window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Mutum sama da miliyan daya sun kamu da coronavirus a duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Awwal Ahmad Janyau, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen wannan shiri da ke kawo muku bayanai kai tsaye dangane da halin da duniya ke ciki kan annobar coronavirus. Da fatan za ku kasance da mu gobe Juma'a da safe. Allah ya tashe mu lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumi, Masu dauke da coronavirus a duniya sun zarce miliyan

    Mutanen da ke dauke da coronavirus a duniya yanzu sun zarce miliyan daya, kamar yadda alkaluman Jami'ar Johns Hopkins suka nuna.

    Sama da mutum 51,000 cutar ta kashe a duniya, yayin da sama da mutum 208,000 suka warke, a cewar alkaluman jami'ar da ke Amurka.

    Amurka ce ta fi yawan masu dauke da cutar, yayin da cutar ta fi yin kisa a Italiya.

    Cutar ta fara bulla ne a China watanni uku da suka gabata.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Johns Hopkins

  3. Coronavirus: BUK ta fara aikin kera na'urar numfashi ta ventilators

    Tsangayar fasaha a jami’ar Bayero da ke Kano ta ce tana aikin samar da na’urorin taimaka wa numfashi da ake kira ventilators domin amfanin cibiyoyin da aka yi tanadi idan an samu wadanda suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus a Kano.

    Wasu kwararru ne suka hadu a tsangayar Fasahar da ke Jami’ar Bayero suka fara aikin kera na’ura daya a matsayin gwaji kafin samar da na’urorin da za a yi amfani da su domin yaki da coronavirus a Najeriya.

    Shugaban tsangayar fasaha a Jami’ar Bayero Farfesa Salisu Danazumi ya shaida wa BBC cewa sun yi nisa da aikin.

    “Sun fara aiki kuma sun cimma kusan kashi 50 na samar da wannan na’ura,” inji shi.

    Ya kuma ce an samu samfurin na’urar ne daga irin wadda ake amfani da ita a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano kuma a cewarsa, “mako daya muka ba kwararrun domin kammala aikin samar da na’urar.”

  4. Coronavirus: Za a fara gurfanar da masu shiga Kano a gaban kuliya

    Ganduje

    Hukumar da ke kula da tituna ta Kano, KAROTA, ta ce za ta fara gurfanar da wadanda take zargi da karya dokar hana shiga da fita daga jihar da gwamnatin ta Kano ta kafa, a gaban kuliya bisa laifin yunkurin kisan kai.

    Shugaban hukumar da ke kula da tituna na jihar ta KAROTA, Baffa Babba Dan'agundi ya shaida wa BBC cewar sun gano karin hanyoyi 17 da direbobi kan bi wajen shiga jihar.

    Ya kara da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta dukkan wanda aka kama yana karya dokar hana shiga jihar.

  5. Labarai da dumi-dumi, An samu karin mutum 10 da suka kamu da coronavirus a Najeriya

    Hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar da samun karin wasu sabin mutum 10 da suka kamu da cutar coronavirus.

    NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce daga cikin mutanen 10, 7 sun fito daga Legas inda 3 suke daga birnin Abuja.

    Ya zuwa karfe 8:00 na daren Alhamis, jumullar mutanen da ke dauke da cutar a kasar sun zama 184, in ji NCDC.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Coronavirus: An sa dokar hana fita ta awa 24 a Makka da Madina

    Makka

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Saudiyya ta sanar da sanya dokar hana fita na awa 24 a birnin Makkah da Madina da za ta fara aiki yau Alhamis.

    Wannan dokar dai kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta rawaito kamfanin dillancin labarai na kasar, har sai baba ta gani.

    Dokar ta tanadi cewa mutane za su fita waje ne kawai bisa biyan bukatar neman abinci ko asibiti kuma za a yi hakan ne tsakanin karfe 6 na safe zuwa 3 na ranar kowace ranar.

    Har wa yau, dokar ta hana shiga ko fita daga biranen amma ta kebance jami'an tsaro da ma'aikatan lafiya da 'yan jarida.

    Wannan doka dai wani mataki ne da gwamnatin kasar Saudiyya ta dauka da manufar shawo kan annobar coronavirus a biranen guda biyu.

    Ma'aikatar lafiyar kasar dai ta ce kawo yanzu kasar na da mutum 1,885 da ke dauke da cutar coronavirus, inda mutum 21 suka rasu sannan 328 suka warke.

  7. Coronavirus: Karin mutum 11 sun warke a Legas

    Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa an sallami mutum 11 daga cibiyar killace masu cutar coronavirus da ke Yaba a birnin.

    Gwamnan wanda ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter ya ce an yi wa mutanen gwaji inda gwajin ya nuna cutar ta bar su.

    Sai dai kuma hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar, NCDC ba ta wallafa batun warkewar ba.

    Hukumar ta NCDC dai ta sallami mutum 9 bayan sun warke daga cutar.

    Yanzu kenan za a iya cewa bisa sanarwar Gwamnan na jihar Legas, akwai mutum 20 da suka warke da cutar a Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Coronavirus: 'Yan kasuwa a Legas sun fara fita kasuwa

    Legas

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu daga cikin ‘yan kasuwa a birnin Legas sun bude kasuwanninsu, tun bayan da gwamnatin tarayya ta umarci a bude kasuwanni a jihar Legas da Abuja, babban birnin tarayyar kasar

    Sai dai wasu daga mazauna jihar Legas sun nuna fargabar cewa bayar da umarnin bude kasuwannin daga karfe goma na safe zuwa karfe biyu na rana a kowacce rana zata iya zama kafar da za a baza cutar Coronavirus cikin al’umma.

  9. Coronavirus: 'Yan Najeriya sun sako gwamnatin kasar a gaba

    Ma'aikatar kudi ta Najeriya ta yi watsi da wani roko da aka wallafa a shafinta na Twitter inda aka nemi fitaccen dan kasuwar nan dan Amurka, Elon Musk da ya taimaka wa kasar da na'urorin shakar iska na ventilators.

    Mai magana da yawun ma'aikatar kudin kasar, Yunusa Tanko Abdullahi ya ce wani wanda ba a amince ya yi amfani da shafin Twitter na ma'aikatar ba ne ya wallafa wannan sako a shafin.

    'Yan Najeriya dai sun sako gwamnatin kasar a gaba a shafukan sada zumunta bayan Ma'aikatar Kudi ta roki wani dan kasuwar Amurka tallafin na'urar numfashi ta ventilator don yakar coronavirus.

    Shafin Tiwtter na Ma'aikatar Kudi ta Najeriya ne ya nemi tallafin daga Elon Musk, shahararren kasuwar nan na Amurka bayan ya bayyana cewa kamfaninsa na Tesla yana da na'urar da zai taimaka wa wasu kasashe don dakile coronavirus.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Sai ma'akatar kudi da kasafin Kudi ta Najeriya ta mayar da martani cewa: "Zuwa ga Elon Musk, Najeriya na bukatar na'urar numfashi 100 zuwa 500 domin yaki da Covid-19 da ke kara kamari a Najeriya."

    Sai dai tuni suka goge wannan sakon daga shafin nasu, amma sun yi shuka a idon makwarwa, domin kuwa BBC ta gan shi.

    Sakon Twitter

    Yayin da wasu ke ganin babu laifi gwamnati ta nemi tallafi, wasu na ganin hakan bai dace ba.

    Wani ya ce: "Kasar da ta ware naira biliyan 37 domin gyaran majalisar dokkoki bai kamata ta nemi tallafin na'urar numfashi daga Elon Musk ba.

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Wani ma ya ce: "

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  10. Coronavirus: Aradu ta kashe mutum 20 a Congo

    Lighting

    Wasu mutum 20 sun mutu sakamakon wata aradu da ta fada kan layin wutar lantarki a Congo-Brazzaville.

    Al'amarin dai ya faru ne a ranar farko da fara dokar kulle a babban birnin kasar, Brazzaville domin dakile yaduwar cutar.

    Kawo yanzu dai mutum 22 ne cutar ta coronavirus ta kama a kasar ta Congo-Brazzaville, inda kuma mutum biyu suka mutu.

    Wadanda suka shaida faruwar al'amarin sun ce wayar wutar lantarkin ce ta fada kan wasu gidaje inda ta rinka jan jama'a.

    An dai kwashe awowi ana zabga ruwa kamar da bakin kwarya.

  11. Coronavirus: Zambia ta samu mutum na farko da ya cutar ta kashe

    Zambia

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasar Zambia ta samu mutum na farko wanda ya mutu sakamakon cutar coronavirus.

    Ministan Lafiyar kasar, Chitalu Chilufya ya tabbatar wa da manema labarai cewa da safiyar Alhamis ne mutumin ya rasu.

    Ya ce a awowi uku da suka gabata kasar ta kara samun masu dauke da cutar ta coronavirus, inda yanzu haka jumullar masu dauke da cutar suka kai 39.

  12. Coronavirus: Fiye da mutum 10,000 sun mutu a Sipaniya

    Spain

    Asalin hoton, EPA

    Sipaniya na ci gaba da rasa 'yan kasar sakamakon annobar coronavirus, inda yanzu haka mutum fiye da 1000 suka mutu.

    Har wa yau, Sipaniya wadda ita ce kasa ta biyu a duniya da cutar tafi yi wa barna bayan Italy, ta rasa ayyukan yi kimanin 900,000.

    Ita ma Amurka ta ce ta rasa ayyukan yi milyan 6.6.

    Rashin ayyukan yi dai alamu ne na irin illar da cutar coronavirus ta yi wa tattalin arzikin kasashen duniya.

  13. Buhari ya gana da wasu ministoci kan coronavirus

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, @MBuhari

    Shugaba Mujhhammadu Buhari na Najeriya ya gana da Ministar Kudi da Ministan Man Fetur da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da shugaban kamfanin mai na NNPC.

    Buhari ya ce ministocin sun bayyana masa halin da ake ciki a ci gaba da yaki da yaduwar coronavirus.

    A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta fara raba wa marasa karfi tallafin naira 20,000 domin rage musu radadin halin da matakin yaki da coronavirus ka iya jefa su a ciki.

    Mutum 174 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya zuwa yanzu, a cewar hukumomi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Coronavirus ta kashe mutum fiye da 5,000 a Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkaluman mutanen da ke mutuwa sakamakon coronavirus a Amurka sun karu zuwa fiye da mutum 5,000, inda kuma alkaluman kasashen duniya suka kusa kai wa milyan daya.

    An samu mutuwar mutum 884 a Amurka a cikin awowi 24, in ji jami'ar John Hopkins University.

    Yanzu haka fiye da mutum 216,000 sun kamu a Amurka.

  15. Covid-19: 'Yan Masar na so a mayar da gidan Shugaba Sisi wurin killace mutane

    'Yan kasar Masar sun yi tururuwa a shafin Twitter suna kira da a mayar da gidan shugaban kasar Abdul Fattah al-Sisi wurin killace masu dauke da coronavirus.

    Kiraye-kirayen na zuwa ne a lokacin da ake tababar ko wane ne ya kamata ya dauki nauyin wadanda ake killacewar idan sun dawo daga kasashen ketare.

    An samu tayar da jijiyoyin wuya ne bayan da aka kulle wasu kwararru a wani babban otal kusa da filin jirgin sama na Alkahira sannan aka ce musu su za su dauki nauyin kansu.

    A ranar Laraba ne kuma Shugaba Sisi ya sauya shawara, inda ya sanar da wani asusu na musamman da zai kula da wannan bangare.

  16. Coronavirus: An umarci jami’an tsaro su bindige masu kunnen-kashi a Philippines

    Shugaba Duterte

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Philippines, Rodrigo Duterte, ya yi gargadin cewa za a iya harbe mutane idan suka tayar da yamutsi saboda dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya saboda coronavirus.

    A jawabin da ya yi a gidan talbijin, Shugaba Duterte ya ce 'yan sanda da sojoji suna da ikon harbi idan suka ga rayuwarsu ta fada cikin hatsari.

    Ya yi gargadin ne bayan 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar neman tallafin abinci a birnin Manila.

    Da ma dai ana zargin Shugaba Duterte da aiwatar da dokar kashe mutanen da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ba tare da an yi musu shari'a ba.

    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce bai kamata a rika yin amfani da karfin da ya wuce kima ba wajen tursasa wa mutane bin dokar hana fita.

  17. Karin mutum biyar sun kamu da coronavirus a Senegal

    Kasar Senegal ta tabbatar da karin mutum biyar da suka harbu da cutar coronavirus, yayin da ta ce mutum 10 sun warke.

    Jumullar adadin wadanda suka harbu a kasar ya zama 195, sannan 55 suka warke da kuma mutum daya da ya mutu.

    Daya daga cikin wadanda suka kamu an kai shi Faransa. Mutum 135 ne ke dauke da cutar a yanzu.

    Coronavirus a Senegal

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Abuja: Jami'an tsaro sun kasa sun tsare a babbar hanyar Kubwa

    Abuja

    Jami'an tsaro da suka hada da na 'yan sanda da na kiyaye hadura sun rufe babbar hanyar Kubwa ta shiga garin Abuja.

    Kamar yadda aka sani dokar hana shige da fice ta fara aiki a birnin Abuja tun daga daren ranar Litinin.

    Abuja

    Zuwa yanzu birnin Abuja yana da mutum 35 da suka kamu da cutar coronavirus daga cikin 174 da suka kamu a Najeriya baki daya.

    Abuja

    Sai kuma Jihar Legas da ke da mafi yawan masu cutar - 91, wadda ita ma aka saka dokar hana fita.

  19. An rufe asibiti a Afirka ta Kudu bayan ma'aikaciya ta kamu da coronavirus

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, Reuters

    An rufe wani karamin asibiti a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu bayan wata ma'aikaciyar jinya ta kamu da coronavirus mai haddasa cutar Covid-19.

    An tunanin ma'aikaciyar ta harbu ne bayan ta je ibada wani coci a wani gari a watan da ya gabata.

    Duk wadanda suka yi aiki tare da ita an kilace su, yayin tuni wasu daga cikinsu suka fara nuna alamun cutar kuma suna jiran sakamakon gwajin da suka yi.

    Fiye da mtum 60 da suka halarci zaman cocin tare da ita sun kamu da cutar.

    Wani fasto dattijo ya rasu sakamakon coronavirus bayan ya sha fama da wasu cutukan daban.

  20. Coronavirus: Ana bincike kan mutum 25 a Kano

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Ibrahim Tsanyawa
    Bayanan hoto, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Ibrahim Tsanyawa kenan yayin taron manema labarai a yau Alhamis

    Gwamnatin Jihar kano ta ce tana gudanar da bincike kan mutum 25 da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a jihar.

    A wani taron manema labarai a ranar Alhamis a Kano, Kwamishinan Lafiyar Jihar, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce tuni gwaji ya nuna 22 daga cikinsu ba sa dauke da cutar yayin da ake jiran sakamakon gwaji na mutum uku.

    Ya kara da cewa mafi yawan rahotannin da suke samu daga mutane, jita-jita ce, sannan ya ce sun samar da wasu lambobi na kira domin bayar da rahotannin wadanda ake tunanin sun kamu da coronavirus.

    Lambobin kiran gaggawa a Kano kan Coronavirus
    Bayanan hoto, Sababbin lambobin kiran gaggawa don bayar da rahoton mai dauke da coronavirus a Kano

    Kazalika Aminu Ibrahim ya ce Alhaji Aliko Dangote zai gina cibiyar kebe masu coronavirus mai gado 500, sabanin 600 da wasu kafofin yada labarai suka rawaito.

    Kwamishinan ya kuma jaddada kokarin gwamnatin Kano na ci gaba da sanya ido kan dokar hana shiga jihar da suka kafa tun a makon da ya gabata.

    Makociyarta wato Jihar Kaduna, dokar hana fita baki daya aka saka duk da cewa gwamnati ta sassauta a ranar Laraba.