    La Liga ranar 14 ga watan Satumba

    • Sociedad 0-2 Real Madrid

    Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana ƴan ƙwallon da za su buga wa Real karawar a Santiago Bernabeu.Ƴan wasa 11 na Real Madrid:13. Lunin17. Lucas V.14. Tchouameni35. Asencio20. Fran García10. Modrić8. Valverde19. Ceballos15. Arda Güler9. Mbappé21. BrahimƳan zaman benci:1. Courtois26. Fran González7. Vini Jr.18. Vallejo29. Youssef30. Gonzalo31. Jacobo36. Chema.

  20. Simeone bai ji daɗi ba Atletico za ta kare kakar nan ba kofi, Atletico Madrid

    Diego Siemon

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai horar da tamaula, Diego Simeone ya ce bai ji daɗi ba Atletico Madrid ta kare kakar nan ba tare da ɗaukar kofi koda ɗaya ba, amma yana sa rai a Club World Cup.

    Atletico, wadda take ta ukun teburi da tazarar maki 12 tsakani da Barcelona, wadda ta lashe La Liga na bana na 28 jimilla, ta kasa cin Copa del Rey, inda Barca ta fitar da ita, sannan Real Madrid ta yi waje da ita a Champions League a kakar nan.

    A watan Yuni za a fara Club World Cup a Amurka a kare a cikin watan Yuli.

    Simeone, wanda ya lashe La Liga biyu da Europa League a Atletico ya ce ya mayar da hankali kan yadda zai doke Girona, domin ya tabbatar da ya kare a mataki na uku a bana.