window.__reverb = {}; window.__reverb.__reverbLoadedPromise = new Promise((resolve, reject) => { window.__reverb.__resolveReverbLoaded = resolve; window.__reverb.__rejectReverbLoaded = reject; }); window.__reverb.__reverbTimeout = setTimeout(() => { window.__reverb.__rejectReverbLoaded(); }, 5000);

Mutum sama da miliyan daya sun kamu da coronavirus a duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Awwal Ahmad Janyau, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, Fiye da mutum 3,000 sun mutu a Iran

    Yawan wadanda suka mutu a Iran sakamakon annobar coronavirus ya zarce 3,000, bayan mutum 138 sun mutu a cikin awa 24 da suka gabata.

    Karin mutum 2,987 ne suka kamu da cutar a cikin sa'a 24 din, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito, abin da ya kai jumullar adadin zuwa 47,593 a kasar.

    Wannan yana zuwa ne yayin da Iran, wadda ke cikin kasashen da cutar ta fi yi wa illa, ta yi kira ga jama'arta su zauna a gida a ranar karshe ta bikin sabuwar shekarar yankin Fasha da ake kira Nowruz.

    Akasarin Iraniyawa sun yi bikin ne ta hanyar yawon shakatawa a wurare daban-daban.

    Sai dai yanzu an bayar da umarnin kulle dukkanin wuraren shakatawar sannan aka kai 'yan sanda domin hana mutane shiga cikinsu.

  2. 'Coronavirus ce kalubale ma fi girma tun bayan yakin duniya na II'

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargadin cewa annobar coronavirus ce kalubale ma fi girma da duniya ta taba fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

    Mista Guterres ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da wani rahoto kan yadda annobar za ta shafi tattalin arzikin duniya, inda ya ce annnobar za ta iya haddasa rikicin tattalin arziki "wanda ba a taba ganin irinsa ba a baya-bayan nan".

    Wannan gargadi nasa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashe kan yadda matakan da ake dauka na yaki da coronavirus za su shafi tattalin arziki.

    "Covid-19 ce ma fi girman kalubale da muka fuskanta tun bayan kafa Majalisar Dinkin Duniya," in ji Guterres.

    Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi hasashen cewa za a rasa aikin yi kusan miliyan 25 a fadin duniya sakamakon annobar. Sannan ya yi hasashen cewa kudaden zuba jari ma za su ragu da kusan kashi 40 cikin 100.

    Adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu a fadin duniya ya kai kusan 42,000 sannan kusan 860,000 suka kamu.

    Fiye da mutum 4,000 ne suka mutu a Amurka sakamakon cutar - sama da na kasar China, inda cutar ta fara bulla a karshen shekarar bara.

    Jami'ar Johns Hopkins ta ce mutum 865 sun mutu a cikin awa 24 da suka gabata a Amurka, sannan mutum 189,000 ne suka kamu da cutar a kasar.

  3. Labarai da dumi-dumi, Mutane da dama sun mutu a cikin awa 24 a Spain

    Kasar Spain ta bayar da rahoton mutuwar mutum 864 a cikin awa 24, adadi mafi yawa na rana guda kenan da aka taba samu tun bayan bullar annobar cornavirus a kasar.

    Jumullar mutum 9,053 ne suka mutu a kasar, sai kuma mutum 102,136 da suka kamu da ita.

    • Covid-19: Mutum na farko ya mutu a Myanmar

      A karon farko wani mutum ya mutu sakamakon kamuwa da coronavirus a Myanmar, a yayin da wadanda suka kamu da cutar a kasar ke ci gaba da hauhawa.

      Da ma dai mutumin mai shekara 69 yana fama da cutar daji, kuma ya mutu ne a babban birnin kasar Yangon ranar Talata.

      Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce mutumin ya je Australia domin neman magani kuma ya yada zango a Singapore a kan hanyarsa ta komawa gida.

      Lamarin na faruwa ne a yayin da Myanmar ta kwashe makonni da dama tana musanta cewa akwai masu dauke da cutar a kasar - ko da yake masana sun yi shakkar ikirarin nata.

      Wani mai maana da yawun gwamnatin kasar ya yi ikirarin cewa "yanayin rayuwar da mutane ke gudanarwa da irin abincin da suke ci" sun kare su daga kamuwa daga cutar.

      Yanzu haka akwai mutum 14 da ke dauke da coronavirus a Myanmar.

      Yanzu haka akwai mutum 14 da ke dauke da coronavirus a Myanmar.

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Yanzu haka akwai mutum 14 da ke dauke da coronavirus a Myanmar
    • Amurkawa za su sake fadawa mawuyacin hali kan coronavirus - Trump

      Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci 'yan kasar su shiryawa fadawa cikin "mawuyacin hali" a makonnin da ke tafe.

      An yi hasashen cewa adadin wadanda za su kamu da coronavirus a kasar zai zarta 250,000 a makonni da watannin da ke tafe.

      "Mako biyu masu zuwa za su kasance mayuwacin hali," in ji Mr Trump a jawabin da ya yi a White House, yana mai bayyana coronavirus a matsayin "annoba".

      "Ina son ko wanne Ba'amurke ya shirya fuskantar mawuyacin hali nan gaba."

      Trump

      Asalin hoton, Getty Images

    • Coronavirus ta bulla a Burundi da Sierra Leone

      Burundi da Sierra Leone, wadanda ke cikin kasashe kadan a Afirka da basu samu bullar coronavirus ba, yanzu sun bayyana cewa annobar ta bulla a cikinsu.

      Da ma dai an yi ta shakkar ikirarin da Burundi ta yi cewa ba ta da mai dauke da coronavirus. Kakakin shugaban kasar ya ce ba a samu bullar annobar ba ne saboda kasa ce da ta "take sanya Allah a gaba kafin komai".

      Ministan lafiya Thadée Ndikumana ya sanar ranar Talata cewa biyu daga cikin 'yan kasar sun kamu da coronavirus bayan sun dawo daga balaguron da suka yi zuwa Rwanda da Dubai.

      A Sierra Leone, an gano cewa wani mutum mai shekara 37 wanda ya koma kasar daga Faransa ya kamu da Covid-19 bayan ya kammala wa'adin da aka ba shi na killace kansa.

      Gwamnati ta ce ba za ta rufe kasar baki daya ba amma ta ayyana dokar ta-bacin kan harkokin lafiya ta shekara daya, sannan ta dakatar da sauka da tashin jiragen sama, kuma ta rufe makarantu.

      A farkon watan jiya, an umarnin duk mutanen da za su tsallaka iyaka zuwa Burundi su wanke hannunsu saboda fargabar coronavirus

      Asalin hoton, AFP

      Bayanan hoto, A farkon watan jiya, an umarnin duk mutanen da za su tsallaka iyaka zuwa Burundi su wanke hannunsu saboda fargabar coronavirus
    • Covid-19 ta kashe tsohon shugaban Olympique de Marseille

      Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar Faransa ta Olympique de Marseille , Pape Diouf, ya mutu bayan ya kamu da coronavirus - inda ya kasance mutum na farko da ya rasu a Senegal sanadin wannan annoba.

      An kwantar da tsohon shugaban mai shekara 68 ne a asibitin Fann Hospital da ke Dakar, babban birnin kasar.

      Mr Diouf, dan Senegal wanda ya koma Marseille lokacin yana matashi, ya zama shugaban kungiyar daga 2005 zuwa 2009, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

      Sakon da kungiyar ta Ligue 1 ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce : "Olympique de Marseille ta samu labari cike da bakin ciki na rasuwar Pape Diouf. Pape zai ci gaba da kasancewa a zukatan 'yan kungiyar Marseillais a matsayinsa na daya daga cikin wadanda suka kafa tarihinta. Muna mika ta'aziyyarmu ga iyalai da masoyansa."

      Pape Diouf

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Pape Diouf ya zama shugaban kungiyar daga 2005 zuwa 2009
      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Fiye da mutum 178,000 sun warke daga coronavirus

      Bayanan da ke fitowa daga Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, wacce ke bibiyar halin da ake ciki game da coronavirus, sun nuna cewa akalla mutum 178,378 sun warke daga cutar ya zuwa safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.

      A cewar Jami'ar, sama da mutum 860,000 ne suka kamu da cutar a fadin duniya, yayin da akalla mutum 42,354 suka mutu.

      Kasashe goman da suka fi fama da annobar su ne:

      Amurka - 189,633

      Italiya - 105,792

      Spaniya - 95,923

      China - 82,301

      Jamus - 71,808

      Faransa - 52,836

      Iran - 44,605

      Birtaniya - 25,481

      Switzerland - 16,605

      Turkiyya - 13,531

    • Barkanmu da warhaka,

      Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da wannan safiya. Da fatan za ku kasance tare da mu domin sanin halin da ake ciki dangane da coronavirus, cutar da ta addabi kasashen duniya.

      Baya ga labaran wannan annoba, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

      Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.

    • Coronavirus: Babu tabbas kan gudanar da aikin hajji a bana

      Kaabah

      Asalin hoton, Getty Images

      Ma'aikatar aikin hajji da Umra ta kasar saudiyya ta nemi kasashen duniya da su dakata da karbar kudaden jama'a domin zuwa aikin hajjin bana, har zuwa lokacin da al'amura suka daidaita.

      A wani sako da ministan ma’aikatar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ma’aikatar ta ce yanke hukuncin aikin hajji yanzu zai zamo aikin gaggawa, inda ya nemi da a kara tsahirtawa a ga abin da zai je ya zo dangane da cutar coronavirus.

      ta kuma kara da cewa Saudiyya ta mayar wa da duk mutumin da ya biya kudin bizar Umrar bana kudadensu.

      Ma’aikatar aikin hajjin ta kara da cewa mutanen da suka makale a Makka sakamakon dokar kunle a kasashensu za a tsugunar da su a otal na alfarma da kulawa ta musamman har zuwa lokacin da kasashensu za su bude kofa.

      Sai dai ma’aikatar ta fadi dalilin barin mutane kalilan su yi dawafi, inda ya ce sun dauki hukuncin ne saboda yin ragakafi.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Coronavirus: Dan shekara 13 ya rasu a London

      Wani yaro mai shekara 13 wanda ya kamu da cutar coronavirus yake kuma karbar magani a asibitin King's College Hospital Trust a London ya rasu.

      Rasuwar yaron dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar mace-macen masu dauke da cutar ta coronavirus.

      A yanzu haka alkaluman mutanen da suka mutu a Burtaniya sakamakon cutar sun kai mutum 1,789.

    • Coronavirus ka iya yaduwa a gidajen yarin Najeriya - Amnesty

      Amnesty International

      Asalin hoton, Getty Images

      Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty International ta bukaci mahukunta da su dinga la`akari da gidajen yari da sauran sansanonin marasa galihu wajen daukar matakan da za su kare su daga harbuwa da cutar coronavirus.

      Mafi yawan gidajen yarin Najeriyar dai na fama da cinkoson jama`a.

      Ko da a yau Talata din nan sai da wasu fursunoni suka yi bore a Kaduna sakamakon cinkoson da suke fama da shi da kuma fargabar barkewar cutar coronavirus.

      Sai dai gwamnatin tarayya a nata bangaren, ta kafa wani kwamiti da nufin rage cinkoson a gidajen yarin,

      Kungiyar ta Amnesty International din ta bayyana cewa akwai rukunonin al`umma, wadanda ba a kodayaushe hankali kan yi saurin zuwa gare su ba, idan mahukunta suka tashi shiryawa ko aiwatar da wadansu manufofinsu.

      Amnesty ta kuma kara da cewa fursunoni da sansanonin masu gudun hijira na cikin irin wadannan rukunonin jama`a wadanda kuma idan ba a kiyaye ba, cutar coronavirus za ta yi saurin illata su idan ta bulla a tsakaninsu

    • Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: An kara samun mutum 4 a Najeriya

      Hukumar yaki da cuttuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an kara samun mutum hudu da ke dauke da coronavirus a kasar.

      Mutum uku a Abuja babban birnin Tarayya da kuma karin mutum daya a Legas.

      Yanzu jimillar mutum 139 ke dauke da cutar a Najeriya, yayin da aka sallami mutum Tara.

      Mutum biyu kuma suka mutu kawo yanzu

      Hukumar NCDC

      Asalin hoton, @NCDCgov

    • Abubuwan da ke faruwa a Afirka

      ·Habasha ta sanar da dage babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa a watan Agusta saboda cutar coronavirus

      ·Tsohon shugaban Congo-Brazzaville Jacques Joaquim Yhombi Opango ya rasu a Paris inda ake tunanin coronavirus ce ta kashe shi. A 1979 ne aka hambarar da gwamnatinsa. Iyalinsa sun ce ya dade yana rashin lafiya kafin kamuwa da cutar.

      ·Gwamnatin Somalia ta sanar da rufe makarantun Islamiya da na Allo domin dakile yaduwar cutar coronavirus inda gwamnatin ta bukaci mutane su kasance a gida tare da kauracewa sallar jam’I a masallatai tsawon mako biyu.

      ·Uganda ta takaita fita na tsawon mako biyu wanda ya kunshi hana hawan motocin hawa a kasar sai idan mutum ya samu izini daga gwamnati.

      ·Kasashen Botswana da Mozambique sun ayyana dokar ta-baci domin dakile yaduwar cutar coronavirus, yayin da kuma Guinea ta kafa dokar hana fita.

      ·Ana ci gaba da rikici da barin wuta a Tripoli babban birnin kasar Libya duk da kiran a tsagaita buda wuta saboda barazanar bazuwar coronavirus.

      ·Afirka ta kudu ta kaddamar da gagarumin shirin yi wa jama’a gwajin cutar coronavirus, inda ma’aikatan lafiya za su fara kai ziyara gidajen mutane domin gwajin.

      Yadda jami'an tsaro ke tabbatar da dokar hana fitar dare a Kenya

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Yadda jami'an tsaro ke tabbatar da dokar hana fitar dare a Kenya
    • Yadda Shugaban Najeriya ke wanke hannu don gudun coronavirus

      .

      Asalin hoton, @BashirAhmaad

      .

      Asalin hoton, @BashirAhmaad

    • Yadda gwamnatin Legas ke raba wa mutane kayan abinci

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

      Gwamnatin Legas na raba wa mutane kayan abinci

      Asalin hoton, @followlasg

    • Yadda dokar hana fita ta yi tasiri a Ghana

      Titunan birnin Accra
      Titunan birnin Accra
      Titunan birnin Accra
    • Labarai da dumi-dumi, An samu mutum na uku mai dauke da coronavirus a Bauchi

      An samu mutum na uku mai dauke da cutar coronavirus a jihar Bauchi.

      Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati na jihar, Ladan Salihu ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

      Ladan ya bayyana cewa an yi wa mutum 99 gwajin cutar a jihar ta Bauchi, amma mutum uku ne ke dauke da ita a halin yanzu.

      Gwamnan jihar Bala Mohammed na daya daga cikin masu dauke da cutar a jihar.

    • Gwamnatin Nijar na son 'yan kasuwa su rage farashin kayayyaki

      Gwamnatin Nijar ta tattauna da ‘yan kasuwa domin diba yiyuwar rage farashin kayayyaki saboda cutar coronavirus inda tuni farashin wasu kayayyakin ya tashi.

      Wakiliyar BBC a Nijar Tchima Illa Issoufou ta ce ‘Yan kasuwar ne ke da ikon rage farashin inda tun a 1992 gwamnati ta cire hannunta kan farashin kayayyaki a kasar ta sakar wa ‘yan kasuwa.

      ‘Yan kasuwar sun bukaci gwamnati a nata bangaren ta rage harajin kayayyaki, daga bangarensu kuma su ji dadin rage farashin kayayyakin.

      Sai dai babu Karin bayani kan lokacin da ‘yan kasuwar za su rage farashin kayayyakin.

      Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

      Asalin hoton, Getty Images

    • Labarai da dumi-dumi, An sallami mai coronavirus daya tilo na jihar Ekiti

      Jihar Ekiti ta sallami mara lafiyar nan daya tilo da ke dauke da coronavirus a jihar.

      Gwamnatin jihar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter inda ta ce mara lafiyar ya shafe kusan kwanaki 12 yana jinya a wurin da aka killace sa.

      Kwamishinar lafiya ta jihar Dakta Mojisola Yaya-Kolade da kuma wani ma'aikacin hukumar UNICEF ne suka raka mara lafiyar zuwa mota domin kai shi gida.

      .

      Asalin hoton, @ekitistategov