An fara zaman gida a Eritrea saboda coronavirus
Kasar Eritrea ta saka dokar zaman gida na tsawon kwana 21 domin dakile yaduwar coronavirus.
Sanarwar ta zo ne bayan ministan lafiya ya bayar da rahoton karin mutum uku da suka kamu da cutar, abin da ya kawo adadin wadanda suka kamu a kasar zuwa 18.
Daya daga cikinsu yarinya ce 'yar shekara 13, wadda ta harbu da cutar daga mahaifiyarta wadda ta koma daga kasar waje.
Su ma sauran biyun sun koma kasar ne kafin a haramta saukar jiragen haya a kasar, a cewar ma'aikatar lafiya.
Yayin dokar, dukkanin 'yan kasar wadda ke bin tsarin jam'iyyar siyasa guda daya sannan take da nuna karfin soja, za su kasance a gida - ma'aikata da 'yan kasuwa.
Mutum daya daga kowane gida yana da damar fita domin sayen kayan abinci da rana a shagunan cefane, wadanda za su kasance a bude.
Su ma kantinan sayar da magani da bankuna za su ci gaba da kasancewa a bude, amma an rufe kasuwanni na mako-mako da sauran wuraren kasuwanci.
Sai dai manoma da ke zaune a yankunan karkara ba sa cikin wannan doka sakamakon abinci da suke samarwa.
Ayyukan gine-gine ma za su ci gaba da gudana, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images